An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 29 January 2016 13:18

Suratul Naml Aya Ta 57-60 (Kashi Na 687)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

 

**************MUSIC********

To Madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 57 da ta 58 a cikin suratul Namli:

 

فَأَنجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ قَدَّرْنَاهَا مِنَ الْغَابِرِينَ

 

57-Sai Muka tserar da shi tare da iyalinsa in ban da matarsa da Muka rubuta ta cikin hallakakku.

 

وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا فَسَاء مَطَرُ الْمُنذَرِينَ 

 

58-Muka kuma yi musu ruwan azaba, to ruwan azabar wadanda aka yi wa gargadi ya munana.

A cikin shirin da ya gabata kun ji cewa;mutanan annabi Ludu (AS) a maimakon sun saurari jawabinda da tuba daga ayyukan sabo da banna sai suke yi masa barazana da cewa:za mu fitar da kai daga wannan gari ko ma huta daga bayananka da galgadinka kan ayyukan da muke aikatawa da ranmu ke so wani lokaci ma za su rika yi masa izgili da cewa idan kana so ka ci gaba da kasancewa tsarkakekke ka fice daga wannan gari namu kar azabarmu ta shafe ka.To wannan ayar na cewa:Allah madaukakin sarki mai hikima da kafa hujja kan mutanan annabi Lud (AS) masu bakar jayayya kafin a sabkar masu da azaba ya aikawa annabi ludu (AS) mala’ika  da umurtarsa da ya fice daga garin kafin azaba ta sabka kuma haka aka yi ya fice tare da wadanda suka yi imani da shi daga wannan gari, kuma azaba ba ta shafe sub a da hikimar Allah.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da daukan darasin abubuwa uku:

Na farko:Amincewa da sabo ko fasadin da wasu ke aikatawa a gurin allah daidai yake da wanda ya aiakta aikin kuma azaba tana shafarsu baki daya.

Na biyu:A sunna da koyarwa  irin ta addinin Allah kuma haka yake a gurin Allah Imani ne ke kan gab aba dangantaka ba misali matar annabi Ludu da dan annabi Nuhu sun hallaka kuma kasancewar su suna da dangantaka ta kud da kud da wadannan annabawan Allah (AS) bai amfane su da komi ba amma ita kuwa matar Fir’auna ta kasance yar aljanna.


Na uku:Tsoron Allah da tsarkin imani a wannan duniya shi ne dalilin kubuta daga azaba da fushin Allah.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 59 a cikin wannan sura ta Namli:

 

قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ وَسَلَامٌ عَلَى عِبَادِهِ الَّذِينَ اصْطَفَى آللَّهُ خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ

 

59-Ka ce: Godiya ta tabbata ga Allah ,kuma aminci ya tabbata ga bayinsa wadanda ya zaba.Yanzu Allah ne ya fi ko kuwa abin da suke Tarawa da shi.

A karshen takaitaccen tarihin manzonnin Allah biyar sai wannan ayar ke Magana kai tsaye da manzon rahamaha tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka da cewa: ka yi godiya ga Allah ga ya tsarkake wannan duniya da masu shirka da aikata banna a doran kasa da kare ka daga aikinsu kuma aminci ya tabbata ga annabawa da manzonni da waliyan Allah saboda jan kokarin da suka yi kan hanyar shiryar da mutane da nuna masu hanya madaidaiciya babu kasawa dare da rana. Ci gaban ayar na cewa: Shin gumakan da mushrikai ke bautawa ko tarin dukiya da karfin iko sun kare su daga fushi da azabar Allah ne? Me ya sa bas u bautawa Allah daya abin bauta sun fi son bautawa alloli masu yawa da suke raya a zukata da tunaninsu? Shin bas u da labarin mummunan karshen al’ummomin da suka gabace su ne da yadda aka hallakar da su a wannan duniya ne.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da daukan darasin abubuwa biyu:

Na farko:Bayan godiya ga Allah madaukakin sarki kan ni’imomin da yayi mana sai kuma yi wa bayun allah na gari fatar alheri kan ayyukan alheri da suka yi don mu da kuma tunawa da su.

Na biyu:Waliyan Allah kullum a raye suke suna samin sakonmu na alheri da salama kuma amincin Allah na isa a gare su.

*************MUSIC**************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 60 a cikin wannan sura ta Namli:

 

أَمَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ السَّمَاء مَاء فَأَنبَتْنَا بِهِ حَدَائِقَ ذَاتَ بَهْجَةٍ مَّا كَانَ لَكُمْ أَن تُنبِتُوا شَجَرَهَا أَإِلَهٌ مَّعَ اللَّهِ بَلْ هُمْ قَوْمٌ يَعْدِلُونَ 

 

60-Ko kuwa wane ne ya halicci sammai da kassai,ya kuma saukar muku da ruwa daga sama sannan Muka tsirar da shukokin gonaki masu kayatarwa,ba kuwa za ku ya tsirar da bishiyoyinsu ba? Shin wani sarki ne tare da Allah? A’a ,su dai mutane ne da suke kauce wa gaskiya.

Wannan ayar ci gaban bayanin ayar da ta gabace ta ce da ke bayani kan karfi da kudurar Allah madaukakin sarki inda wannan ayar ke bayani kan ilimi da kudurar Allah da hakan ya bayyana hatta a irin ni’imomin da yayi mana iri iri a cikin sammai da kassai da cewa; Shin wadanda kuke bautawa ba Allah bas u ne suka halicci sammai da kassai kuma suke yi maku ruwa daga sama?Shin allolin da kuke bautawa sune suka shinfida maku tsirrai da lambu da itatuwa? Mi yasa ba ku fahimtar gaskiya da karbar gasika ne?Wannan ayar tana koyar da mutum da mutane baki daya hanyar tunani da nazari kan halittun Allah da kuma wanda ya halicce sun .Saboda duk mutum mai hankali da tunani mai kyau  zai iya fahimta cikin sauki cewa wannan duniya mai girma da tsari akwai mai tafiyar da it ace ba mu mutane ba kuma tana karkashin iko da iradarsa ne kuma dole mun fahimta da yarda tabbas wanda ya halicce ta da tafiyar da ita wannan duniya mai iko da karfi da kudura da ilimi da hikima ne kuma tana karshin iko da tsarinsa ne.

 

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko:Tunani da nazari cikin  halittun Allah it ace babbar hanya ta isa ga Allah.

Na biyu: Idan muka fahimci karfi da kudurar Allah za mu kuma fahimci kasawarmu da ta sauran halittu.

Na uku:Tafiyar da lamuran wannan duniya baki daya yana hannun Allah ne da kuma sabkar da rahamarsa da ruwa da fito da tsirre duka na hannun allah da kudurarsa.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh