An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 29 January 2016 13:04

Suratul Naml Aya Ta 50-56 (Kashi Na 686)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 50 zuwa ta 53 a cikin surtatul Namli:

 

وَمَكَرُوا مَكْرًا وَمَكَرْنَا مَكْرًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

 

50- Kuma suka shirya makirci Mu kuma Muka shirya ruguza makircinsu,alhali kuwa sub a su sani ba.

 

فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ مَكْرِهِمْ أَنَّا دَمَّرْنَاهُمْ وَقَوْمَهُمْ أَجْمَعِينَ 

51- Sai ka dub aka ga yadda karshen makircinsu ya zama ,watau Mun hallakar da su tare da mutanensu baki daya.

 

فَتِلْكَ بُيُوتُهُمْ خَاوِيَةً بِمَا ظَلَمُوا إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَعْلَمُونَ

 

52-To ga gidajensu can a rugurguje saboda zalincinsu,Hakika a game da wannan lallai akwai aya ga mutanen da suke tunani.

 

وَأَنجَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ

 

53-Muka kuma tserar da wadanda suka ba da gaskiya,suka kuma kasance suna tsoron Allah.

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda masu adawa da kafircewa kiran annabi Salihu (AS) suka yanke shawara da kudurta niyar aiwatar da kisan gilla kan annabin Allah kuma suka yi rantsuwa a tsakaninsu da suka fito daga kungiyoyi tara daban daban ta haka ba za a zargi wani ko wata kabila ba da kasha annabi Salihu (AS). Kuma sun yi niyar yin haka ne a lokacin da ya kebantu da iyalansa da sahabbansa a can inda yak e halwa da ambaton Allah shi kadai sais u kai masa hari da kasha shi  a can cikin tsaunukan duwatsu amma da taimakon Allah sai bulbudin duwatsu daka rufto masu  daga sama suka hallakar da su nan take. Wadannan ayoyin na cewa ne :Su sun yi zaton makircin da suka kitsa za su kai ga nasara da iya kasha Annabi salihu (AS) alhali Allah mai duka mai komi da kowa yayi niyar kare annabinsa daga makircinsu. Kuma wannan hallakar ba wai kawai ta shafi wadanda suka shirya makircin kasha annabi Salihu (AS) hatta wadanda suka amince da kasha annabin Allah Salihu (AS) daga cikin kaumu Samud an hallakar da su baki daya kuma mumunai daga cikin su da wannan azabar ta shafa a lahira za su shiga aljanna saboda bas u aikata wani laifi ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu:

Na farko:idan ma’abuta imani suka yi aiki da nauyin da ya rataya a kansu Allah zai kare su daga makircin kafirai da yi masu sakayya ta alheri.

Na biyu:Sunnar Allah ce a kullum gaskiya ke cin nasara kan karya ko da kuwa a zahiri wasu za su ga karya ta yi nasara a hakikanin gaskiya bah aka ne ba.

Na uku: al’ummomin da suka gabace mu da aka hallakar kan leifufffukan da suka aikata ya zame mana darasi a rayuwa.

Na hudu: Ma’abuta imani ba wai kawai a  lahira ba a nan duniya ma za su ga alherin ayyukan da suka aikata.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 54 da ta 55:

 

وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ

54-Kuma ka ambaci Ludu lokacin da y ace da mutanensa: Yanzu kwa rika zaike wa alfasha alhali kuwa kuna gani?

 

أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ النِّسَاء بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ

55-Yanzu kwa rika zaike wa maza don sha’awa ba mata  ba? A’a, ku dai wasu irin mutane ne da kuka jahilci mummunan sakamakon wannan aikin.

Bayan da muka ji takaitaccen tarihin rayuwar annabi Salihu (AS) da yadda aka hallakar da Samudawa da suka kafirce wa kiransa na tauhidi yanzu kuma za mu fara takaitaccen tarihin rayuwar annabi Lud (AS) da mutanasa kuma suraori da dama a cikin kur’ani sun yi bayani kan mutanan annabin Lud kuma wannan na nuni da muni ayyukan da mutanan annabi Lud (AS) suka aikata  da hakan ya zama babban darasi a gare mu baki daya da aikata fasadi a doran kasa da hakan ya zama darasi a kanmu da duk al’ummomin da suka biyo bayansu. Wadannan ayoyi da muka saurara na bayyana cewa:Annabi Lud (AS) a kullun yana nunawa alummarsa takaicinsa da damuwarsa kan mummunan aikin da suke aikatawa inda maza ke saduwa da junansu yan jinsi guda da ce masu: ku da kanku kun san munin wannan aiki da kuke aikatawa to mu me yasa kuke aikata wannan aiki? Kuma ku da kuke da matan aure me yasa ba ku zuwa wajen matanku sai ku rika neman mata da cutar da matanku? A bisa dabi’a idan mazaje na zuwa wajen maza yan uwansu da saduwa da su sannu a hankali suma matansu za su fara neman junansu da nisanta da mazajensu da ruguza rayuwar iyali da gurbata iyalinsu da yawaitar rabuwar aure a tsakanin al’umma. Abin takaic a wannan duniyar ta mu ta yau ma duk da wayewar da aka samu da ci gaban ilimi da akida ana aikata wannan mummunan aiki da saboda shi aka hallakar da mutanan annabi Lud (AS).aikin da ya saba da fidirar mutum kuma abin mamaki hatta wasu kasashen yammacin turai hatta dokokin da ke yaki da wannan mummunan aiki a hukumci ya rusa su.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:Yaki da gwagwarmaya da ayyuka mummunan da yada fasadi a tsakanin jama’a ya rataya kan annabawan allah da duk wani mai son gyaran al’umma.

Na biyu:Ita saduwa wani abu ne da jikin mutum a dabi’ance ke bukatuwa amma dole ya kasance kan shari’a  da tsarin da shari’a ta amince.

Na uku:Saduwar yan jinsi daya na nuni da wawanci da dabbanci ko da kuwa mai aikatawar a zahri masani ne da wayewa.

 

*****************MUSIC************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 56 a cikin wannan sura ta Namli:

 

فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا أَخْرِجُوا آلَ لُوطٍ مِّن قَرْيَتِكُمْ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ

 

56-Babu wani jawabin da ya zo daga wajan mutanensa sai cewa: Ku fitar da Ludub Shi da iyalinsa daga alkaryarku: hakika su mutane ne da suke kyamar abin  da muke yi.

A amimakon sun amince da wannan bayani na hankali da hujjoji da annabi Lud (AS) ya tabbatar masu da sabon da suke aikatawa sai suka fara neman bijirewa da daukan matakin fito na fito  da cewa; dole annabi Lud (AS) da iyalansa da sahabbansu da duk wani mai binsa da ke ganin munin  aikin da muke aikatawa  ku fitar da shi daga garin ta haka ba za a samu wani da zai sake aibata aikin da muke aikatawa ba. Haka ne a duk lokacin da sabo da ya mamaye guri a maimakon a hukumta mai leifi a’a mai gaskiya da wa’azi ne za a hukumta da takurawawa ko azabtar da shi kamar yadda Annabi Yusuf (AS) yana matashi ya fuskanta da kakaba shi a gidan yari na tsawon shekaru kan leifin da bai aikata ba kuma leifinsa yaki ya aikata sabon  da Zulaiha ta bukaci ya aikata.

Daga wannan aya za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:ba a amince mutum yayi gum da bakinsa yana ganin ana aikata sabo dole yayi aiki da duk wata damar da yake da ita sai idan abin yafi karfinsa.

Na biyu:Masu raya yanci sun eke yada mumunar dabi’a ta saduwa da juna nay an jinsu daya kuma ya samo tushe daga mutanan annabi Lud da aka hallakar kan wannan mummunan aiki kuma jahilai.Kaicon wannan yanci.

Na uku:a ko’ina ana samin mutanan kirki ko da a kasashen kafirai ne mutum na iya rayuwa mai tsafta da tsoran Allah.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh