An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 29 January 2016 12:51

Suratul Naml Aya Ta 45-49 (Kashi Na 685)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah za mu fara shirin na yau tare da sauraren karatun aya ta 45 zuwa 47 a cikin wannan sura ta Namli.

 

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ

45-Hakika kuma Mun aiko wa Samudawa dan uwansu Salihu da cewa: Ku bauta wa Allah,sai ga su sun rabu biyu suna jayayya.

 

قَالَ يَا قَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ الْحَسَنَةِ لَوْلَا تَسْتَغْفِرُونَ اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ 

 

46- Yace : Ya ku mutanena,don me kuke neman gaggautowar mummunan sakamako tun gabanin kyakkyawa? Ai ya kamata ku nemi gafarar Allah ko a ji kan ku.

 

قَالُوا اطَّيَّرْنَا بِكَ وَبِمَن مَّعَكَ قَالَ طَائِرُكُمْ عِندَ اللَّهِ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ تُفْتَنُونَ 

 

47- Sai suka ce: Mu mun camfa ka kai da wadanda suke tare da kai.Sai y ace :A’a ,mummunan abin da ya same ku daga wurin Allah yake.A’a ,ku dai mutane ne da ake jarraba ku.

Daga farkon wannan sura ta namli zuwa yanzu sun ji takaitaccen tarihin rayuwar annabawa kamar annabi Musa,Annabi Dawud,da Annabi Sulaiman (AS) to amma wadannan ayoyi da muka saurara suna Magana ne kan annabi Salihu da al’ummar Samudawa al’ummar da Annabi Salihu (AS ) ya nuna masu kauna  da soyayya da yan uwantaka da kuma kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta ba tare da sun hada shii da wani a bautar ba,Wasu kadan daga cikin al’ummar tasa sun yi  imani da shi da yi masa biyayya amma mafi yawa daga cikin al’ummar tasa ta Samudawa sun kafirce da bijirewa wannan kira na sa. Kuma wannan lamari na rabuwar al’umma gida biyu kafirai da mumunai ya haddasa rikici da kusuma wani lokaci tsakanin mutane biyu wani lokaci ma gungu –gungun jama’a.Annabi Salihu (AS) ya gargadi kafirai masu bakar jayayya da yi masu kashedi cewa makomar aikinsu azaba da fushin Allah ne kuma me ya sa ba ku tuba da nadama da wannan mummunan aiki da kuke aikatawa kuma me yasa kuke bijirewa umarnin  Allah? Amma a maimakon sun yi wannan nasiha ta annabi Salihu kollon basira da fahimta ta gari sai suka ce: Idan abin da kake fada da gaske ne me yasa Allanka bay a gaggauta sabkar mana da azabar? Kuma a wannan duniya ta haka mu da kai kowa zai san matsayinsa.

Ci gaban ayoyin da muka saurara na cewa:Annabi Salihu (AS) ya amsa masu da cewa:me yasa a maimakon ku yi istigfari da tuba kan sabon da kuka aikata sai ku nemi azaba a maimakon rahamar Allah.? A maimakon tuba azaba kuke bukata? Me ya sa ba ku wani habbasa na neman rahamar Allah da alheri da sa’ada da dacewa duniya da lahira kuma idan azaba ta fara riskarku tabewa ta karshe ta same ku . a tsawon tarihi kafirai da masu jayayya bas u fahimta da aiki da galgadin annabawa da manzonnin Allah ,suna yin riko da matakin  fito na fito da ci gaba da yada fasadi da banna da kisa a doran kasa. Misali duk da bijirewar da Samudawa suka yi wa kashedin da annabi Salihu (AS) yayi masu lokacin da suka fuskanci fari a mai makon su fahimci kuskuransu sai suka ce: dukan wannan abu da yake faruwa da mu maganganunka ne ya jawo mana har yanayi yayi fushi da mu da fuskantar matsaloli kuma ka yi mana camfi. Amma cikin saukin kia sai Annabi Salihu ya amsa masa cewa:makomarku mai kyau ko lala tana hannun Allah ne kuma wannan halin da kuke ciki wata jarrabawa ce daga Allah  ba wai lamari na camfi ba daga wani daga cikin bayun Allah kuma me yasa kuke son danganta wannan lamari da wanin ku ba ku yin dubi kan ayyukan da kuke aikatawa  masu muni da sabawa Allah.

Daga cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Kira zuwa ga tauhidi da kadaita Allah da bauta shi ne lamari na farko da manzonni ke himmatuwa da shi.

Na biyu:A tsawon tarihi ana samin rikici tsakanin gaskiya da karya kuma ba zai yuyu ba al’ummar wani yanki da zama baki dayanta kan gaskiya ko ma’abuta imani.

Na uku: a daidai lokacin da ake gargadi da kashedi kan masu sabio da banna sai a hada da hanyar tuba  da neman rahamar Allah ga masu sabo.

Na hudu:a maimakon fahimtar bayani na hankali da hujja na manzonni ,kafirai na ci gaba da riko da kafirci da munanan tunani na shaidanci.

******************MUSIC**********

Daga karshe kuma za mu saurari karatun aya ta 48 da kuma ta 49 a cikin surar ta Namli:

 

وَكَانَ فِي الْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ

 

48- A cikin garin kuma akwai wani gungu na mutum tara wadanda suke barna a bayan kasa kuma bas a gyara.

 

قَالُوا تَقَاسَمُوا بِاللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّهُ وَأَهْلَهُ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّهِ مَا شَهِدْنَا مَهْلِكَ أَهْلِهِ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ

 

49- Sai suka ce: Mu rantse da Allah a junanmu cewa lallai za mu kasha shi cikin dare shi da iyalinsa,sannan lallai za mu fada wa manema jininsa cewa: ba mu halarci wurin kasha iyalinsa ba ,kuma wallahi da gaske muke.

Wadannan ayoyi na nuni ne da makircin da kafirai suk shirya na yin kisan gilla kan annabi Salihu(AS) da cewa;a tsakanin al’ummar Samudawa wani gungu da wasu mutane da suka yi nisa a fasadi da banna kuma bas u da zabi sai ko su ci gaba da banna ko yin tuba  da gyara halayensu  sune suka yi wa junansu alkawali na kissa kisan gilla kan Annabi Salihu (AS) da iyalan gidansa da sahabbansa kuma bayan wannan aika-aika duk wanda ya zarge su shi ma su kasha shi. Da daura leifin kan wasunsu. Abin mamaki a lokacin da suka yi alkawali a tsakaninsu sun yi rantsuwa da Allah da tunawa da Allah da hakan ke nufin sun amince da Allah ne ya halicce su.Amma wajen bauta suke bautawa gomaka da cewa: Allah ne ya halicce mu  amma y aba mu yanci yin abin da muka ga dama don haka duk wani aiki da muka gay a dace za mu aikata ba shamaki kuma ba mu bukatar wani annabi ko manzo. Wannan Magana tasu  ta yi daidai da abin da wasu masana da ganin kansu wayayyu ke fada a yau ke nan na musanta akwai Allah da danganta duk wani aki ga mutum da aikata abin da ya ga dama da ransa ya raya masa da sharadin kar ya cuci waninsa.

Makircin kisan gilla kan Annabi Salihu 9AS) domin a tunatar da mushrikan makka ne makircin da suke kullawa manzon Rahama(SWA) na kisan gilla kansa a cikin dare kuma kowace kabila ta bada mutum guda daga cikinta ta haka kowace kabila ta hadu akisan manzon rahama (SWA) kuma ba za a zargi wata kabila guda da leifin kisan ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko:Masu kiyayya da  manzonni ba mutane ne da ke aiki da hankali da tunani ba kawai abin da ya rufe masu ido ta inda za su hana manzonni yada addini da kiran mutane zuwa ga tauhidi don haka suke kitsa da shirya kisan gilla kansu.

Na biyu:A tsawon tarihi abubuwa masu yawa sun faru da killa makirce makirce na kisa kan bayun Allah da waliyan Allah da annabawa da manzonnin Allah a gurare masu tsarki da daraja da rayuku.

 

 

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh