An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 29 January 2016 12:43

Suratul Naml Aya Ta 41-44 (Kashi Na 684)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah masu saurare a shirin na yau za mu saurari karatun aya ta 41 zuwa 43 a cikin suratul  Namli:

 

قَالَ نَكِّرُوا لَهَا عَرْشَهَا نَنظُرْ أَتَهْتَدِي أَمْ تَكُونُ مِنَ الَّذِينَ لَا يَهْتَدُونَ

 

41- Sai Silaimana y ace: Ku sauye kamar gadon nata mu gani za ta gane shi ne ko kuwa za ta zamanto cikin wadana bas a ganewa?.

 

فَلَمَّا جَاءتْ قِيلَ أَهَكَذَا عَرْشُكِ قَالَتْ كَأَنَّهُ هُوَ وَأُوتِينَا الْعِلْمَ مِن قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ

 

42- To lokacin da ta zo,sai aka ce da ita: Shin haka kuwa gadonki yake? Sai ta ce: Sai k ace shi ne Sulaimana y ace: an kuwa mun kasance Musulmi.

 

وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعْبُدُ مِن دُونِ اللَّهِ إِنَّهَا كَانَتْ مِن قَوْمٍ كَافِرِينَ

 

43-Kuma abin da ta kasance tana bauta wa ba Allah ba shi ya hana ta yin imani,hakika ita ta kasance cikin mutane kafurai.

A cikin shirin da ya gabata kun yadda sarauniyar Saba’a Balkissa tare da babbar tawaga ta fadawanta ta kama hanyar zuwa Sham daga yankin Yamen  domin amsa kiran Annabi Sulaiman (AS) Kuma kafin ta iso Annabi Sulaiman (AS) ya bukaci a kawo masa gadan sarautarta tun kafin ta iso fadarsa kuma haka aka zartar da wannan bukata tashi kafin ya kibta idonsa cikin ikon Allah.

To wadannan ayoyi da muka saurara na cewa:Sulaiman yayi haka ne domin sanin karfin fahimtar sarauniya Balkisa da kuma nuna mata mu’ujizarsa kuma ya bada umarnin a yi wa wannan gadon sarauta nata kwaskwarima ko za ta iya gane shi  kuma isowarta ke da wuya sai aka nuna mata wannan gadon da cewa: Shin gadon mulkinki yayi kama da wannan? Duk da kwaskwarimar da aka yi masa da wasu canje canje sai ta amsa da cewa :wannan gadona ne. Bayan da Balkisa ya gane gadonta sai ta cewa Annabi Sulaiman (AS) da Mukarrabansa cewa: idan kun yi haka ne domin ku nuna mana karfin iko da kudurar da Allah ya baku don mu mika wuya a gare ku to mu tun kafin mu iso nan  muna da masaniya kan karfin da kuke da shi kuma muni so nan ne domin karbar musulunci da amincewa da kiran annabi Sulaiman (AS). Ci gaban ayar na cewa:saboda sarauniya balkisa ta yankin Saba’a ta rayu tare da manyan kafirai da bautawa rana da goma na tsawon shekaru ba a shirye suke bas u amince da karbar musulunci da amincewa da bautawa Allah daya amma ganin  ta furta da amincewa da musulunci bas u da wani zabi face amincewa da addinin musulunci da bautawa da Allah daya na gaskiya ,Allan annabi Suleiman (AS),

 

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Yin imani da mika wuya ga gaskiya na matukar daraja da matsayi amma idan yana karkashin ilimi da masaniya na yin biyayya ido rufe cikin jahilci ba.

Na biyu:Idan aka samu gurbatattun tunani da akida a tsakanin jama’a na hana isa ga gaskiya da imani.

Na uku: a kullum abin da mutum ya aikata ake aiki da shi idan ya tubu da gyara halayansa ba a waiwaya baya.

********************MUSIC****************

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 44 a cikin wannan sura ta Namli:

 

قِيلَ لَهَا ادْخُلِي الصَّرْحَ فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّةً وَكَشَفَتْ عَن سَاقَيْهَا قَالَ إِنَّهُ صَرْحٌ مُّمَرَّدٌ مِّن قَوَارِيرَ قَالَتْ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَانَ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

 

44-Aka ce da ita : Ki shiga fadar,to lokacin da ta gan ta sai ta zace ta ruwa ne mai zurfi,sai kuwa ta yaye kwabrinta. Sai Sulaimana y ace: Ai ita fada ce da aka gina da gogaggun kasaken karau ruwa  yake gudana ta karkashinsu. Ta ce; Ya Ubangijina ,Hakika na zalunci kaina, na kuma musulunta ga Allah Ubangijin talikai tare da Sulaimana.

Kamar yadda ya zo a littafen tarihi da kuma bayanin wannan ayar ,Annabi Suleiman ya bada umarnin a gina masa falfajiya ta gilashi da ruwa ke gudana karkashinta to lokacin da Sarauniya Balkisa za ta fice a tunaninta ruwan teku ne g=ke gudana  sai ta tattare rigarka kar ta jike ganin haka sai Annabi (AS) ya cewa sarauniya Balkisa: wannan falfajiya ce da aka yi da gilashi da ruwa da ruwa ke gudana karkashinta tamkar ruwan teku. A dabi’ance Sarauniyar Saba’a Balkisa ganin tana ji da mulki da sarauta itama  abin da ya faru a fadar Annabi Sulaiman (AS) ya kasha mata ji da da daukaka hukumar Sulaiman yayin da masarautar kuwa ta kaskanta da ita kanta sarauniya Balkisa don haka babu abin da yayi mata saura face kaskantar da kanta a gaban Annabi Sulaiman (AS). Ta wata fuskar Annabi Sulaiman (AS)  ya nunawa Sarauniya Balkisa da fadawanta karfin iko na sahiri da badini  da fahimtar da su cewa idan suka yanke shawarar yaki da shi babu wata riba da za su samu sai asara da kaskanta.Saboda haka bayan sun ga hukumar annabi Sulaiman (AS) ta zarta ta su kuma ta fuskar ma’anawiya ma haka domin duk da wannan iko da duniya da kudura da Allah ya huwace ma annabi Sulaiman (AS) bai damu da sub a ya maida hankali kan bautawa Allah da gode masa da kiran sauran mutane a yankuna dabana daban da lungu da saka na duniya zuwa ga kadaita Allah da bauta shi kadai ba tare da an hada shi da wani da bauta ba. Ganin haka Sai Sarauniya Balkisa da fadawanta suka karbi musulunci da neman gafarar Allah da ya yafe masu kan shirker da suka yi a baya ta bautawa rana da gama Allah da waninsa da bauta. Kuma Sarauniya Balkisa ba ta ce ba ina mika wuya da Sulaiman sai ta ce ina mika wuya da Allah da hakan ke nufi shi ma Sulaiman ya mika wuya da Allah ne ke nan mu duga biyu bayun Allah da hakan na tabbatar da imanin sarauniyar Saba’a Balkisa imani ne na hakika har zucci kuma har a bada ta bar bautawa Rana sai dai bautawa Allah da ya halicci kowa da komi.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa hudu:

Na farko: a rika amfani da dukiya da damar da Allah y aba mu wajen yada addini kamar yadda Annabi Sulaiman (AS) yayi .

Na biyu: Duk wata kwarewa da hikima mu yi amfani da su domin kafawa kafirai hujja da yin imani.

Na uku:Yin tuba ta hakika it ace amincewa da ayyukan da mutum ya aikata da neman Allah ya gafarta masa da haskaka masa hanya da shiriya daga Allah.

Na hudu:Ruhin Imani shi ne mika wuya ga Allah mahaliccin talikai da duniya baki daya kamar yadda sarauniyar Saba’a Balkisa ta bayyana imaninta ga Allah bayan tsawon shekaru ta bautawa Rana.

 

 

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh