Print this page
Friday, 29 January 2016 12:24

Suratul Naml Aya Ta 36-40 (Kashi Na 683)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

 

To madallah masu saurare yanzu kuma za mu fara shirin da sauraren karatun ayoyi na 36 da 37 a cikin  suratul Namli.

 

فَلَمَّا جَاء سُلَيْمَانَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٍ فَمَا آتَانِيَ اللَّهُ خَيْرٌ مِّمَّا آتَاكُم بَلْ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ

 

36-To lokacin da manzon ya zo wa Suleaimana sai y ace: Yanzu kwa kare ni da wata dukiya,alhali abin da Allah y aba ni ya fi anda Y aba ku? A’a ,ku ne kuke farin ciki da hadayarku.

 

 ارْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُمْ بِجُنُودٍ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخْرِجَنَّهُم مِّنْهَا أَذِلَّةً وَهُمْ صَاغِرُونَ

 

37- Koma musu da hadayarsu sannan ka gaya lallai za mu zo musu da runduna wadda ba za su iya tunkarar ta ba,kuma lallai za mu fitar da su daga cikinta alkaryar a wulakance suna kaskantattu.

 

A cikin shirin da ya gabata kun amsar da Sarauniya Balkisa ta yankin Saba’a ta mayar ga wasikar annabi Sulaiman (AS) ta aika masa manzo na musamman tare da hadaya wato kyauta ta musamman domin samin hakikanin abin da yake bukata a gare su shin bukatarsa dukiya da kwadayin wani abu a wannan duniya ko kuwa a’a? Kuma ta bukaci manzonni da su lura da ganin abin da zai yi lokacin da ya ga wannan hadaya da kawo mata rahoto kan hakan.

Wadannan ayoyi da muka saurara lokacin da annabi sulaiman ya ga wannan hadaya bayan bai ji  dadi da nuna farin cikinsa ba  sai ma ya dauka wani cin hanci da rashawa suke neman bas hi da cewa: shin kun yi zaton ni ina kwadayin wani abu daga dukiya da wadata a wannan duniya don haka kuka taho da wannan hadaya a gare ni? Wannan abu da kuka kawai bai kai kwayar zarra  ba daga cikin abin da Allah ya huwace mani . Burina ku amince da karbar gaskiya  amma idan kuka ki mika wuya  zan tura maku rundunar da ba a cin nasara kanta da mamaye hukuma da mulkinku baki daya da maida ku kaskantattu raunana da kuma fitar da ku daga yankin baki daya. Bugu da kari ni nay i zaton za ku nemi hujja da dalili kan abin da na ke rayawa na annabci ba wai ku aiko mani hadaya ba  da kokarin yaudara ta.

Daga cikin wadannan ayoyi  za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka;

Na farko: Waliyan Allah kudi da dukiya bas u rude su a ayyukan da suke yi kuma burinsu sabke nauyin da Allah ya daura masu da amincewa da yardarsa ba dukiya ba da dodar duniya.

Na biyu:Wajen gamsar da wasu ana bukatar kafa masu hujja da dalili na hankali amma wasu kuwa ana bukatar nuna masu karfi.

Na uku:A sauran addinai da suka gabata ma jihadi wajibi ne.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 38 a cikin wannan sura ta Namli.

 

قَالَ يَا أَيُّهَا المَلَأُ أَيُّكُمْ يَأْتِينِي بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَن يَأْتُونِي مُسْلِمِينَ

 

38- Sai Sulaimana ya ce: Ya wazirai wane ne daga cikinku zai zo min da gadon mulkinta tunkafin su zo min suna masu mika wuya?

Kamar yadda ya zo a cikin littafen tarihi manzonnin musamman da Sarauniya Balkisa ta aika wa Annabi Sulaiman (AS) da hadaya sun koma gurinta da yi mata bayani dalla dalla kan ganawarsu da Annabi Sulaiman (AS)  da yadda yaki karbar wannan hadaya da kuma karfin iko da rundunar tsaron da yake da ita.Bayan haka sai sarauniya Balkisa  ta yanke shawarar tare da manyan fadawanta baki daya za su zo gurin Annabi Sulaiman (AS) da bayyana masa su manufarsu ba yaki ba da tsayin daka a ggare shi ba. To Allah ya sanar da annabinsa Sulaiman (AS) wannan mataki na Sarauniya Balkisa da fadawanta saboda da ya nuna mata karfin iko da mulkin da allah y aba shi  ya bukaci wadanda key i masa hidima wane ne daga cikinsu zai iya kawo masa gadon mulkin sarauniya Balkisa  kafin sui so nan fadarsa dake Sham kuma za su dauko shi ne daga yankin Yaman .

A cikin wannan aya za mu dauki darasin abubuwa da dama amma za mu takaita da guda biyu kamar haka:

Na farko:Annabwa da manzonnin Allah suna da ilimin gaibi daga Allah suna amfani da shi a duk gurin da ya dace.

Na biyu: Nesa ta komo kusa da tafiyar kwanani a yi ta a rana daya wani abu ne mai yuyuwa ko bag a manzonni ba  balantana manzonni don haka Annabi Sulaimana (AS) ya bukaci kawo mashi da gadan Balkisa na mulki.

******************MUSIC******************

To daga karshe za mu saurari karatun aya ta 39 da ta 40 a cikin wannan sura ta Namli:

 

قَالَ عِفْريتٌ مِّنَ الْجِنِّ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَ وَإِنِّي عَلَيْهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٌ

 

39- Sai wani kakkarfan aljani yace; Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga majalisarka,hakika ni kuma mai karfi ne amintacce game da kawo shi.

 

قَالَ الَّذِي عِندَهُ عِلْمٌ مِّنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَن يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ فَلَمَّا رَآهُ مُسْتَقِرًّا عِندَهُ قَالَ هَذَا مِن فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيٌّ كَرِيمٌ

 

40- Sai wani mutum wanda yake da ilimin littafi na Attaura yace: Ni zan kawo maka shi kafin ka kifta idonka” To lokacin da ya gan shi gingirim a wurinsa sai y ace: Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni Ya gani shin zan gode ne ko zan butulce,to duk wanda yayi godiya kansa yayi wa, wanda kuwa ya butulce,to hakika Ubangijina Mawadaci ne Mai karemci.

 

Mutum biyu ne dai suka bayyana zartar da wannan bukata ta Annabi Sulaiman (AS) na kawo wannan gado na sarauniya Balkisa  a cikin kankanan lokaci daga yankin Yamen zuwa yankin Sham. Na farko Ifritu ne daga cikin jinsin aljannu wanda ya durkusa a gaban Annabi Sulaiman y ace masa zai zartar da wannan bukata ta  kafin  ya tashi daga wannan majalisa ta sa.

Amma shi mutum na biyu  mai suna Asif bin Barkhiya daya daga cikin wazirai a fadar mulkin annabi Sulaiman (AS) kuma shi ne bayan rasuwar annabi Sulaiman (AS) shi ne ya jagoranci al’ummar Annabi sulaiman (AS)ya bayyanawa Annabi Sulaiman (AS) cewa zai iya  kawo masa wannan gadon mulki na sarauniya Balkisa kafin ya kibta idonsa. Ganin lokacin da Waziri Asif bin Barkhiya ya fada yafi kankanta sai Annabi Sulaiman (AS) ya amince da ya zartar da wannan bukata kuma haka ya aiwatar a cikin kankanan lokaci. Wannan jan aiki daya daga cikin yara kuma wazirin Annabi Sulaiman (AS) aka zartar  to zai iya yuyuwa ya sanya girman kai  saboda hana yaduwar wannan mummunan hali a tsakanin jama’a sai annabi Sulaiman (AS) ya fara da ambaton sunan Allah  da gode masa kan wannan babbar ni’ima da ba mu damar zartar da wannan aiki cikin nasara.Kuma ta haka duk wanda yake gurin ya fahimci wannan aiki Allah ne ya zartar da su ba  da tunawa da Allah da gode masa  duk da cewa Allah bay a bukatuwa da godiyarmu kuma amfanin godiyar yana komowa a gare mu ne.

Daga cikin wadannan ayoyi na mu ilmantu da abubuwa akalla guda uku:

Na farko : Mutum ta hanyar ilimin da Allah y aba shi yana iya sarrafa dabi’a ta inda yake so.

Na biyu: a yau mutum ya samu ci gaban ilimi da kere-kere don haka abin da ya faru a lokacin Annabi Sulaimanu (AS) ba abin mamaki ne ba  ga wanda yake da ilmin kitab.

Na uku: kar ka yi alfahari da ilimi da kudura domin duk wata Ni’ima ta Allah ce da lutifin Allah ya sanya a hannunka sai ka yi aiki da ita ta hanyar da ta dace.

 

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh