An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 29 January 2016 12:01

Suratul Naml Aya Ta 30-35 (Kashi Na 682)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC*********

      To Madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 30 zuwa 32 a cikin suratul Namli :

 

إِنَّهُ مِن سُلَيْمَانَ وَإِنَّهُ بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

 

30-Mai Cewa: Lallai wannan wasikar daga Suliamana ne kuma lallai ina farawa  da Bismillahir Rahamni ar Rahamani ar Rahimi.

 

أَلَّا تَعْلُوا عَلَيَّ وَأْتُونِي مُسْلِمِينَ

 

31-Kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu mika wuya.

 

قَالَتْ يَا أَيُّهَا المَلَأُ أَفْتُونِي فِي أَمْرِي مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّى تَشْهَدُونِ

 

32-Sai Sarauniyar Ta ce: Ya ku wazirai,ku ba ni shawara game da al’amarina, domin ni ba zan yanke shawarar wani al’amari sai kuna nan.

 

A cikin shirin da ya gabata kun ji cewa: bayan da annabi Suleiman (AS) ya samu labarin halin da mutanen yankin Saba’a ke ciki na bautawa rana ya rubuta wasika da bawa Hud –Hud da ya kai masu kuma haka Hud-hud yayi ya isar da wannan sakon wasika ta annabi Suleiman (AS) ga sarauniyar Saba’a balkissa. Kuma wadannan ayoyin da muka saurara na bayyana cewa: Sarauniya Balkisa ta yankin Saba’a ganin wannan wasika sai ta fahimci wannan tsintsu mau kyau halitta ne ya kawo ta  kuma wasika ce daga babban mutum mai fdaraja da daukaka ,ba da wata wata ba ta shawarci makusantanta da manyan fadawanta kan wannan lamari kuma a gabansu aka karanta wasikar  da ta fara da sunan Allah mairahama da jin kai kuma ta fito ne daga Suleiman kuma tana kiransu zuwa ga karbar gaskiya kuma kar su kuskura su bijirewa  da baudewa hukumar Suleiman.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Duk wani aiki a fara shi da sunan Allah mai rahama da jin kai ko da kuwa rubuta wasika ne zuwa ga kafirai.

Na biyu: wajen karbar gaskiya babu wani mikami ko nuna fifiko a tsakanin mutane.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 33 da 34 a cikin wannan sura ta Namli:

 

قَالُوا نَحْنُ أُوْلُوا قُوَّةٍ وَأُولُوا بَأْسٍ شَدِيدٍ وَالْأَمْرُ إِلَيْكِ فَانظُرِي مَاذَا تَأْمُرِينَ

 

33-Sai suka ce: Mu dai karfafa ne kuma mayaka sosai,al’amarin kuwa yana hannunki,sai ki duba abin da za ki yi umarni.

 

قَالَتْ إِنَّ الْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوا أَعِزَّةَ أَهْلِهَا أَذِلَّةً وَكَذَلِكَ يَفْعَلُونَ

34-Sai ta ce : ba shakka sarakuna idan suka shigo wata alkarya sai su yi kaca-kaca da ita,kuma su mayar da manyanta kaskantattu,kuma haka suke aikatawa.

Bayan karanta wannan wasika ta Suleiman ,sai sarauniyar Saba’a Balkisa mace mai zurfin tunani da karfin siyasa  ta bukaci manyan fadawanta da shugabannin sojoji  amsar da za a bawa Suleiman .A dabi’ance ta shawarce su ne da neman taimakonsu  ba don ba ta san ba cewa a shirye suke su kalubalanci rundunar Suleiman ba kawai salo ne na tafiyar da mulki.Mukarrabanta da komandodin sojoji sai suka ce mata mu ma’abuta karfi da yaki ne kuma a shirye muke su kobza fada da yaki da rundunar Suleiman. A hakikanin gaskiya daga wasikar su sun fahimci cewa: Annabi Suleiman (AS) ya shelanta yaki ne a kansu kuma kamar yadda dabi’ar komandodin soji take a kowace kasa ko yawancin kasashe suna rungumar yaki ne a maimakon mika wuya. Sai dai sun ce amma matakin karshe yana gare ta Sarauniya Balkisa kuma duk abin da ta zartar su a shirye suke su zartar da aiwatarwa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: samin karfi da nuna karfin soji da dakaru da na’urori da makamai ga kasa yana da kyau amma kar su zama dalilin girman kai da dagawa wajen karbar gaskia.

Na biyu: Yin shawara a lamrua na tafiyar da mulki yana da kyau amma matakin karshe mutum daya ne ke daukansa gudun kar a samu matsala a zartarwa da karo da juna.

*********************MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta  35 a cikin wannan sura ta Namli:

 

وَإِنِّي مُرْسِلَةٌ إِلَيْهِم بِهَدِيَّةٍ فَنَاظِرَةٌ بِمَ يَرْجِعُ الْمُرْسَلُونَ

 

35- Ni kam zan aika musu ne da wata hadaya sannan in saurari abin da manzannin za su dawo da shi.

Bayan da sarauniya Balkisa ta ji shawarar da manyan fadawanta da komandodin sojoji da fahimtar cewa a shirye suke su yi yaki da rundunar Suleiman.Sai ta bayyana masu cewa ku sani fa idan muka shika yaki babu wani abin sai banna da asara da ruguza komi  dalili kuwa su sarakuna mai karfi da danniya idan suka shiga gari  suna lalata gidaje ,da kasha mutanen garin  da haddasa masu babbar asara da raunana wasu. Don haka a maimakon mu shelanta yaki mai zai hana su kara samin cikekken labara da sanin abin da Suleiman ke nufi da mu da aiko mana wannan wasika. Don haka za mu tura masa manzo dauke da kyauta ta musamman  sannan muga amsar da Suleiman zai bayar. Kuma idan ya amince da wannan kyauta ba zai yake mu ba idan kuma nufinsa mamaye za mu fahimta da daukan matakin da ya dace da mu ko mu yayi yaki da shi ko a’a.

Tana yuyuwa Sarauniya Balkisa ta hanyar wannan kyauta  tana son sanin gaskiyar shi Suleiman manzon Allah ne da gaske ko kuwa sarki ne kamar sauran sarakuna na nuna karfi da mamaye sauran kasashe. Saboda ta san su manzonnni  bas u bukatuwa da dukiya ko kwadayin wani abu a wannan duniya. Babu abin da suka dukufa da shi kamar yada addini da gasakiya a doran kasa  da kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta,amma su sarakuna sun fi maida hankali kan tara dukiya da karfi iko ta kowace hanya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:yada fasadi da neman yaki wata hanya ce da hukumomin da ban a Allah ba ke bi don mallakar sauran al’ummomi.

Na biyu:Mu yi hankali wani lokaci wasu na fakewa da taimako don cutar da mu da kuntata mana.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh