An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 13:14

Suratul Naml Aya Ta 23-29 (Kashi Na 681)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC*********

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au da sauraren karatun aya ta 23 da 24 a cikin wannan sura ta Namli.

 

إِنِّي وَجَدتُّ امْرَأَةً تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِن كُلِّ شَيْءٍ وَلَهَا عَرْشٌ عَظِيمٌ

23-Shi ne hakika na sami wata mace tana mulkin su,an kuma ba ta daga kowane abu na mulki tana kuma da gadon sarauta mai girma.

 

وَجَدتُّهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِن دُونِ اللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لَا يَهْتَدُونَ 

 

24-Na same ta ita fa mutanenta suna sujjada ga rana ba Allah ba. Shaidan kuma ya kawata musua ayyukansu sannan ya kange su dage bin hanya ta gaskiya,to sub a sa shiriya.

 

أَلَّا يَسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي يُخْرِجُ الْخَبْءَ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ 

 

25-Don kada su yi sujjada ga Allah wanda Yake fito da abin da yake boye a cikin sammai da kassai,kuma Yake sane da abin da kuke boyewa da abin da kukke bayyanawa.

A cikin shirin da ya gabata a kun ji yadda Alhud-hud ya tafi gurin annabi Suleiman (AS) don bayyana masa dalilin rashin kasancewarsa cikin tawagar tsuntsaye na wani lokaci  da cewa; Ni na tafi kasar Saba’a kuma ina dauke da labara mai muhimmancin gaske. To wadannan ayoyi da muka saurara na bayani ne kan rahoton da Hud-hud ya zo wa Annabi Suleiman (AS) da shi  daga yankin Saba’a da cewa sabanin sauran yankuna a wannan yankin na Saba’a wata mat ace ke mulkinsu  kuma Allah ya bata dukan dukiya da mulki  da duk abin da take bukata  kluma tanada fada  babba da yi mata fadanci da girmama ta ba iyaka. Amma babu abin da suke yi wa sujada sai ran aba Allah ba saboda Shaidan ya kayata masu ayyukansu. Annabi Suleiman (AS) da jin wannan rahoto na Hud-hud da karfin iko da hukumar wannan mata sai mamaki ya kama shi kuma Hud Hud a cikin rahotonsa yayi nuni da lamari mai matukar muhimmanci  cewa: ba gadon mulkin da karfin ikon wannan mace ba ne ya bawa Annabi Suleiman (AS) mamaki a’a  a matsayinsa na Manzon daga Allah  dole ya san wadannan mutane da ke bautawa Ran aba Allah ba a wannan yankin na Saba’a da yadda suka gurbata da sabo  da yadda shaidan ya yaudare su haka  har suka nuce a aikata sabo da banna a doran kasa da kuma yake tunanin  hanyar shiryar da su duk da cewa lamari ne mai matukar wahala.

A cikin wadannan ayyoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Ni’imomi daga Allah baa lama b ace ta mutuman kirki ko lala.Misali Annabi Suleiman (AS) da Balkisa dukansu biyu Allah ya huwace masu da ni’imomi  ba iyaka amma daya Monzon Allah ne dayar kuwa  sarauniya kafira.

Na biyu:Mutane yawancinsu na tunanin hukuma na tasiri a rayuwar mutane  da taka rawar gani a lamura da suka shafi addini da imani.

To yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 26 da 27 a cikin wannan sura ta Namli:

 

 اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ

26-Shi ne Allah Wanda babu wani sarki sai Shi ,Ubangijin Al’arshi mai girma.

 

قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ الْكَاذِبِينَ 

 

27-Sai Sulaimana ya ce: To za mu duba ko ka yi gaskiya ko kuwa ka zama cikin makaryata.

Alhud-hud a cikin rahotonsa yana mamakin yadda wadannan mutane na yankin saba’a ke bautawa Rana da cewa me yasa bas u bautawa Allah wanda ya fito da tsirrai a samai da kasai  da sanin duk wani abu da suka boye da bayyanawa a sarari kuma mai kudura da irada da zartar da duk abin da ya so masani mabuwayi mai haskaka zucciya.

 A mahangar Hud-hud hatta Suleiman a matsayinsa na manzon Allah  da karfin iko na zahiri  ba za a yi masa bauta  saboda iliminsa takaitacce ne  hatta labarin yankin Saba’a da mutanen yankin ya buya a gare shi  don Allah ne kadai ya cancanci a bauta masa masanin komi da kowa a wannan duniya  da zartar da duk abin da ya so  kuma Shi ne mai iko na karshe.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: Yin bauta wani lamari ne na fidira a tsawon tarihi mutum na kaddasa abubwan da yake rayuwa da su kama da duwatsu da dabbobi da mutane wani lokaci da bauta masa wani a kan hanyar neman abin bauta na hakika wani kuma ya fada tarkon shaidan.

Na biyu:Abubuwa na dabi’a kamar rana da wata da tsirrai da sauransu na tasiri a rayuwa amma Ba su suka halicci kansu ko suka halicci waninsu ba  don haka Allah wanda ya halicci rana Shi ne ya cancanci a yi wa bauta da sujjada ba ran aba ko wani daga cikin halittu.

3- Burin Shaidan shi ne tushen duk wani sabo da mutane ke aikata da kayatar masu da ayyukansu munana da hana su yi wa Allah sujada a matsayinsa na mahalicci mabuwayi masani.

4- Allah Shi ne masani na karshe wanda babu wani abu da ke boyuwa a gare.

******************MUSIC**********

To daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 28 da 29 a cikin wannan sura ta Namli.

 

اذْهَب بِّكِتَابِي هَذَا فَأَلْقِهْ إِلَيْهِمْ ثُمَّ تَوَلَّ عَنْهُمْ فَانظُرْ مَاذَا يَرْجِعُونَ 

 

28-Ka tafi da wannan wasikar tawa sai ka jefa musu ita sannan ka ja da baya kadan ,sai ka ga da me za su mayar da martani?

 

قَالَتْ يَا أَيُّهَا المَلَأُ إِنِّي أُلْقِيَ إِلَيَّ كِتَابٌ كَرِيمٌ

 

29-Sai ta ce: Ya ku wazirai, hakika an jefo min wata wasika mai girma.

 

Annabi Suleiman (AS) bayan da ya saurari wannan rahoto na Hud-hud  da kawo dalili gamsesshe kan rashin kasancewarsa a cikin tawagarsa sai ya janye maganar hukumtar da shi saboda muhimmancin wannan rahoto nasa kuma na bukatar bincike  don haka Annabi Suleiman (AS) ya rubuta wasika  da wa Hud-Hud domin kai wag a Sarauniyar Saba’a da tsayawa domin ganin amsar da za su bayar. Kuma rubuta wasika domin kiran wata al’umma zuwa ga kadaita Allah da bauta wani salo ne na annabawa da manzonni a tsawon tarihi  kamar yadda tarihi ya tabbatar da Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa yayi rubuta irin wannan wasika domin kiran sarakunan Roma da Iran zuwa ga karbar addinin musulunci.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: a lamari na kiran mutane zuwa da karbar gaskiya dole a yi la’akari da yanayi da kuma amfani da duk wani salo da damar da ta samu,wani lokaci jawabi wani lokacin kuwa rubuta wasika ko aika manzo na musamman.

Na biyu:Rayawar wasu kar ta hana mu yin bincike kamar yadda Annabi Suleiman (AS) yayi bai dogara da labarin da Hud Hud ya bayar sai da yay i bincike da samin tabbaci.

To masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin wannan shiri Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na ke cewa wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barkatuhu.

Add comment


Security code
Refresh