An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 12:47

Suratul Naml Aya Ta 18-22 (Kashi Na 680)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

************MUSIC*********

To madallah kuma yanzu za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun ayoyi na 18 da 19 a cikin wannan sura ta Namla.

 

حَتَّى إِذَا أَتَوْا عَلَى وَادِي النَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَةٌ يَا أَيُّهَا النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ وَجُنُودُهُ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

 

18- Har dai zuwa lokacin da suka iso wani wuri da ake kira Wadin Namli na kasar Sham, sai wata tururuwa ta ce: Ya ku wadannan taron tururuwa,ku shige gidajenku kada Sulaiman da rundunoninsa su ruguza ku ba kuwa da saninsu ba.

 

فَتَبَسَّمَ ضَاحِكًا مِّن قَوْلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَى وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَدْخِلْنِي بِرَحْمَتِكَ فِي عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ

 

19-Sai yayi dariyar murmushi saboda maganarta,kuma y ace: Ubangijina Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imar da Ka yi min ni da mahaifana,da kuma yadda zany i aiki nagari wanda z aka yarda da shi,kuma ka shigar da ni da rahamarka cikin bayinka nagari.

 

A cikin shirin da ya gabata mun kawo bayanin yadda Allah madaukakin sarki ya bawa Annabi Dauda da Suleyman ilimi da kudura kuma suka jagoranci al’umma cikin adalci da hikima a yankin Sham da sauran yankuna da ke dabra da sham. Wadannan ayoyi na nuni da wani lamari mai muhimmanci  da matsayi babba na hukuma  da zama kashin bayan hukuma wato runduna da sojoji da cewa: wani bangare na mutane da aljannu da dabbobi suna yi wa Annabi Suleiman hidima karkashin rundunar su kuma duk lokacin da ya so zartarwa kawai za su yi da abkawa makiya.

Wata rana Annabi Suleiman (AS) da rundunarsa mai girman gaske sun fito a tsakiyar daji sai wata tururuwa ta cewa sauran yan uwanta cewa : ku shige gidajenku  ga Annabi Suleiman (AS) da rundunarsa na zuwa kar su take ku ba tare da sun sani ba. Annabi suleyman (AS) ya fahimci abin da wannan tururuwa ke nufi cewa duk shugaba mai adalci hatta dabbobi da kwaru bai kamata a cutar da su ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

1-Mutum na da karfin sarrafa hatta aljanni ya taimaka masa a bangarori daban daban.

2- Tsari da karfi da tsayin daka na nuni da karfi da girman runduna wajen fuskantar makiya kuma wannan wani lamari ne da rundunar annabawa ta banbanta da ta sauran.

3-dabbobi na hassashen bala’I da hadarin da za su fuskanta da isar da sako ga junansu.

4-Waliyan Allah a doran kasa hatta tsirrai da kwaro bas u cutarwa sun aba su kariya da aminci.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 19 a cikin wannan sura ta Namli:

 Lokacin da Annabi Suleiman (AS) ya ji bayanin tururuwa tana cewa yan uwanta ku yi hankali da shiga gida kar rundunar Annabi Suleiman (AS) su tattake ku ba tare da su sani ba cikin mamaki da al’ajabi annabi Suleyman (AS) yayi murmushi da mamakin yadda wannan tururuwa  take tunanin ceton yan uwanta a bangare guda tata a karkashin hukumarsa za a cutar da wani abu ko da kuwa kwaro ne maras karfi a matsayin zalunci da sani ko ajahilce ,da gangam ko kan kuskure. Saboda haka ya daga hannunsa yana yin godiya ga Allah wanda ya halicce shi da bas hi wannan bauwa da wadata kuma wanda yayi masa dukan wadannan ni’imomi Shi da babansa da kuma uwarsa.Kuma duk wani aikin alheri da ya aikata a karshin mulkin da Allah y aba shi don neman yardarm allah ne  yay i da neman karshen rayuwa mai alheri da zama cikin bayun Allah salihai na gari.

 

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:daya daga cikin abubuwan da ya kamata jagoran  da shugaban al’umma ya kasance yana da shi ,shi ne yalwar kirji da karbar shawara da sukan mai suka don gyarawa kamar yadda Annabi Suleyman (AS) yayi lokacin da ya ji bayanin tururuwa.

Na biyu:godiya ga Allah kan ni’imomin da y aba mu ba ta fatar baki ba kawai fahimta ta k=gaskiya  da aikata Alheri  da yi wa bayun Allah hidima wannan ma godewa Allah ne.

Na uku;ayyukan alheri na da matsayi da daraja kuma babban matsayinsu neman yardarm Allah da kusanci a gare shi ba neman karbuwa ga mutane ba.

**************MUSIC*************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 20 zuwa 22 a cikin wannan sura ta Namli.

 

 وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَائِبِينَ

20- Kuma ya bincika tsuntsaye,sai y ace : Me ya sa ban a ganin hud huda,ko kuwa yana cikin wadanda bas a nan ne?

 

لَأُعَذِّبَنَّهُ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَذْبَحَنَّهُ أَوْ لَيَأْتِيَنِّي بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ

 

21- Wallahi zan yi masa azaba mai tsanani,ko kuma wallahi zan yanka shi,ko kuma lallai ya zo min da hujja kwakkwara.

 

فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِ وَجِئْتُكَ مِن سَبَإٍ بِنَبَإٍ يَقِينٍ

 

22-Sai ko ba da dadewa ba ya dawo,sannan bayan an tambaye shi yace: Ni fan a gano abin da ba ka sani ba m na kuma zo maka da sahihin labara daga birnin Saba’u.

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa hatta tsintsaye suna karkashin ikonsa da kawo masa rahoto kan abubuwa da dama  a fadin yankin sham.To a cikin wannan ayoyin da muka saurara  suna cewa ne :a tsakar tafiya sai ya daga kansa ya kalli rundunar tsintsaye da key i masa inuwa sai bai ga Alhud-hud ba jkuma ya fahimci a zahiri bay a nan  kuma ya jima bay a nan  kamar yadda tsarin hukuma yake  sai ya ce: idan Alhud hud  ya tafi tafiyarsa ne ba tare da wani dalili ba mai karfi zai fuskanci hukumci mai tsanani da rasa ransa  sai dai idan ya kawo hujja da dalili kan rashin kasancewarsa tare da mu.

Ba a jima da wannan maganar ba  sai ga Alhud-hud ya tafi gurin Annabi Suleyman (AS)  ya bayyana cewa; Ni na tafi yankin Saba’a ne kuma a gurin nag a wani abin mamaki da b aka taba jin labarinsa ba amma ni gashi na zo maka da labarinsa. A fakaice Alhud-hud yayi bayanin dalilin rashin kasancewarsa tare da rundunar Annabi Suleyman (AS) kuma Annabi (AS) ba zai hukumta shi ba.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: bincike da sanin halin wadanda ke rayuwa tare da kai sira ce ta waliyan Allah.

Na biyu: Karfin fahimta da salon tafiya da al’umma abubuwa ne da ya kamata jagoran al’umma ya kasance yana da su. Kamra yadda annabi suleyman (AS) yayi a hukumarsa.

Na uku: a tsari na hukuma da tafiyar da hukuma ba a son nuna rauni da sako sako dole a hukumta duk wani mai laeifi daidai da leifin da ya aikata domin hakan zai zama darasi ga sauran mutane.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au a madadin duk wadanda suka tallafa a cikin shirin nay au ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahmatulla……

Add comment


Security code
Refresh