An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 12:34

Suratul Naml Aya Ta 12-17 (Kashi Na 679)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC*********

To madallah yanzu kuma za mu fara shirin na yau da karatun aya ta 12 a cikin sura Namli:

 

وَأَدْخِلْ يَدَكَ فِي جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاء مِنْ غَيْرِ سُوءٍ فِي تِسْعِ آيَاتٍ إِلَى فِرْعَوْنَ وَقَوْمِهِ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ

 

12-Kuma ka saka hannunka cikin wuyan rigarka,zai fito fari fat ba na cuta ba, wannan aya ce daga cikin ayoyi tara zuwa ga fir’auna da mutanensa .Hakika su sun kasance mutane ne fasikai.

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa Annabi Musa (AS) a kan hanyrsa ta komawa Masar tare da iyalansa Allah y aba shi wasu alamomi na mu’ujiza da matsayin manzonsa da cewa: kan yadda sandar da ke hannunka za ta koma macijiya karama da hakan ya tsorata annabi Musa (AS). To amma a wannan ayar ta kara yin nuni da wata alama ta mu’ujiza ta biyu da Allah ya bawa Annabi Musa (AS) da cewa; ka sanya hannunka a aljihunka z aka fito da shi fari mai haske kuma wannan haske ba wata rashin lafiyaba ce ko sihiri.Kuma Allah ya ci gaba da cewa Annabainsa Musa (AS) da cewa: wadannan mu’ujizozi biy bas u kadai ba ne akwai wasu gyda bakwai na daban da z aka iya amfani da su a lokacin da kake kiran fir’auna da al’ummar bani Isra’ila zuwa ga kadaita Allah da bauta da kuma kafa masu hujjoji na karshe.

Daga cikin mu’ujizozin akwai buga sandarsa kan teku ya tsage hanyoyi 12 su bayyanaa a kogin nilo ko maliya. Kuma haka aka yi lokacin da rundunar zalunci ta fir’auna da shi kansa fir’auna suka biyo  Bani Isra’ila da annabi Musa (AS) inda ya buga sandarsa sai hanyoyi 12 suka bayyana shi da Bani Israla suka bi suka fice cikin amincin Allah. Haka a wani lokaci ma ya buda sandar tasa kan wani dutse ko tsoni idanuwan ruwa sha biyu suka bayyana.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Wannan duniya da duk abin da ke cikinta Allah ne ya halicce su kuma shi ke sarrafa su yadda ya ga dama kuma waninsa ba zai iya yi ba.

Na biyu: Wasu mutane na nacewa kan ci gaba da riko da hanyar bata da tabewa ko mu’ujiza ba ta iya canja masu wannan mummunan hali nasu sai sun ga mu’ujizozi da dama watakila su yi imani da bada gaskiya.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 13 da 14 a cikin wannan sura ta Namli:

 

فَلَمَّا جَاءتْهُمْ آيَاتُنَا مُبْصِرَةً قَالُوا هَذَا سِحْرٌ مُّبِينٌ

13-  Sannan lokacin da ayoyinmu wadanda suke a sarari suka zo musu,sai suka ce: Wannan sihiri ne mabayyani.

 

وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ

 

14-  Suka kuma musanta su don zaluntansu sun sakankance da su.To sai ka dub aka ga yadda karshen mabarnata ya kasance.

 

وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ عِلْمًا وَقَالَا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي فَضَّلَنَا عَلَى كَثِيرٍ مِّنْ عِبَادِهِ الْمُؤْمِنِينَ

 

15-  Hakika kuma Mun bai wa Dawuda da Sulaimana ilimi.suka kuma ce Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya fifita mu a kan masu yawa daga bayinsa muminai.

 

وَوَرِثَ سُلَيْمَانُ دَاوُودَ وَقَالَ يَا أَيُّهَا النَّاسُ عُلِّمْنَا مَنطِقَ الطَّيْرِ وَأُوتِينَا مِن كُلِّ شَيْءٍ إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْفَضْلُ الْمُبِينُ

16-Sulaimana kuma ya gaji Dawuda ,ya kuma ce: Yak u wadanda mutane, watau Yahudawa ,An sanar da mu zancen tsuntsaye ,kuma an ba mu daga kowane abu na tafiyar  da mulki,ba shakka wannan lallai ita ce bayyananniyar falala.

 

وَحُشِرَ لِسُلَيْمَانَ جُنُودُهُ مِنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ وَالطَّيْرِ فَهُمْ يُوزَعُونَ

17-Aka kuma tattara wa Sulaimana rundunoninsa na aljanu da mutane da kuma tsuntsaye,sai aka rika killace su rukuni –rukuni.

Annabi Musa (AS) ya tafi  gurin fir’auna da fadawansa don isar da wannan sako na Allah na kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta amma fir’auna da fadawansa bayan sun ga mu’ijizar da Annabi Musa (AS) ya zo da ita duk da haka suka ki yin imani da Shi sai ma suka zarge Shi da bokanci da sihiri.Ci gaban ayoyin na cewa: wannan zargi nasu bai samo asali daga shakku da rashin sani ba  a’a sun fahimci bayani da sakon da Annabi Musa (AS) ya zo da shi da kyau kawai girmankai da ganin sun fi karfin yin biyayya ga mutuman da ke kasa da su a cikin jama’a sai suka bijirewa wannan kira na gaskiya.Don haka Fir’auna da mukarrabansa sun tabka babban guskure da sabo mai girma na zargin Annabi musa da bokanci da sihiri kuma hakan ya tabbata lokacin da suka nice da hallaka a cikin kogin maliya .

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:matsayin imani ya zarta na ilimi da yakini domin shi imani amincewa da gaskiya ne idan ta bayyana ga mutum sabanin ilimi.

Na biyu:Daya daga cikin abin da ke hana mutum karbar gaskiya akwai girman kai da ji da fifiko.

Na uku:Karshen kafirci da ayyukan kafirai hallaka da tabewa.

 

**********MUSIC*********

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 15 da 16 a cikin wannan sura ta Namli

Bayan bayani kan abubuwan da suka faru tsakanin annabi Musa (AS) da kuma yadda aka hallakar da fir’auna da mutanasa da suka kafircewa kiran shiriya da tsira da sakon da Annabi Musa (AS) ya zo masu da shi daga Allah madaukakin sarki.Sai wadannan ayoyi da muka saurara suka fara bayanin tarihin annabi Dawuda da annabi Sulaiman suma Annabawa da aka turowa Banio Isra’ila kuma tarihinsu ya sha banban da tarihin sauran annabawa hatta tsarin hukumarsu. Idan sauran annabawa da sun fuskanci takurawa daga mutanansu wasu ma da fitar da su daga inda suke rayuwa to amma Annabi Dawud da Suleiman (AS) Allah y aba su karfin iko da kudura ta mulki kan  mutanansu hatta aljannu suna karkashin ikonsu ba mutane kadai. Wadannan ayoyi sun yi nuni da dalilin karfin iko da hukumar Dawuda da Suleiman (AS) shi ne ilimi da Allah ya basu da sauraran maganganun kowa hatta dabbobi kuma sun fadada mulkinsu da daukaka su a tsakanin sauran al’ummomin lokacinsu. Duka wannan wani lutifi ne daga Allah madaukakin sarki.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Ilimin annabawa ladunni ne daga Allah masani.

Na biyu:Addani bay a rabuwa da siyasa kuma ta wannan hanya ce mumunai za su yaki zalunci da azzalumai da kafa hukumarsu.

Na uku:Lafiyar da hukuma dole ya kasance karkashin ilimi ba son rai ba.

Na hudu:Duk wani abu da z aka samu daga ilimi  da ni’imomin wani lutifi ne daga Allah da girmamawa daga gare shi ba tsantsanta ba.

Da kuma wannan ne muka kawo kawo karshen wannan shiri nay au a madadin wadanda suka taimaka a wannan shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma da na gabatar na ke cewa wassalam alaikum .

Add comment


Security code
Refresh