An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 12:23

Suratul Naml Aya Ta 6-11 (Kashi Na 678)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**********MUSIC*********

To madallah za mu fara shirin na yau da sauraren karatun aya ta  6 a cikin suratul Namli.

 

وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى الْقُرْآنَ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ عَلِيمٍ

 

6-    Hakika kuma kai lallai ana yi maka wahayin Alkur’ani ne daga wajen Allah Gwani Masani.

 

Suratul Namli ta fara ne da bayani kan girma da matsayin kur’ani da rawar da yake takawa wajen shiryar da mumunai da sa’adarsu.Dagan ta ci gaba da bayani kan abubuwan da mumunai suka kebanta da sauran mutane  sai kuma mumunar makomar wadanda bas u yi imani da lahira ba ranar sakamako. Ci gaban ayoyin wannan sura ta Namli  kafin fara bayani kan takaitaccen tarihin Annabawa da manzonni (AS) wannan aya ta shidda ta fara da cewa; wannan littafi wato kur’ani ya kumshi ilimi da hikima daga Allah.Ilimin Allah da bay a da karshe ,Allah ya sanan duk wani alkheiri da lala  na mutum da aljana.Kuma haka khikimarsa na kumshi a cikin takalifin da ya rataya kanmu da dokokin da ya shata mana da duk wanda ya kiyaye zai isa da kusanci ga Mahaliccinsa.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Kur’ani  littafi ne na ilimi da hikima kuma wanda aka sabkar kansa wannan kur’ani iliminsa ladunni ne.

Na biyu:hukumce-hukumcen  addini ya samo asali daga ilimi daga Allah kuma a cikin kowane daya daga cikin hukunce-hukuncensa akwai hikima ko da kuwa ba mu riski hakan ba.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 7 zuwa ta 9 a cikin wannan sura ta Namli.

 

إِذْ قَالَ مُوسَى لِأَهْلِهِ إِنِّي آنَسْتُ نَارًا سَآتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ آتِيكُم بِشِهَابٍ قَبَسٍ لَّعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ

7-  Ka tuna lokacin da Musa yace da iyalinsa.Hakika ni na hango wuta ,to zan je in zo muku da labara,ko kuma in zo muku da garwashin wuta don ku ji dimi.

 

فَلَمَّا جَاءهَا نُودِيَ أَن بُورِكَ مَن فِي النَّارِ وَمَنْ حَوْلَهَا وَسُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

 

8-  Lokacin da ya zo mata (wutar sai aka kira shi cewa ,an yi albarka ga wanda yake kusa da wutar  Watau Musa,da wadanda suke dabra da ita watau malaiku,kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

 

يَا مُوسَى إِنَّهُ أَنَا اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ 

 

9-  Ya musa hakikar lamarin dai ,Ni ne Allah Mabuwayi Gwani.

 

A cikin wannan sura za mu ji takaitaccen tarihin manzonni biyar(AS) masu girma da daukaka a gurin Allah  da kuma yadda al’ummominsu suka bijirewa kiransu da kafircewa da kuma yadda suka hallaka. Da farko za mu fara ne da yadda aka aiko Annabi Musa (AS). Kamar yadda ya zo a tarihi . A lokacin da annabi Musa (AS)  tare da iyalansa ya bar Annabi Shuaibu (AS) domin komawa Yankin Masar.  Cikin dare a kan hanyarsa  sai ya bada ga tsananin sanhi da  iska da ambaliyar ruwa. Annabi Musa (AS) yana neman hanyar tsira da shi da iyalansa haka kwatam sai ya tsinkayi wuta nesa da su sai y ace : tabbas ga wasu sun kunna wuta  bari in je wajensu don su taimaka mana.To amma  ba zai iya tafiya da iyalinsa ba  saboda tana yuyuwa yan fashi ne da kwace don haka y ace wa iyalinsa ku tsa a nan  har inje in komo ko in zo maku da labarin hanayr da za mu samu tsira ko in zo muku da  garwashin wuta don kubuta daga wannan tsananin sanyi.

Lokacin da ya iso gurin wannan wuta babu wani a kusa da ita  sai dai abubuwan mamaki  da ya gani.Wutar tana fitowa daga iccen da dukan jikinsa tshanwa shar ne kuma duk inda ya motsa hasken wutar na bins aba tare da ya wutar da shi   ko kona shi ba. Wannan lamari ya sake tsoratar da shi da ja da baya. Sai kuma ya ji an kirayi sunansa  kai Musa karka ji tsoro.Ni ne Allah Mabuwayi Mai Hikima,Ina son in aike ka zuwa Fir’auna a matsayin manzoNa. Wannan wutar ma alama ce ta karfi da kudurata ba za ta cutar da kai ba kuma ba za ta wutar da wannan icce ba da duk wani abu da ke kewayen nan  kuna cikin aminciNa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Annabawa (AS) na rayuwa cikin sauki kamar sauran mutane. Musa (AS) domin biyan bukatar iyalinsa  sai gashi ya samu matsayi mai girma na manzonci daga Allah.

Na biyu: Idan Allah ya kudurta  hatta wuta ba za ta kuna ko cutar da wani daga cikin bayunsa kamar yadda ta zama mai salama ga Annabi Ibrahim (AS) lokaci da makiyansa da makiya Allah suka kulla masa makirci da cutarwa.

********************music*************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 10 da ta 11 a cikin wannan sura ta Namli.

 

وَأَلْقِ عَصَاكَ فَلَمَّا رَآهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَانٌّ وَلَّى مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ يَا مُوسَى لَا تَخَفْ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ الْمُرْسَلُونَ

 

10-Kuma ka jefa sandarka. To lokacin da ya gan ta tana jujjuyawa kamar macijiya,sai ya juya da baya bai waiwaya ba.Allah ya ce :Ya Musa ,Kada ka ji tsoro,Hakika Ni manzanni bas a jin tsoro a wurina.

 

إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْنًا بَعْدَ سُوءٍ فَإِنِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ

11-Sai dai wanda ya zalunci kansa ,sannan ya musanya kyakyawa bayan mummuna,to hakika Ni  Mai gafara ne Mai jin kai.

Adabi’ance bayan da Musa ya ji an kiraye shi da ganin wutar da ba ta cutarwa magana tana fitowa sai ya fara shakku tayaya zan tabbatar abin da na ji maganar Allah ce .Sai Allah ya umarce shi da ya yada sandar da ke hannunsa ,ba da wata wata ba yayi abin da Allah ya umarce shi ,yin haka ke da wuya sandarsa ta koma maciji a gabansa yana nufarsa , sai tsoro ya kama Musa saboda bai yi tunanin ganin hakan ba mamaki ya kama shi.Sai aka sake kiransa Kai Musa wannan alama ce ta manzoncinka  kuma abin da ka gani  mu’ujiza ce  ka tafi da ita zuwa da al’ummarka  domin su samu nucuwa kai manzonn Allah  ba mai sihiri da bokanci ba.

 

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu abubuwa guda uku:

Na farko:Muujiza lamari ne daga Allah ba bukata ba ta manzonni don haka babu wani mutun da zai iya kawo muujiza sai da yardar Allah .

Na biyu: Shi azzalumi kulum yana cikin tsoro da fargaba ba cikin aminci da nucuwa ba.

Na uku: Gafarar Allah tana risker bawansa bayan aikin alheri da gyara sabon da ya aikata.

A nan ne kuma muka kawo karshen shirin nay au  amadadin wadanda suka tallafa a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damgaram da na gabatar na ke cewa wassa…

Add comment


Security code
Refresh