An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 12:06

Suratul Naml Aya Ta 1-5 (Kashi Na 677)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

-------------------------------/ 

To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 1 da ta 2 a cikin suratul Namli.

طس تِلْكَ آيَاتُ الْقُرْآنِ وَكِتَابٍ مُّبِينٍ

1-Da sin ,Allah ne Ya san abin da yake nufi da wannan.Wadannan ayoyi na Alkur’ani ne kuma littafi mabayyani.

 

هُدًى وَبُشْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ

2-Kuma shiriya da albishir ne ga muminai.

Wannan sura ta Namli kamar sauran yan uwanta surori 28 ta fara ne da Haruffa da babu wanda ya san ma’anarsu sai Allah mai hikima gwani masani da haka ke nuni da girman Kur’ani. Da bayani kan ayoyin kur’ani a fayyace kuma a bayyanai da fayyace gaskiya da karya .Wannan kur’ani littafi ne na shiriya ga dukan mutane amma a fili take duk wanda yaki bada gaskiya da yin imani wannan sa’ada ba za ta riske shi ba. Saboda haka duk wanda yayi imani ku’ani zai zamia masa littafin shiriya da tsira duniya da lahira. Ayoyin da aka sabkar zuwa ga manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa sune aka hada a cikin kur’ani wani lokaci kira shi da sunan Littafi domin karantawa ga jama’a ta hanyar limamin tsira da sahabbansa.

 

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka;

Na farko: akullum su Annabi da manzonni (AS) a shirye suke wajen isar da sakon Allah da shiryar da al’umma.

Na biyu: Kur’ani mai tsarki littafi ne na tsira da shiriya da bushara da gidan aljanna ga wadanda suka aika ayyukan alheri.

Na uku: Bushara da lada a gaskiya yana gomawa ne ga mutanan da suka karbi tsira da shiriya zuwa da Allah.

*********************MUSIC**************

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 3 zuwa ta 5 a cikin wannan sura ta Namli

 

الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُم بِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ

3-    Wadanda suke tsai da salla,suke kuma ba da zakka suna masu sakankancewa da ranar lahira.

 

إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمْ أَعْمَالَهُمْ فَهُمْ يَعْمَهُونَ

 

4-    Hakika wadanda ba sa ba da gaskiya da ranar lahira Mun kawata musu ayyukansu,sai suka rika faganniya.

 

أُوْلَئِكَ الَّذِينَ لَهُمْ سُوءُ الْعَذَابِ وَهُمْ فِي الْآخِرَةِ هُمُ الْأَخْسَرُونَ

 

5-  Wadannan su ne wadanda mummunar azaba take a kansu,kuma su ne suka fi tabewa a lahira.

 

Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da muka saurara ne a farkon wannan shiri da suke bushara ta alheri ga mumunai wadanda a aikace suke sabke farillu da suka rataya kansu na farko kan aiki na biyu ya shafi tunani. Na farko yin salla da fitar da zakka yayinda na biyu yin imani da lahira da nucuta da tabbacinta. Duk wand aba ya da daya daga cikin wadannan wannan lamura biyu  imaninsa bai cika ba amma  kuma bayan sallah da fitar da zakka shi ne yin imani da rayuwa bayan mutuwa wato lahira to ya rago domin yin imani da rayuwar lahira yana cikin gimshikin addini da kara kusanci da Allah ta hanyar watsi da dodar duniya da dukiya. A fili yake duk wanda bai amince da yin imani da ranar lahira a gurinsa aikin alheri da lala daya ne bas u da bambanci kuma ba ruwansa da azabar da take jiranshi a lahira bayan yayi watsi da gidan aljanna da aka yi wa wanda ya aikata aikin alheri tanadi. A cikin ayoyi da daman a alkur’ani sun yi nuni da yadda shaidan ke kyayatawa wasu mutane ayyukan lala su koma masu kyau a idanunsu. Wasu kuma sun nutsu a aikin sabo har ya zame masu bas u ganin aikin sabon a matsayin mai muni da zama al’ada a gare su. Don haka a kullum mu kasance masu kaucewa ayyukan bata da masu muni da yin istgfari da neman tsari daga aikin shaidan da rundunarsa .

 

Daga cikin wadannan ayoyi za mun ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Daya daga cikin lamarin da ya banbanta addinin musulunci da sauran addinai a yau shi ne dangantaka ta kud da kud tsakanin mutane da Allan ta hanyar kyautatawa mabuka.

Na biyu:wasu bala’o’in da muke fuskanta a rayuwa da shiga matsaloli sun samo asali ne daga munanan ayyukanmu yayinda wasu ayyukan alheri da haskaka mana rayuwa.

Na uku: Yin imani da rayuwa bayan mutuwa da rayuwa a lahira zai taimaka mana a ayyukan da muke aikatawa yayinda wanda bai yi imani ba zai ci gaba da aikata sabo da nisanta daga kusantar Allah.

Na hudu: Rashin yin imani da lahira babbar tabewa ce ga dan adam duniya da lahira.

To masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa har shirin ya kamala  ni da na shirya kuma na gabatar nake cewa wasallamu alaikum wa rahamatulllah.

Add comment


Security code
Refresh