An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 27 January 2016 09:03

Suratush Shu'ara Aya Ta 63-68 (Kashi Na 658)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

*****************MUSIC*************

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 217 zuwa 220 a cikin wannan sura ta shuara’a.

 

وَتَوَكَّلْ عَلَى الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ

 

217- Ka kuma dogara ga Mabuwayi Mai rahama.

 

 

الَّذِي يَرَاكَ حِينَ تَقُومُ

 

218- Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi don yin salla.

 

وَتَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ

219- Da kuma yayin jujuyawarka cikin masu sujjada.

 

إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ 

220- Hakika Shi Mai ji neMasani.

 

A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Allah madaukakin sarki ya bawa manzonsa umarnin mayar da amsa kan maganganun maras tushe da ya kamata da makiya kafirai da mushrikai ke fada.To a yau ayoyin da muka saurare ci gaban wannan umarni ne  da cewa manzon rahama da yayi hakuri da kokarin yin tawakkali da Allah saboda Shi Allah mai nasara da galaba ne kan komi da kowa ,Idan ya kudurta babu wani abu ko wani da zai iya jurewa kudurasa. Idan kuka yi dubi a cikin tarihin annabawa da manzonnin da suka gabata za ku fahimci haka ku kalli makomar fir’auna da namrudu duk da karfin ikoknsu da tarin dukiya  sun hallaka da daukaka annabi Musa (AS) kamar yadda aka hallakar da al’ummomin da suka kafircewa kiran annaba da manzonni (AS) a baya.

Ci gaban ayar na cewa:Allah madaukakin sarki a kullum da kowa ne lokaci yana tare da kai ko da a lokacin da kake sallah da ibadodi a tsakanin jama’a ko da a lokacin da kake kiran mushrikai zuwa ga kadaita Allah da bauta.Ma’ana a dukan lokaci yana ji yana ganin abin da kake yi kuma masani ne kan komi ko zai taimaka maka don haka ka yi tawakkali da allah da ci gaba da riko da hanyar shiryar da al’umma da jurewa adawar kafirai .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:a maimakon ka yi dogaro da dukiya da matsayi na sahiri mafi dacewa shi ne dogaro da Allah madaukakin sarki wanda babu wani abu ko wani a wannan duniya da zai yi galaba kansa.

Na biyu: waliyan Allah suna cikin kulawa ta musamman ko da a lokacin da suke cikin yin ibada.

Yanzu kuma za mu saurari karatun  aya ta 221 zuwa 223.

 

هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَى مَن تَنَزَّلُ الشَّيَاطِينُ

 

221- Shin ba Na ba ku labara ba game da wanda shadanu suke saukar masa?

 

تَنَزَّلُ عَلَى كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ 

 

222- Suna sauka ne kan duk wani makaryaci fajiri.

 

يُلْقُونَ السَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَاذِبُونَ

 

223- Suna kasa kunne gamaganganun shaidanun ,yawancin su kuwa makaryata ne.

 

Wadannan ayoyi da muka saurara sun sake kawo wani daga cikin zargin makiya maras tushe da mushrikai da kafirai key i kan Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarka kuma suna cewa shaidan ne yake gayawa manzo wasu maganganu  bugu da kari cewa: Shaidan yana rudar matane makaryata da karfafa masu yada fasadi da sabo da yada karyayyaki. To wannan zargi nasu ya sabawa hankali da tunani na hakika domin Shi Manzon a rayuwarsa ba a taba saminsa da karya kuma su kansu Mushrikan makka sun shaida hakan da saninsa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana da aikata gaskiya.Shi kum taba saminsa da yin karya da yanzu za ku zarge shi da raya karya da cewa sakon da ya zo maku da shin a alheri daga shaidan ne ? Bugu da kari abubuwan da ke kumshe a cikin kiransa babu wani abu face tsarkake zucciya ,alheri da aikata ayyukan alheri da kuma nisantar zalunci da fasadi .alhali shi shaidan yana maida hankali ne wajen yada banna da fasadi da batar da mutane da sanya wasiwasi a cikin zukatansu.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Zukatan da suka gurbata wasiwasin shaidan yana ratsa su.

Na biyu: Karya  da makaryaci wani babban gumshiki ne na aikata banna da sabo da aikin shaidan da kuma yake ratsa zucciyar mutum shi shaidan din.

****************MUSIC***********
Daga karshe za  mu saurari karatun aya ta 224 zuwa 227 a cikin shu’ara’a.

 

 وَالشُّعَرَاء يَتَّبِعُهُمُ الْغَاوُونَ

 

224- Mawaka kuwa batattu ne suke bin su.

 

أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ

 

225- Ba ka san cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne lamari ba?

 

 وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ

 

226- Hakika kuma suna fadar yin abin da ba sa aikatawa.

 

إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيرًا وَانتَصَرُوا مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ

 

227- Sai dai wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan  an zalunce su. Wadanda suka yi zalunci kuwa ba da dadewa ba za su san kowace makomar za su koma.

Wadannan ayoyi sun zo ne a karshen surar Shu’ara’ kuma suna bayani ne kan daya daga cikin zargin makiya kan manzon Rahama (SWA)  da amsa masu da cewa:Manzo shi ba mawaki ba ne kuma dukan maganganunsa gaskiya kwai suka kumsa ba hassashen mawaka ba .

Abin lura a nan a lokacin da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bayyana .mawaka da dama ne ke rayuwa a yankin Hijaz kuma duk wakokinsu sun kumshi ta’assubanci jahiliya da soyayya tamkar mafarki da yake yake a tsakanin kabilu da fifita wani ko wata kabila kan karya da hakan ke kara masu karfin guiwa da nuna jarumta kuma a duk shekara a birnin Makka ana tara mawaka domin nuna da zabar wakar da tafi fice da kafa ta a jikin dakin Ka’aba. Don haka Mushrikan maka suke danganta sakon da Manzon Rahama ya zo da shi da wake irin na su domin kaucewa gaskiya da gangan da kaucewa karbar gaskiya da kawao rudani a tsakanin jama’a.Shi wake bisa al’ada bay a aiki da hankali da hujjoji na hankali kawai kawo misali da yayi hannun riga da hakika kamar cewa wani zaki ne ,giwa ko nuna shi da wata dabba mai rauni  da zurfafawa ko da kuwa aikin wannan mutum sam bai daidai da abin da wannan mawaki ke fada ba. Daga cikin mawaka ana samin wadanda ke yin tunani da fadin gaskiya da fadin kusan abin da wani ke aikatawa amma sai sun kasance ma’abuta tunani da aiki na alheri kamar yadda kur’ani yayi nuni da su da cewa; mawaka mumunai salihai wakokinsu na karfafawa mutane ga tunawa da Allah  da fadakar da su daga barci kan aikata sabo da banna a tsakanin jama’a ,su azzalumai su sani za su hallaka ,su kuwa mumunai su ci nasara.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Ita kwarewa nada amfani  musamman wadda aka yi tunani kanta da taimakwa jama’a isa da tsira  ba wadda za ta kai mutane ga bata ba.

Na biyu: a musulunci wake yanada matsayi  amma wanda ke fadin gaskiya da karfafawa mutum ga karba da aiki da gaskiya da ruhin imani.

Na uku:Kur’ani ya sabawa wake domin  Shi kur’ani littafi ne na shiriya da shiryarwa da karfafa ruhin mumunai da sanya nutsuwa a ciki da wajen zukatan mumunai.

Na hudu:Allah bay a zaluntar kowa  sai dai ya shirya amma ga wanda ya so shiriyar.

 

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Add comment


Security code
Refresh