An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 27 January 2016 09:02

Suratush Shu'ara Aya Ta 224-227 (Kashi Na 676)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

*****************MUSIC*************

 

****************MUSIC***********
Daga karshe za  mu saurari karatun aya ta 224 zuwa 227 a cikin shu’ara’a.

 

 وَالشُّعَرَاء يَتَّبِعُهُمُ الْغَاوُونَ

 

224- Mawaka kuwa batattu ne suke bin su.

 

أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ

 

225- Ba ka san cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne lamari ba?

 

 وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ

 

226- Hakika kuma suna fadar yin abin da ba sa aikatawa.

 

إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيرًا وَانتَصَرُوا مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ

 

227- Sai dai wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan  an zalunce su. Wadanda suka yi zalunci kuwa ba da dadewa ba za su san kowace makomar za su koma.

Wadannan ayoyi sun zo ne a karshen surar Shu’ara’ kuma suna bayani ne kan daya daga cikin zargin makiya kan manzon Rahama (SWA)  da amsa masu da cewa:Manzo shi ba mawaki ba ne kuma dukan maganganunsa gaskiya kwai suka kumsa ba hassashen mawaka ba .

Abin lura a nan a lokacin da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bayyana .mawaka da dama ne ke rayuwa a yankin Hijaz kuma duk wakokinsu sun kumshi ta’assubanci jahiliya da soyayya tamkar mafarki da yake yake a tsakanin kabilu da fifita wani ko wata kabila kan karya da hakan ke kara masu karfin guiwa da nuna jarumta kuma a duk shekara a birnin Makka ana tara mawaka domin nuna da zabar wakar da tafi fice da kafa ta a jikin dakin Ka’aba. Don haka Mushrikan maka suke danganta sakon da Manzon Rahama ya zo da shi da wake irin na su domin kaucewa gaskiya da gangan da kaucewa karbar gaskiya da kawao rudani a tsakanin jama’a.Shi wake bisa al’ada bay a aiki da hankali da hujjoji na hankali kawai kawo misali da yayi hannun riga da hakika kamar cewa wani zaki ne ,giwa ko nuna shi da wata dabba mai rauni  da zurfafawa ko da kuwa aikin wannan mutum sam bai daidai da abin da wannan mawaki ke fada ba. Daga cikin mawaka ana samin wadanda ke yin tunani da fadin gaskiya da fadin kusan abin da wani ke aikatawa amma sai sun kasance ma’abuta tunani da aiki na alheri kamar yadda kur’ani yayi nuni da su da cewa; mawaka mumunai salihai wakokinsu na karfafawa mutane ga tunawa da Allah  da fadakar da su daga barci kan aikata sabo da banna a tsakanin jama’a ,su azzalumai su sani za su hallaka ,su kuwa mumunai su ci nasara.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Ita kwarewa nada amfani  musamman wadda aka yi tunani kanta da taimakwa jama’a isa da tsira  ba wadda za ta kai mutane ga bata ba.

Na biyu: a musulunci wake yanada matsayi  amma wanda ke fadin gaskiya da karfafawa mutum ga karba da aiki da gaskiya da ruhin imani.

Na uku:Kur’ani ya sabawa wake domin  Shi kur’ani littafi ne na shiriya da shiryarwa da karfafa ruhin mumunai da sanya nutsuwa a ciki da wajen zukatan mumunai.

Na hudu:Allah bay a zaluntar kowa  sai dai ya shirya amma ga wanda ya so shiriyar.

 

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Add comment


Security code
Refresh