An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Dubi A Rayuwar Salihai

Dubi A Rayuwar Salihai (25)

Tuesday, 18 November 2014 14:46

Hikayar Annabi Lũɗu {1}

Written by
A shirinmu na wannan mako zamu fara tabo wani abu ne daga cikin hikayar Annabi Lũɗu {a.s} da ya kasance daga cikin Annabawan Allah Madaukaki masu girman daraja, kuma Annabi Lũɗu {a.s} ya kasance daga cikin makusantar Annabi Ibrahim {a.s} kuma dan uwansa na jini, sannan tare suka yi hijira daga yankin Babil na kasar Iraki zuwa Palasdinu, bayan nan Annabi Ibrahim {a.s} ya tura shi zuwa garin Sadum da a halin yanzu yake kasar Jordan domin kiran mutanen yankin  da suka shahara a fagen aikata munanan dabi’u da gudanar da barna a bayan kasa zuwa ga tafarkin shiriya. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:45

Hikayar Annabi Salihu {3}

Written by
A karshen ‘yar takaitacciyar hikayar da muka gabatar muku ta Annabi Salihu {a.s} da Samudawa zamu ambaci wasu ‘yan darussa da zamu iya dauka a cikin hikayar kamar haka:-
Tuesday, 18 November 2014 14:43

Hikayar Annabi Salihu {2}

Written by
A shirinmu da ya gabata mun fara magana ne kan hikayar Annabi Salihu {a.s} da Allah Madaukaki ya aiko shi zuwa ga kabilar Samudawa, inda ya kira su zuwa ga bautan Allah shi kadai ta hanyar kauracewa bautar gumaka da suka sassaka da hannayensu, kuma Annabi Salihu {a.s} ya dauki matakan tunasar da su irin tarin ni’imomin da Allah ya yi musu tare da fayyace musu damar da suke da ita na tuba daga zunubansu tare da samun rahamar Allah Madaukaki, amma sai Samudawa suka nuna kokwantansu kan gaskiyar da ta je musu, don haka Annabi Salihu {a.s} ya dauki matakin yi musu gargadi kan mummunan sakamakon da zai sauka a kansu matukar suka doge a kan tafarkinsu na kafirci da sabawa umurnin mahalicci, sai a biyo don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:41

Hikayar Annabi Salihu {1}

Written by
A shirinmu na wannan mako zamu fara gabatar muku da hikayar Annabi Salihu {a.s} ne da ya kasance daga cikin Annabawan Allah Madaukaki da aka aiko su domin shiryar da al’umma zuwa ga tafarkin madaidaici, inda Annabi Salihu {a.s} ya kirayi mutanensa da ake kira da Samudawa zuwa ga kadaita Allah Madaukaki tare da gudanar da bauta a gare shi. Hakika kabilar Samudawa sun zo ne bayan Adawa, kuma sun kasance a kan tafarkin bata da rudun rayuwa ta hanyar gudanar da bauta ga gumakan da suka sassaka da hannayensu, don haka Allah Madaukaki ya aiko musu da Annabi Salihu {a.s} a matsayin manzo da zai ‘yantar da su daga duhun kafirci zuwa ga hasken shiriya. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:40

Hikayar Annabi Hudu {4}

Written by
A karshen takaitacciyar hikayar da muka gabatar muku ta Annabi Hudu {a.s} zamu karkare shirin ne da ambato wasu daga cikin darussa da zamu iya dauka a hikayar kamar haka:-
Tuesday, 18 November 2014 14:38

Hikayar Annabi Hudu {3}

Written by
A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Hudu {a.s} da mutanensa; a cikin shirinmu daya gabata mun tabo batun mummunan matakin da Adawa suka dauka ne na butulcewa kiran Annabi Hudu {a.s} tare da zabarwa kansu tafarkin kafirci gami da daukan matakan muzantawa da yin kazafi kansa ta hanyar zarginsa da hauka da rashin gabatar musu da kwararan dalilai da zasu gamsar da su kan ingancin kiran nasa, don haka Annabi Hudu {a.s} ya dauki matakin gargadinsu kan fuskantar azaba daga Allah Madaukaki. To a karshen dan takaitaccen hikayar ta Annabi Hudu {a.s} zamu tabo irin hukuncin da Allah ya zartar kan Adawa ne da suka yi girman kai tare da kafircewa sakonsa. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.
Tuesday, 18 November 2014 14:36

Hikayar Annabi Hudu {2}

Written by
A shirinmu da ya gabata mun fara sauraren hikayar Annabi Hudu {a.s} ne da Allah Madaukaki ya aiko domin shiryar da mutanensa bayan da suka koma kan tafarkin bata da shirka a bayan Annabi Nuhu {a.s}, inda Annabi Hudu {a.s} ya dauki matakin mai da su kan hanyar kadaita Allah Madaukaki tare da yin watsi da gumakan da suka sassaka da hannayensu kuma suke musu bauta a matsayin iyayen gijinsu. To a wannan mako zamu tabo irin mummunan matakin da Adawa suka dauka ne wajen butulcewa kiran dan uwansu Annabi Hudu {a.s}, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:35

Hikayar Annabi Hudu {1}

Written by
A shirinmu a wannan mako zamu fara gabatar da hikayar Annabi Hudu {a.s} ne da ya kasance daga cikin Annabawan Allah Madaukaki da aka aiko domin shiryar da al’umma zuwa ga kadaita Allah da gudanar da bauta a gare shi, kuma Annabi Hudu {a.s} ya zo ne bayan da al'umma suka sake komawa kan tafarkin shirka bayan tsawon shekaru masu yawa da barin Annabi Nuhu {a.s} duniya, kuma an aiko Annabi Hudu {a.s} ne ga mutanensa da ake kira da Adawa. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:33

Hikayar Annabi Nuhu {3}

Written by
A hikayar da muka fara gabatar muku ta Annabi Nuhu {a.s} a cikin shirinmu da ya gabata mun tabo irin gwagwarmayar da Annabi Nuhu {a.s} ya gudanar ne a fagen kiran mutanensa zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki tsawon lokaci tare da irin tsaurin kai da kekashewar zuciya da suka nuna ta hanyar bijirewa duk wata gaskiyar da ta zo musu har ta kai ga matakin da suka fito fili suna kalubalantarsa da ya zo musu da azabar da yake yawan musu gargadi idan har ya kasance daga cikin masu gaskiya, to a cikin shirinmu na wannan mako zamu fara tabo umurnin da Allah Madaukaki ya yi ne ga Annabi Nuhu {a.s} na sassaƙa jirgin ruwa a matsayin shimfidar saukar azaba a gare su, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Tuesday, 18 November 2014 14:30

Hikayar Annabi Nuhu {2}

Written by
A shirinmu da ya gabata mun fara gabatar muku da hikayar Annabi Nuhu {a.s} ne da ya kasance daga cikin manyan annabawan Allah mafiya girman matsayi a bayan kasa da aka aiko domin shiryar da mutane zuwa ga bautan Allah Madaukaki, amma mafi yawan mutanensa suka butulce wa gaskiyar da ta je musu ta hanyar yin riko da tafarkin kafirci, suna masu kafa hujja da wasu raunanan dalilai ta son rai, to a cikin shirinmu na wannan mako zamu ji irin matakan da kafirai suka dauka dangane da kiran da Annabi Nuhu {a.s} ke yi a gare su, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
Page 2 of 2