An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 15 March 2015 16:08

Hikayar Annabi Ibrahim {11}

A karshen ‘yar takaitacciyar hikayar Annabi Ibrahim {a.s} da ke gabatar muku, a wannan mako zamu ƙarƙare hikayar ce ta hanyar ambaton kissar babbar jarabawar da aka yi wa Annabi Ibrahim {a.s} ta hanyar umurtansa da ya dauki matakin yanka ɗansa Isma’il da aka azurta shi bayan tsawon shekaru yana begen samun haihuwa da kuma irin gagarumar nasarar da ya samu a fagen cin jarabawar ta hanyar sallawa umurnin Allah Madaukaki ba tare da yin tababa ko shakka ba, sai a biyo mu don jin abin da shirin namu ya kunsa:-

 

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki tsawon lokaci da matarsa Saratu ba tare da samun haihuwa ba, kuma zuciyar Annabi Ibrahim {a.s} tana begen samun haihuwa, ganin haka matarsa Saratu ta shawarce shi kan ya auri kuyangarta Hajara, bayan auren Hajara kuwa sai Allah Madaukaki ya azurta Annabi Ibrahim {a.s} da ɗa kuma ya rada masa suna Isma’ila. Hakika Annabi Ibrahim {a.s} kasance cikin murnar samun haihuwa tare da gudanar da kyakkyawar tarbiya ga ɗan nasa, har zuwa lokacin da Isma’il ya kai matsayin matashi tare da fara taimakawa mahaifinsa game da ayyukansa na rayuwa, sai kuma ga umurnin Allah Madaukaki kan Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin yanka wannan ɗa nashi Isma’il? Hakika wannan wata babbar jarabawa ce gare shi.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul- Saffati daga aya ta 101 zuwa 110 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:-

“Sai Muka yi masa bushãra da yãro mai haƙuri”.

“Sannan a lõkacin da ya kai matsayin yin aiki tãre da shi, sai ya ce: Ya ƙaramin ɗãna, Lalle haƙĩƙa na ga inã yanka ka a cikin mafarki, To, sai ka yi tunani, mẽ ka gani? (Yãron) ya ce: Ya Bãbãna, Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so daga mãsu haƙuri”.

“Sannan a lõkacin da suka mika kai ga al’amarun Allah, (Ibrahĩm) ya kwãntar da shi ta gẽfen gõshinsa {da nufin yanka shi}”.

“Kuma sai Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!”.

“Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin, Lalle kamar haka ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa”.

“Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananniya”.

“Kuma Muka fanshe shi da abin yanka mai girma”.

“Kuma Muka bar (kyakkyawan yabo) a kansa ga na baya”.

“Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm”.

“Kamar haka ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce dangane da babbar jarabawar da ya fuskanta a kan ɗansa Isma’il kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Wata rana Annabi Ibrahim {a.s} ya roki Ubangijinsa Allah Madaukaki kan ya azurta shi da yara nagari salihai, yana mai cewa: “Ya Ubangijina Ka yi mini baiwar {ɗa} daga mutane nagari”. Sai kuwa Allah ya azurta shi Isma’il da Is’hak. Bayan da Isma’il ya girma har zuwa matsayin matashi maji karfi da zai taimakawa mahaifinsa tare da masa rakiya zuwa duk wajen da zai je, a cikin wani dare sai Annabi Ibrahim {a.s} ya yi mafarki da a ciki ya ga yana yanka ɗan nasa Isma’il, hakika wannan mafarki ya kasance wani umurni ne daga Ubangijin talikai kan ya yanka babban ɗansa. Sakamakon haka Annabi Ibrahim {a.s} ya fuskanci ɗansa Isma’il ya ce masa: “Ya ƙaramin ɗãna, Lalle haƙĩƙa na ga inã yanka ka a cikin mafarki, To, sai ka yi tunani, mẽ ka gani?  Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ba yana nufin neman shawarar ɗansa ko yana kokwanto kan cika umurnin Allah ba ne, iyaka dai yana son sanin matsayin ɗan nasa ne dangane da umurnin Allah, sai amsar ɗansa Isma’il ta zo a matsayin amsar ɗa mai kaunar gamuwa da Allah fiye da son rayuwar duniya, inda ke cewa: “Ya Bãbãna, Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so daga mãsu haƙuri”.

Bayan nan sai Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki ɗansa Isma’il ya tafi da shi kan dutsen Minnah, kuma a lokacin da suka isa kan dutsen na Minnah sai Isma’il ya ce: Ya mahaifina ka daure ni da igiya domin kada na motsa a lokacin da kake cika umurnin Allah Madaukaki, saboda ina tsoron motsin da hannaye da kafafuna zasu yi a lokacin da kake yanka ni, su rage yawan ladar da zan samu a wajen Allah. Ya mahaifina ka wasa kaifin wukar da zaka yanka ni da ita saboda na samu saukin zafin yanka, sannan kafin nan; Ya mahaifina ka cire tufar da ke jikina domin kada mahaifiyata taga jini, hakan ya janyo mata rashin juriya da hakuri. Bayan nan ka isar da sakon gaisuwata gare ta, kuma idan babu matsala ka gabatar mata da tufata domin ta rike shi a matsayin abin da zata dinga tuna ni ta hanyar tufar, watakila hakan ya rage mata tsananin damuwa sakamakon jin kamshin ɗanta, kuma rungumar tufar ta sanyaya mata zuciya a duk lokacin da zuciyar ta yi kunci.

Bayan kammala dukkanin shirye-shiryen aiwatar da umurnin Allah Madaukaki, ganin yadda Isma’il ya mika wuya ga lamarin Allah, hakan ya sanya Annabi Ibrahim {a.s} ya rungume shi yana sumbantar fuskarsa, sai dukkaninsu biyu suka fashe da kuka da take fayyace irin karayar zuciyar ɗan- Adam a yayin rabuwar masoya tare da shaukin gamuwa da Allah Madaukaki, inda Annabi Ibrahim {a.s} ke cewa ɗansa Isma’il madalla da irin wannan haɗin kai da kaba ni domin aiwatar da umurnin Allah Madaukaki, sannan ya sanya wuka mai kaifi a wuyar ɗansa Isma’il kuma ya ja da karfi cikin sauri domin hutar da shi zafin yankar, kuma duk da cewar zuciyar Annabi Ibrahim {a.s} tana bugawa amma duk da haka son Allah ya shige gaban duk wata alaka da take tsakanin ɗa da mahaifi, sakamakon haka ba tare da nawa ko kokwanto ba, Annabi Ibrahim {a.s} ya cika umurnin Allah Madaukaki, sai dai duk da kaifin wukar Annabi Ibrahim {a.s} amma babu wani tasiri da ta yi a wuyar ɗansa Isma’il.

Hakika Isma’il ya ji shiru domin mahaifinsa bai aiwatar da umurnin yanka shi ba, sai yake ce masa: Ya mahaifina yaya ka tsaya, mene ne ke faruwa? Sai Annabi Ibrahim {a.s} ke bayyana masa cewa: Lalle wukar bata tasiri a wuyarka, don haka mike tsaye, babu batun yanka, amma sai Isma’il ke cewa; Ya mahaifina idan yankar ta gagara, to ka soke ni, don haka Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin soke ɗansa Isma’il da tsinin wukar da ke hannunsa, sai dai sukar babu wani tasiri da ta yi a wuyar Isma’il. Hakika Allah Madaukaki shi ne mahaliccin dukkan komai, kuma shi ke bai wa duk wani kaifi ikon yin tasiri wajen yanke abu, don haka bai bada iko wa wukar ta yi tasiri a kan Isma’il ba. Hakika Allah Madaukaki a cikin yalwan iliminsa yana da masaniyar cewa; lalle Annabi Ibrahim da ɗansa Isma’il {a.s} ba zasu taba saba umurninsa ba, bayan nan sai Annabi Ibrahim {a.s} ya ji kira cewa: Ya Ibrahim lalle haƙĩƙa ka gaskata mafarki kan yanka ɗanka, Annabi Ibrahim {a.s} yana dubawa sai ga Mala’ika Jibrilu {a.s} da rago daga aljanna a matsayin fansa ga Isma’il, kamar yadda alkur’ani mai tsarki ke bayyana cewa: “Kuma Muka fanshe shi da abin yanka mai girma”. Wato lalle Allah Madaukaki ya fanshi Isma’il da rago mai girma da albarka.     

More in this category: « Hikayar Annabi Ibrahim {10}

Add comment


Security code
Refresh