An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 15 March 2015 16:03

Hikayar Annabi Ibrahim {10}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s} a cikin shirinmu da ya gabata mun tabo batun bukatar Annabi Ibrahim {a.s} ce ta neman Allah ya nuna masa yadda take rayar da matacce da kumu manufarsa kan gabatar da wannan bukatar gami da girman ikon Allah Madaukaki da ya gani kan rayar da matattu. To a cikin shirinmu na wannan mako zamu tabo wani abu ne dangane da hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} kan zaunar da wasu daga cikin iyalansa a filin saharar da ke Jazirar Larabawa, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Bayan Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki tsawon lokaci da matarsa Saratu ba tare da samun haihuwa ba, kuma shekarun Saratu sun fara nisa, inda tsufa ta fara bijiro mata, sannan zuciyar Annabi Ibrahim {a.s} tana bukatar samun haihuwa, ganin haka Saratu ta shawarci Annabi Ibrahim {a.s} kan ya auri kuyangarta Hajara, inda bayan Allah ya azurta Annabi Ibrahim {a.s} da samun ɗa Isma’ila, amma sai Allah ya umurce shi da ya zaunar da iyalinsa Hajara da ɗanta Isma’ila a Jazirar Larabawa a wajen da babu tsiro ko ruwa, don haka Annabi Ibrahim {a.s} ya cika wannan umurni tare da gabatar da roko kan Allah ya aminta wannan yanki kuma ya ‘yantar da zuriyarsa daga daudar shirka.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratu-Ibrahim daga aya ta 35 zuwa 41 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:- 

“Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: Yã Ubangijina, Ka sanyã wannan gari amintacce kuma Ka nĩsanta ni da kuma ‘ya’yãna daga bauta wa gumãka”.

“Yã Ubangijina, Lalle sũ {gumakan} sun ɓatar da mutãne mãsu yawa, don haka wanda ya bĩ ni, to haƙĩƙa shi yanã tare da ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to lalle Kai Mai gãfara ne Mai jin ƙai”.

“Yã Ubangijinmu, haƙĩƙa ni, na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shũka a cikinsa, a wajen ɗãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu, dõmin su tsayar da salla, kuma Ka sanya zukãtan mutãne sunã karkatowa zuwa gare su, kuma ka azurtã su da 'ya'yan itãce, don su gõdẽ {maka}”.

“Yã Ubangijinmu, haƙĩƙa Kai Ka san abin da muke ɓõyẽwa da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽ ga A1lah daga abin da ke cikin ƙasa da abin da ke cikin sama”.

“Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni Ismã'ila da Is'hãƙa inã halin tsufa. Lalle Ubangijina haƙĩƙa Mai jin addu'a ne”.

“Yã Ubangijina, Ka sanyã ni mai tsayar da salla kuma daga zũriyata. Yã Ubangijinmu, kuma Ka karɓi addu'ata”.

“Yã Ubangijinmu, Ka gãfarta mini da iyayena da kuma mũminai, a rãnar da za a tsayãr da hisãbi”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce dangane da addu’arsa ga Ubangijin talikai kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Hakika matar Annabi Ibrahim {a.s} Saratu ta kasance macen da bata haihuwa kuma tsufa ta fara bijiro mata saboda yawan shekaru, kuma ga shi ba a mata tsammanin haihuwa, sannan zuciyar Annabi Ibrahim {a.s} tana kwadayin samun ɗa a matsayin magaji, sakamakon haka Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin gudanar da addu’a yana rokon Allah Madaukaki da ya wadata shi da ɗa nagari. Hakika matarsa Saratu ta fahimci halin da mijinta Annabi Ibrahim {a.s} yake ciki na bukatar ɗa, don haka ta gabatar masa da bukatar auren baiwarta Hajara watakila Allah ya azurta shi da ɗa ta hanyarta.

Bayan Annabi Ibrahim {a.s} ya auri Hajara guyangar matarsa Saratu, sai kuwa Allah Madaukaki ya azurta shi da samun ɗa kuma ya naɗa masa suna Isma’il, sannan Annabi Ibrahim {a.s} ya amsa umurnin Allah Madaukaki na wahayin da aka masa kan ya dauki matarsa Hajara da ɗanta Isma’il ya tafi da su Makkah. Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya dauke su tare da tafiya da su kasar Makkah har lokacin da ya zo wani waje mai nisa da babu alamar gine-gine, sannan aka umurce shi da yada zango a wajen, bayan nan aka umurce shi da tsugunar da matarsa Hajara da ɗanta  wannan waje, amma a lokacin da Annabi Ibrahim {a.s} ya kama hanya zai barsu a wajen da babu abinci ko ruwan sha, sai Hajara ta biyo shi, inda tausayinta ya nemi hana shi rabuwa da ita, amma saboda cika umurnin Allah haka ya daure ya rabu da ita da ɗansa, ita kuma ta dogara da Allah Ubangijin talikai ta hanyar dawo wa wajen da ta ajiye ɗanta.

Tabbas Annabi Ibrahim {a.s} ya dawo gida zuciyarsa tana wajen matarsa da ɗansa amma nufin Allah ya rinjayi nufinsa don haka ya sallamawa Ubangiji dukkanin al’amuransa yana mai gabatar da roko gare shi cewa: “Yã Ubangijinmu, haƙĩƙa ni, na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shũka a cikinsa, a wajen ɗãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu, dõmin su tsayar da salla, kuma Ka sanya zukãtan mutãne sunã karkatowa zuwa gare su, kuma ka azurtã su da 'ya'yan itãce, don su gõdẽ {maka}”. “Yã Ubangijinmu, haƙĩƙa Kai Ka san abin da muke ɓõyẽwa da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽ ga A1lah daga abin da ke cikin ƙasa da abin da ke cikin sama”.

Hakika Hajara da zauna a wajen da mijinta ya tsugunar da ita da ɗanta suna ci da sha daga guzurin da ya bar musu har lokacin da guzurinsu ya kare, kuma suka shiga cikin halin kishin ruwa, inda ɗanta Isma’il yake watsal-watsal da kafafu saboda kishin ruwa, don haka Hajara ta mike tana dube-duben yankin da take ciki, inda ta tafi ta hau kan wani tsauni da ake kira da Safa ta duba duk wajen da idonta ke iya gani amma babu wata alamar ruwa, don haka ta sauko, kuma ta sake nausawa zuwa daya bangaren har ta kai ga wani tudu da ake kira da Marwa ta duba duk yadda idonta zai iya tsinkaya a yankin amma babu alamar gurbin ruwa, sannan ta dawo zuwa tudun Safa, sannan ta koma Marwa har tafiyarta tsakanin Safa da Marwa cikin sarsarfa ta kai sau bakwai, kuma a lokacin da Hajara take kan tudun Marwa sai ta hango tsuntsu yana shawagi a saman wajen da ta ajiye ɗanta, hakika ganin faruwar haka a bisa al’ada yana nufin akwai abin da ke wakana, don haka Hajara ya gangaro domin ganewa idonta abin da ke faruwa, isarta ke da wuya sai ta ga ruwa yana ɓuɓɓugowa a wajen da ta ajiye ɗan nata, sai kuwa ta duƙa tana kamfatar ruwan da hannayenta tana sha tare da shayar da ɗanta Isma’il har suka koshi.

Wasu mutane daga ƙabilar Jurhum suna shigewa ta kusa da matsugunin Hajara da ɗanta Isma’il da suka ga tsuntsu yana shawagi a saman wajen, sai suka fara tambayar junansu kan dalilin faruwar hakan, saboda hakan wata alama ce ta samuwar ruwa a waje, amma a iyaka saninsu babu wani gurbin ruwa a yankin, don haka suka dauki matakin tabbatar da haƙĩƙanin abin da ke faruwa ta hanyar tura wani mutum daga cikinsu domin ganewa idonsa, sai ga mutumin dauke da busharar cewa ruwa ne ke ɓuɓɓuga a wannan waje, sakamakon haka ƙabilar Jurhum suka zo suka roƙi Hajara kan ta amince musu domin zama tare da ita a wannan waje, amma ruwan ya ci gaba da kasancewa mallakinta, inda Hajara ta amince da shawararsu, sakamakon haka ‘yan ƙabilar Jurhum suka kafa gari tare da zama da Hajara har lokacin da ɗanta Isma’il ya kai matsayin saurayi kuma ya auri ‘yar ƙabilar ta Jurhum kuma ya koyi harshen Larabci daga gare su.

        

Add comment


Security code
Refresh