An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 14 March 2015 21:59

Hikayar Annabi Ibrahim {9}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s}, a cikin shirinmu da ya gabata mun tabo wani abu ne dangane da muhawarar da ta gudana tsakanin Annabi Ibrahim {a.s} da azzalumin Sarki Namrudu da ke jayayya kan samuwar Allah tare da da’awar cewa shi ma Ubangiji ne kuma yana rayarwa da kashewa, inda Annabi Ibrahim {a.s} ya bukace shi da ya fito da rana daga kusuwar yammacin akasin yadda take fitowa a dabi’arta idan har ya kasance mai gaskiya kan da’awarsa, lamarin da ya rusa da’awar kafirci da Sarki Namrudu ke riyawa kuma rauni da jahilci da karancin tunaninsa suka bayyana ga al’umma. To a shirinmu na wannan mako zamu tabo hikayar bukatar Annabi Ibrahim {a.s} ce ta neman Allah ya gwada masa yadda yake rayar da matacce, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya kasance daga cikin manyan Annabawan Allah madaukaka da girman matsayi da ake kira da Ulul-Azmi da aka aiko da sakon shiriya domin ‘yantar da al’umma tare da dora su a kan tafarkin gaskiya musamman tabbatar musu da samuwar Allah Madaukaki da kadaita shi wajen bauta da kuma yin imani da rayuwa bayan mutuwa wato akidar tashin kiyama domin bayi su riski sakamakon ayyukansu na duniya. Sakamakon haka a fili yake cewa Annabi Ibrahim {a.s} yana da cikakkiyar akida da imani kan tashin kiyama wato rayuwa bayan mutuwa, kuma yana da cikakken imani da tabbaci kan girma da buwayan Allah dangane da ikonsa na rayar da matacce, imanin da ya ginu a kan kwakkwaran dalili na hankali da shari’a, to ko mene ne manufar Annabi Ibrahim {a.s} ta neman Allah ya nuna masa yadda yake rayar da matacce?.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul-Baqara aya ta 260 yana fayyace mana hakikanin hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} kan bukatar da ya gabatar ga Ubangijin talikai kan ya nuna masa yadda yake rayar da matacce da kuma manufarsa ta gabatar da irin wannan tambaya da cewa:-

“Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina, Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu" Ya ce: Shin ko ba ka yi ĩmãni ba ne? Ya ce: Kwarai {nayi imani} amma dai dõmin zũciyãta ta samu nutsuwa; Ya ce: To ka dauki tsuntsãye guda huɗu, ka yanka su gunduwa-gunduwa, sannan kuma ka sanya sassan jikinsu a kan kõwane dũtse, sannan kuma ka kiraye su, zã su zo maka da gaggawa. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, mai hikima”

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce dangane da bukatar da ya gabatar ga Allah Madaukaki kan ya nuna masa yadda yake rayar da matacce da dalilin da ya sanya shi gabatar da wannan bukata kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Wata Annabi Ibrahim {a.s} yana shigewa ta gefen bakin teku, sai ya ga gawar wani mutum a bakin tekun, gefen jikinsa a cikin ruwa kifaye suna ci, kuma bangaren jikin da yake kan kasa dabbobi suna ci, ganin wannan yana yi ya wurga Annabi Ibrahim {a.s} cikin tunani kan sake tayar da matattu a ranar kiyama, don haka ya roki Allah ya nuna yadda yake tayar da matattu saboda ya samu yakinin ganin ido, inda ke cewa: “Ya Ubangijina, Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu”. Sai Allah Madaukaki ya ce masa: “Shin ko ba ka yi ĩmãni ba ne?” Sai Annabi Ibrahim {a.s} ya ce: “Kwarai nayi imani, amma dai dõmin zũciyãta ta samu nutsuwa ce” Allah Madaukaki ya ce: “To ka dauki tsuntsãye guda huɗu, ka yanka su gunduwa-gunduwa, sannan kuma ka sanya sassan jikinsu a kan kõwane dũtse, sannan kuma ka kiraye su, zã su zo maka da gaggawa. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, mai hikima”.

Sakamakon haka Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki zakara, tattabara, dawisu da hankaka ya yanka su kuma ya yi gunduwa- gunduwa da namarsu sannan ya cakuda su waje guda, bayan nan ya dibi sassan dabbobi ya rarraba ta hanyar dorawa a kan duwatsu guda goma da suke kewaye da shi, sannan ya tsaya a gefe guda ya kirayi sunayen tsuntsayen kuma a gabarsa akwai ruwa da hatsi, sai gabar jikin tsuntsu daga wannan dutse ya tashi ya tarar da wancan gaba da ke wancan dutse, haka har dukkanin gabobinsa su hadu waje guda, sai tsutsu ya sake dawowa kamar yadda yake tun da fari, sannan ya zo gaban Annabin Ibrahim {a.s} a cikin halittarsa domin cin hatsi da ruwan da ya tanada masa, bayan dukkanin tsuntsayen nan hudu sun sake dawowa kaidin rayuwa, sai suka taru a gaban Annabi Ibrahim {a.s} kuma suka ci hatsin da ruwan da ya tanada musu, sannan suka masa godiya kan ciyar da su da ya yi.

A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu ne daga cikin taskar iyalan gidan Manzon Allah Tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} kamar haka:-

An ruwaito daga Imam Ja’afar Sadiq {a.s} dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: “Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina, Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu” Wannan aya tana daga cikin ayoyi masu fuska biyu wato mutashabiha, inda ma’anarta ke nufin cewa: Annabi Ibrahim {a.s} ya yi tambaya kan yadda ake rayar da matattu, kuma rayar da matattu yana daga cikin ayyukan Allah Madaukaki, don haka rashin sanin masani dangane da yadda ake gudanar da wani aiki, hakan ba aibi ba ne, kuma tambayar bata tauyaye wani abu daga akidarsa ba.

Har ila yau an tambayi Abu-Hasan Imam Ali Arridha {a.s} dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa; “Kwarai {nayi imani} amma dai dõmin zũciyãta ta samu nutsuwa ce”. Shin hakan yana nufin a cikin zuciyarsa akwai kokwanto ne? Sai Imam Ridha {.a.s} ya amsa da cewa: A’a baya nufin akwai kokwanto a cikin zuciyarsa iyaka dai yana bukatar Allah ya kara masa tabbaci da yakini ne a zuciyar tasa.

Add comment


Security code
Refresh