An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 15:04

Hikayar Annabi Ibrahim {8}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s} da mutanensa da suka shahara a fagen bautar gumaka, a shirinmu da ya gabata mun ambaci matakin da Sarki Namrudu da muƙarrabansa suka dauka ne na zartar da hukuncin kisa kan Annabi Ibrahim {a.s} ta hanyar ƙõna shi a gaban idon jama’a saboda rusa gumaka da kuma mu’ujizar da ta bayyana gare su, inda wutar da aka wurga Annabi Ibrahim {a.s} ta zame tamkar dausayi gare shi. Don haka a shirinmu na yau zamu tabo muhawarar da ta gudana tsakanin Annabi Ibrahim {a.s} da Sarki Namrudu ne da ya yi da’awar cewa: Shi ne Ubangiji talikai da ke da ikon rayarwa ko kuma ke kashewa, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.

 

Hakika bayan da Allah Madaukaki ya kubutar da Annabi Ibrahim {a.s} daga makircin Sarki Namrudu da muƙarrabansa na kokarin ƙõna shi a gaban idon jama’a, tabbas hakan ya kai jama’a ga fahimtar gaskiyar sakon kiran Annabi Ibrahim {a.s} ta kadaita Allah Madaukaki, tare da rusa musu akidar ganin kima da tasirin gumaka a cikin zukatansu. Bayan nan hikayar ta ci gaba da fayyace matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka wajen rusa da’awar kafirci ta Sarki Namrudu da ke cewa; Shi ne Ubangiji da ke da ikon rayarwa da kashewa a muhawarar da suka gudanar, inda Annabi Ibrahim {a.s} ta tabbatar wa Sarki Namrudu kasancewarsa bawa mai rauni da ya nadawa kansa rawanin girman kai da dagawa a bayan kasa sakamakon jahilci, karancin hankali da butulci.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul- Baqara a cikin aya ta 258 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:-

“Shin ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi jayayya da Ibrãhĩm a game da {samuwar} Ubangijinsa, dõn Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yake matarwa." Ya ce: "Nĩ ma ina rãyarwa kuma ina kashewa." {Sai Ibrãhĩm} ya ce: "To hakika Allah Yana fito da rana daga gabas, saboda haka sai ka fito da ita daga yamma" Sai wanda ya kãfirta ya ɗimauce. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ne musamman dangane da muhawarar da ta gudanar tsakaninsa da Sarki Namrudu da yake da’awar cewa shi Ubangiji ne saboda giyar mulki da girman kai da dagawa a bayan kasa, kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Hakika bayan da Allah Madaukaki ya rusa makircin Sarki Namrudu da muƙarrabansa na kokarin ƙõna Annabi Ibrahim {a.s}, inda bayan an harba Annabi Ibrahim {a.s} cikin wuta ta hanyar majajjawa, kafin isarsa cikin wutan sai Allah ya umurci wutar da cewa: “Ke wuta, Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm” don haka wutar ta kasance tamkar dausayi ga Annabi Ibrahim {a.s} ganin haka ya sanya Sarki Namrudu tambayar Azara cewa; Ya Azara wani irin daukakan matsayi danka yake da shi a wajen Ubangijinsa? Sannan bayan Annabi Ibrahim {a.s} ya fito daga cikin wutar ya je wajen Sarki Namrudu, inda ya kara jaddada yin kira gare shi zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki, sai Namrudu yake tambayar Annabi Ibrahim {a.s} cewa; Ya Ibrahim shin wane ne wannan Ubangiji naka? Annabi Ibrahim {a.s} ya amsa masa cewa: Ubangijina shi ne mai rayarwa da kashewa, Namrudu ya ce; Ni ma ina rayarwa kuma ina kashewa.

Annabi Ibrahim {a.s} ya tambayi Sarki Namrudu cewa ta yaya kake rayarwa da kashewa? Sai Namrudu ya aika aka zo masa da mutane biyu da aka yanke musu hukuncin kisa, inda ya ce wa daya daga cikinsu tafi na sallameka, sannan ya bada umurnin kashe dayan, sannan ya ce kaga lalle na kashe kuma na raya. Hakika wannan mataki da Sarki Namrudu ya dauka na yin ahuwa ga mutum guda tare da zartar da hukuncin kisa kan guda ta hanyar raba shi da ransa lamari ne da ke fayyace jahilcinsa dangane da manufar rayarwa da kashewa da Annabi Ibrahim {a.s} ke magana kansu. Tabbas Annabi Ibrahim {a.s} yana kokarin fahimtar da Sarki Namrudu cewa ne hakika Allah ne yake bada rayuwa kuma shi ne ke karbar ran bayinsa. Sakamakon haka sai Annabi Ibrahim {a.s} ya ce ga Namrudu, inda har kai mai gaskiya ne kan da’awarka, to ka tada wannan matacce da kasa aka kashe? Sai ya zame babu amsa daga Namrudu.

Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin kau da kai daga wautar Sarki Namrudu ta hanyar sake gabatar masa da wata kwakkwarar hujjar da ba zai taba tunanin furta maganar wauta ba, inda ya ce masa; "To hakika Allah Yana fito da rana daga gabas, saboda haka sai ka fito da ita daga yamma" Wato lalle yana daga cikin ikon Ubangijina a kowace rana da safe yana fitar da rana daga gabashi, to idan har da’awar da kake yi gaskiya ce na cewa kai Ubangiji ne, ka juya akalar lamarin ranar ta fito ta bangaren yammaci? “Sai wanda ya kãfirta ya ɗimauce” Wato hujja ta kare ga Sarki Namrudu ya zame bayi da abin cewa ga Annabi Ibrahim {a.s} sakamakon haka ta bayyana ga al’umma cewa da’awar cewa Sarki Namrudu shi ne Ubangijinsu karya ce tsagwaronta.

A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu ne daga cikin taskar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} kamar haka:- 

Ya zo cikin littafin tafsirin Durul-Mansur na Hafiz Jalaluddeen Suyudi dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: “Shin ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi jayayya da Ibrãhĩm a game da {samuwar} Ubangijinsa” An karbo daga Imam Ali dan Abi-Talib cewa: Wannan da ya yi jayayya da Ibrahim {a.s} game da samuwar Ubangiji  shi ne Namrudu dan Kan’an.

Har ila yau ya zo cikin littafin tafsirin Burhan daga Imam Ja’afar Assadiq {a.s} cewa: Batun jayayya dangane da samuwar Ubanjigi tsakanin Annabi Ibrahim {a.s} da Sarki Namrudu an bayyana cewa batun ya gudana ne bayan wurga Annabi Ibrahim {a.s} a cikin wutar da aka mai da ita sanyi da aminci.             

 

Add comment


Security code
Refresh