An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 15:03

Hikayar Annabi Ibrahim {7}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s} da mutanensa da suka shahara a fagen bautar gumaka, a shirinmu na wannan mako zamu ambaci wani abu ne daga cikin irin darussan da zamu iya dauka a hikayar musamman dangane da matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka na kalubalantar mutanensa da suke riya tasirin gumaka a fagen rayuwa da kuma sabon salon fadakarwa da ya bullo da shi na rusa gumakan domin tabbatar da rashin tasirinsu. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:- 

Dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, {saboda babu abin da zai same ni} sai abin da Ubangijina Yã so”. A cikin wannan ayar zamu iya fahimtar cewa: Annabi Ibrahim {a.s} ya yi kokarin daukan matakin rigakafi ne kan abin da zai faru a nan gaba, inda ke fayyace wa mutanensa da suke da’awar tasirin gumaka a fagen rayuwa cewa; Ya ku mutane na ku sani cewa duk abin da zai faru gare ni a rayuwa lamari ne da ba shi da wata alaka da gumakanku, saboda gumaka wasu abubawa ne da suke sandararru wadanda ba su dauke da ruhi ko ikon amfanar da kansu ko kare kansu daga wata cutuwa, don haka babu yadda wani amfani ko cutuwa zai zo daga gare su, sakamakon haka duk abin da zai faru a kai na lamari ne da zai gudana bisa nufin Allah Madaukaki da yake Ubangijin talikai.

Haka nan dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa; “Kuma yãyã zan ji tsõron abin da kuka yi shirki da shi, alhali ku kuma ba ku tsõron cẽwa lalle kũ kun yi shirki da Allah, abin da kuwa bai saukar muku da wata hujja ba game da shi. To, wani ɓangare daga ɓangarorin biyu ya fi cancanta da samun aminci, idan har kun kasance masu sani?”. Hakika a cikin wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-

A cikin fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Kuma yãyã zan ji tsõron abin da kuka yi shirki da shi”. Zamu fahimci cewa: Lalle mutum baya samun aminci da nutsuwar zuci sai ta hanyar akidar kadaita Allah.

Dangane da fadin cewa; “Abin da kuwa bai saukar muku da wata hujja ba game da shi”. Wannan furuci na Annabi Ibrahim {a.s} dalili ne kan cewa; lalle dole ne a gina akida a kan tubali na hankali da kwakkwarar hujja da zasu katange mutum daga afkawa cikin rudun rayuwa da bata.

Haka nan fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “To, wani ɓangare daga ɓangarorin biyu ya fi cancanta da samun aminci, idan har kun kasance masu sani?”. A cikin wannan muhawara ta Annabi Ibrahim {a.s} da mutanensa zamu fahimci cewa; Annabi Ibrahim {a.s} yana koyar da cewa wajibi ne kada a wofantar da matsayin akidar sauran mutane koda kuwa sun kasance a kan bata, saboda su suna ganin kimar tafarkin da suke kai, don haka idan za a gudanar da muhawara da su, to a fuskance su da kwararan hujjoji da dalilai na hankali domin yin tasiri a cikin zukatansu da tunaninsu.

Dangane da matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka na rusa gumakan mutanensa kamar yadda hikayar ta zo cikin Suratul-Anbiya cewa: “Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan gudanar da shiri a boye na rusa gumãkanku a bãyan kun tafi kuna masu jũya bãya”.

“Sai ya mayar da su guntu-guntu fãce wani babbansu da ya bari, tsammãnin zasu dawo gare shi {don tambayarsa}”.

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya bi mataki-mataki wajen ganin ya shiryar da mutanensa zuwa ga tafarkin shiriya, inda a farko ya fara da matakin kira zuwa ga tahidi wato kadaita Allah Madaukaki yana mai cewa; Wadannan gumaka da kuke bauta musu sandararrun abubuwa ne da kuka sassaka da hannayenku, kuma kuna da tabbacin cewa; lalle ba su dauke da ruhi, sannan ba su magana. Idan kuma kuna riya cewa gumaka ne da kuka gada daga iyayenku, to tabbas kun kasance da iyayenku a kan hanyar bata bayyananniya.

A mataki na biyu Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matsayin fayyace wa mutanensa shiriyar da ta je musu a aikace ta hanyar fahimtar da su cewa; Lalle gumaka ba su da wani tasiri a fagen rayuwa ballantana su amfanar ko cutar, inda ya dauki matakin rusa gumakan a bayan idonsu domin hakan ya kara fayyace musu rudun rayuwar da suke ciki.

A mataki na uku Annabi Ibrahim {a.s} ya kai ga matsayin kure mutanensa a lokacin da suka gurfanar da shi a gaban jama’ar garin kan zargin rusa gumaka, inda suka yi furuci da batarsu suna masu ikrari da zaluntar kansu sakamakon yin riko ga gumaka a matsayin iyayengiji. Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya gabatar musu da kwararan hujjoji da suka ratsa fidira da halittarsu ta dan Adamtaka, kuma ya gabatar musu da dalilai na hankali da suka motsa tunaninsu, sannan ya zarge su kan wofantar da hankalansu tare da sukarsu kan rashin tunani dangane da rudun rayuwar da suka wurga kansu a ciki.

A takaice dai Annabi Ibrahim {a.s} ya bi dukkanin hanyoyin da suka dace waje fadakar da al’ummarsa tare da amfani da dukkanin karfinsa, sai dai a fili yake cewa; Sharadin karbar gaskiya shi ne mutum ya kasance cikin shirin rungumarta a duk lokacin da ta tabbata gare shi, amma babban abin bakin ciki, kadan ne daga cikin mutanen Annabi Ibrahim {a.s} suke shirye su mika kai ga gaskiyar da ta je musu.

Hakika matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka na rusa gumaka tare da mai da su guntu-guntu, mataki ne da ke matsayin rusa akidar bautar gumaka da shafe kimarsu daga zukatan mutanensa, sakamakon haka mutanen nasa suka yi furuci da kasancewarsu azzalumai saboda rikon gumaka a matsayin iyayengiji, kamar yadda alkur’ani mai girma ke fayyace mana cewa: “Sai suka kõma ga {zargin} jũnansu; Sai suka ce: "Lalle kũ dai, kũ ne azzãlumai”.

A fili yake cewa; dukkanin matakan da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka a fagen shiryar da mutanensa, sun kasance a matsayin tubulin wanzar da akidar kadaita Allah a tsakanin al’umma, kuma akalla matakan sun gurgunta kaifin akidar shirka a zukatan mutane tare da sanya alamar tambaya kan bautar gumakan, inda hakan ya zame dalilin fadakar mutane har suka kai ga rungumar gaskiya a karshen lamari, kamar yadda littattafan tarihi suka nakalto.

A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu ne daga cikin taskar iyalan gidan manzon Allah tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s}.

Ya zo cikin littafin tafsirin Durul-Mansur dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:- “Waɗanda suka bada gaskiya, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu”. An karbo daga Abdullahi dan Mas’ud cewa: A lokacin da wannan aya ta sauka, hakan ya wurga mutane cikin damuwa, don haka suke cewa; Ya Manzon Allah ta yaya zai zame ba mu zaluntar kanmu? Sai Manzon Allah {s.a.w} ya ce musu; lamarin ba kamar yadda kuka dauka ba ne, shin ba ku ji abin da Salihin Bawa ke cewa ba ne; Lalle shirka ta kasance zalunci mai girma? Iyaka abin da ake nufin da zalunci a cikin ayar shi ne shirka.

 

 

Add comment


Security code
Refresh