An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 15:02

Hikayar Annabi Ibrahim {6}

A ci gaba da hikayar Annabi Ibrahim {a.s} da muke gabatar muku, a cikin shirinmu da ya gabata mun tabo batun matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka ne na rusa gumakan da mutanensa suke bauta musu a matsayin iyayen giji a lokacin da suke fice daga cikin gari zuwa sahara domin gudanar da bukukuwan sallah, da kuma irin muhawarar da ta gudana a tsakaninsu a lokacin da suka gurfanar da shi a gaban jama’ar gari don tuhumarsa kan dalilinsa na rusa gumakan, inda a karshen lamari ya yi gagarumar nasara a kansu ta hanyar rusa akidar bautar gumaka da ke cikin zukatansu kuma har suka yi furuci da cewa; Lalle sun kasance suna zaluntar kansu sakamakon yin riko da gumaka a matsayin abin bauta. To a cikin shirinmu na wannan mako zamu ji irin mummunan hukuncin da mahukunta suka yanke ne kan Annabi Ibrahim {a.s} domin shafe hasken shiriyar da ya zo musu. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya yi gagarumar nasarar rusa akidar shirka tare da wofantar da kimar da gumaka suke da ita a cikin zukatan mutanensa musamman a lokacin da suka yi furuci da cewa; lalle sun zalunci kansu sakamakon yin riko da gumaka a matsayin iyayen giji, amma kafin wani lokaci sai suka sake komawa kan tafarkinsu na shirka da bata saboda kekashewar zukata, kuma shugabanni daga cikinsu suka hanzarta yanke shawarar kashe Annabi Ibrahim {a.s} saboda ci gaba da rayuwarsa wata babbar barazana ce ga makomar shugabancinsu a kan al’umma, don haka suka fito suna cewa; Hakika babu wani hukunci da ya dace a zartar kan Ibrahim dangane da laifin rusa iyayen gijinsu sai kisa ta hanyar ƙõna shi a gaban idon jama’a.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul-Anbiya daga aya ta 68 zuwa 70 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:-

 “Suka ce: Ku ƙõne shi kuma ku taimaki iyayen gijinku, idan kun kasance mãsu aikatãwa”.

“{Da suka jefa shi a cikin wutar sai}  Muka ce: Ke wuta, Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm”.

“Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri kan shi, sai Muka sanya su mafiya hasãra”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce kan matakin da sarki Namrudu da mukarrabansa suka dauka na ganin sun kawo karshen kiran shiriyar da ya je musu ta hanyar kashe Annabi Ibrahim {a.s} amma sai Allah ya mayar musu da makircinsu kansu kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Bayan da Sarki Namrudu ya ga lalle Annabi Ibrahim {a.s} ya yi nasarar rusa akidar shirka tare da wayar da kan jama’a hakikanin gumakan da suka rika a matsayin iyayen giji ta hanyar fayyace musu rashin tasirin gumakan a fagen rayuwa lamarin da ya wurga Namrudu da mukarrabansa cikin tashin hankali da firgita, don haka Namrudu ya shawarci makusantansa kan neman matakin da ya dace su dauka kan Annabi Ibrahim {a.s} domin ya zame musu babban barazana musamman ga makomar mulkinsu, inda suka cimma matsayar cewa: Su dauki matakin tunzura mutane a kan Annabi Ibrahim {a.s}, don haka suka fara shelanta cewa: “Ku ƙõne shi kuma ku taimaki iyayen gijinku, idan kun kasance mãsu aikatãwa”. Sai aka kama Annabi Ibrahim {a.s} tare da tsare shi a gidan kurkuku, kuma aka umurci jama’a da su hado itatuwa masu yawa domin ƙõna Annabi Ibrahim {a.s}, don haka mutane cikin fushi da nuna kishi ga iyayen gijinsu suka fantsama neman itatuwa sako-sako har lokacin da tarin itatuwa suka zame tamkar tsauni mai girma.

Sarki Namrudu ya sanya an kunna wuta da harshenta ke tozo, kuma saboda tsananin zafinta babu wani tsuntsu da zai ketara ta kanta har sai ya fado a cikinta ƙõnanne, don haka babu wani mahaluki da ke iya kusantar watar. Tabbas ga wuta nan an kunna amma babu hanyar da za a bi wajen wurga Annabi Ibrahim {a.s} a cikinta saboda ba zai yiyu a karato kunsata ba, sunan cikin wannan rudu, sai wani mutum ya bada shawarar wurga Annabi Ibrahim {a.s} a cikin wutar ta hanyar majajjawa, shawarar da ta samu karbuwa, don haka sarki Namrudu ya bada umurnin hanzarta samar da majajjawar. Bayan kammala majajjawa sun fito da Annabi Ibrahim {a.s} tare da sanya shi cikinta da nufin wurga shi cikin wutar.

Kafin aiwatar da umurnin Sarki Namrudu na wurga Annabi Ibrahim {a.s} a cikin wuta, baffansa Azara ya zo yana marin Annabi Ibrahim {a.s} kan ya hanzarta tuba tare da janye maganganunsa na aibanta gumakansu, shi kuma ya yi masa lamunin tseratar da shi daga hukuncin da aka yanke kansa ta hanyar nema masa ahuwa a wajen sarki Namrudu, amma sai Annabi Ibrahim {a.s} da yake daure cikin majjajawa ya doge a kan tafarkinsa na gaskiya tare da jaddada matsayinsa kan bijirewa duk wata hanyar  bata koda kuwa sun dage a kan aniyarsu ta wurga shi cikin wutan da suka tanada.

Bayan nan sai Namrudu ya bada umurnin je fa Annabi Ibrahim {a.s} a cikin wutan, don haka aka harba Annabi Ibrahim {a.s} cikin wutan ta hanyar majajjawar da aka tanada, amma bayan harba shi kafin isarsa cikin wutan Allah Madaukaki ya umurci wutar da cewa; “Ke wuta, Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm”. Sai wutar ta zame dausayi mai ni’ima ga Annabi Ibrahim {a.s} da izinin Allah Madaukaki. Hakika mutanensa sun so shirya masa makirci, amma sai Allah rusa makircin suka zame mafiya hasara da tabewa.

Tabbas Sarki Namrudu da mutanensa sun ga wannan mu’ujiza daga nesa, don haka suka rikice tare da rudewa mutum a cikin wuta tamkar yana cikin dakin shakatawa! Hakika wannan babbar mu’ujiza ta girgiza sarki Namrudu har ta kai shi ga sakin baki yana furuci da cewa; Duk wanda ke neman Ubangiji a matsayin wanda ya cancanci bauta, to ya riki Ubangijin Ibrahima! Wannan subutar baki ya wurga jama’a cikin wani hali na daban, yau ga Sarki Namrudu da kansa yana ikrari da gaskiyar kiran Annabi Ibrahim {a.s} zuwa bautan Allah Makadaici. Ganin haka sai wani daga cikin masu neman fada a wajen sarki Namrudu ya zaburo domin rage kaifin tasirin maganar Namrudu ya ce; Ai shi ne ya umurci wutan kan kada ta kona Ibrahim, fadin haka ke da wuya sai harshen wutar da tartsatsinta suka afka masa nan take ya halaka, karyarsa ta bayyana ga jama’a. Sai sarki Namrudu ya dubi Azara baffan Annabi Ibrahim ya ce masa; Ya Azara wani irin girman matsayi danka yake da shi a wajen Ubangijinsa? Sannan Annabi Ibrahim {a.s} ya fito daga cikin wutar ya zo wajen Namrudu domin kara jaddada yin kira gare shi zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki.  

 

  

Add comment


Security code
Refresh