An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 15:01

Hikayar Annabi Ibrahim {5}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s} mun ambaci kadan daga cikin irin salon matakan da ya dauka a kokarin da yake yi na shiryar da mutanensa zuwa ga hanya madaidaiciya musamman ta hanyar gabatar musu da kwararan dalilai na hankali da na shari’a kan samuwar Allah Ubangijin talikai da kuma irin gagarumar galabar da ya yi a kansu a muhawarar da ta gudana tsakaninsu a lokacin da suke jayayya da shi kan matsayin Allah Madaukaki da da’awar tasirin gumakan da suke bauta musu. A wannan karo zamu ambaci wani sabon salon fadakarwa ne da Annabi Ibrahim {a.s} ya bullo da shi da nufin mai da mutanensa zuwa ga dabi’arsu ta dan Adamtaka ta hanyar yin amfani da hankali. Sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Bayan Annabi Ibrahim {a.s} ya kalubalanci mummunar akidar mutanensa ta bautar gumaka da kwararan dalilai na hankali tare da yin galaba a kanta, kuma mutanensa suka yi furuci da rashin wata madogara kan yin riko da gumaka a matsayin abin bauta, iyaka dai sun tarar da iyayensu ne a kan bautarsu, sai suka bi sahunsu ido rufe, amma duk da haka suka dauki matakin bijire wa gaskiyar da ta je musu, tare da kokarin yin jayayya da Annabi Ibrahim {a.s} kan samuwar Allah suna masu riya tasirin gumaka a fagen rayuwa. Sakamakon haka Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin bullo da wani sabon salon fadakarwa a gare su ta hanyar fayyace musu raunin gumakansu a fili tare da rashin tasirinsu a rayuwa, inda ya rusa gumakan a lokacin da suka fice daga cikin garin domin gudanar da bukukuwan sallar idinsu.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul- Anbiya daga aya ta 57 zuwa 67 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:-

“Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan gudanar da shiri a boye na rusa gumãkanku a bãyan kun tafi kuna masu jũya bãya”.

“Sai ya mayar da su guntu-guntu fãce wani babbansu da ya bari, tsammãnin zasu dawo gare shi {don tambayarsa}”.

“Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu da suke iyayen gijinmu? Haƙĩƙa shi yanã daga cikin azzãlumai”.

“{Wasu} Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatarsu da aibi. Anã ce masa Ibrahĩm”.

“Suka ce: "To {ku je} ku zo da shi kan idanun mutãne, tsammãnin zã su bãyar da shaida {kan zargin da ake yi kansa}”.

“{Bayan sun zo da shi} Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!”.

“Ya ce: "Ã'a, wannan babbansu shĩ ya aikata wannan abu, Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana”.

 “Sai suka kõma ga {zargin} jũnansu; Sai suka ce: "Lalle kũ dai, kũ ne azzãlumai”.

“Sannan aka juyo da kawunansu zuwa ga girman kai da kafirci  {suka ce} "Lalle haƙĩƙa kã sani waɗannan bã su yin magana”.

“Ya ce: To, Shin kwa riƙa bautã wa wani abu da ba Allah ba! Wanda bã zai amfãnar da ku da kõmai ba, kuma bã zai cũtar da ku {komai} ba?”.

“Tir da ku, da kuma abin da kuke bauta wa baicin Allah! Shin bã za ku hankalta ba?”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ce ta Annabi Ibrahim {a.s} kan matakin da ya dauka na rusa gumaka kamar yadda ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

A lokacin gudanar da bukukuwan sallah, al’ummar Annabi Ibrahim {a.s} sun fice daga cikin garinsu zuwa sahara domin gudanar da bukukuwan sallar tasu kamar yadda take a al’ada karkashin jagorancin azzalumin sarkinsu Namrudu, amma sai Annabi Ibrahim {a.s} yak i fita tare da su, sannan a bayan ficewarsu daga garin, sai Annabi Ibarahim {a.s} ya dauki abinci ya tafi wajen bautar gumakansu, inda ya gabatar wa gumakan da abinci yana cewa: “Ashe bã zã ku ci ba?”. “Mene ne ya sa ba kwa magana?” Sannan ya dauki matakin bin gumakan daya bayan daya yana gabatar musu da abinci yana cewa; Ci kuma yi magana, amma babu daya da ya amsa masa, sannan ya dauki gatari ya rusa gumakan, amma sai ya bar babbansu ba tare da ya rusa shi ba, kuma ya dauki gatarin da ya yi amfanin shi wajen rusa gumakan ya rataya a kan kafadar babban gunkin, sannan ya fice daga cikin dakin bautar.

Bayan Sarki Namrudu da mutanensa sun dawo daga Sahara, sun shiga dakin bautar gumakansu sai suka tarar da an rusa gumakan lamarin da ya jefa su cikin dimuwa da kururuwa, suna cewa wane ne ya aikata wannan danyen aiki ga iyayen gijinmu? Wane ne ke da karfin halin aikata wannan babban laifi lalle ya kasance daga cikin batattu, kuma suka ci gaba da neman wanda ke da hannu a wannan lamari, sai wasu jama’a suka ce ai lalle mun ji wani matashi da ake kira da Ibrahim yana aibanta gumakan.

Samun wannan labari kan mutumin da ake zargi da aikata wannan danyen aiki, sai aka tura a zo da shi gaban mutane, kuma jama’a suka famtsama neman Annabi Ibrahim {a.s} har suka gano shi, kuma suka zo da shi gaban taron jama’ar gari, inda jama’a suke kallonsa cikin fushi da bacin rai, sai suka tambayi Ibrahim cewa; "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!”. Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya samu wata babbar damar jiyar da sakon shiriya ga al’ummarsa, domin ga jama’ar gari sun taru a waje guda, sai Annabi Ibrahim {a.s} ya nuna babban gunkin da ya yi saura a tsaye kuma a kan kafadarsa akwai gatari; ya ce wannan babban gunki ne ya rusa sauran gumakan idan har ya kasance yana magana, fasahar wannan magana ta Annabi Ibrahim {a.s} ita ce idan har gunkin baya magana, to lalle ba shi ne ya rusa sauran gumakan ba.

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} yana nufin shiryar da al’ummarsa cewa ne lalle gumaka ba su magana, to don mene ne zasu rike su a matsayin iyayen giji? Wannan furuci na Annabi Ibrahim {a.s} ya yi gagarumin tasiri a cikin zukatan mutanensa, inda suka koma suna zargin kansu kan dalilin bautar abin da baya ji baya gani bayan kuma magana, kuma suka yi furuci da cewa; lalle sun kasance masu zaluntan kansu, amma son rai da dogewa a kan kafirci sai suka nemi nade tabarmar kunya da cewa;   don haka sai suka juyo gare shi suka ce: "Lalle haƙĩƙa kã sani waɗannan bã su yin magana”. Sai Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin sukar lamirinsu kan bautar gumaka duk da cewa sun amince ba su magana, yana mai fayyace musu cewa: “To, Shin kwa riƙa bautã wa wani abu da ba Allah ba! Wanda bã zai amfãnar da ku da kõmai ba, kuma bã zai cũtar da ku {komai} ba?”. “Tir da ku, da kuma abin da kuke bauta wa baicin Allah! Shin bã za ku hankalta ba?”.

  

   

Add comment


Security code
Refresh