An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 15:00

Hikayar Annabi Ibrahim {4}

A ci gaba da hikayar da muke gabatar muku ta Annabi Ibrahim {a.s}, a cikin shirin mun tabo batun matakin da ya dauka na tunkarar baffansa Azara da ya kasance masani ilimin taurari kuma kwararre a fannin sassa gumaka da ake sayarwa ga mutane, domin shiryar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya, amma sai Azara ya kafirce tare da daukan tsattsauran mataki kan Annabi Ibrahim {a.s}. To a cikin shirinmu na wannan mako zamu ci gaba da bijiro da irin matakan da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka ne a fagen tabbatar da akidar tauhidi a tsakanin mutanensa da suka yi nisa a fagen shirka ga Allah Madaukaki ta hanyar gudanar da bautar gumaka, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Hakaki bayan matakan da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka na gabatar da kwararan hujjoji na shari’a da dalilai na hankali kan akidar kaɗaita Allah Madaukaki ga baffansa Azara da kuma mutanensa, kuma bai gushe ba ya ci gaba da gudanar da kira gare su kan su nisanci gurbatacciyar akidarsu ta bautar gumaka tare da yin riko da tafarkin kaɗaita Allah Madaukaki, amma sai mutanensa suka bude fagen muhawara da shi domin kare akidarsu tare da gudanar da jayayya ta hanyar riya cewa gumaka suna da tasiri a fagen rayuwa, don haka suke kokarin tsoratar da shi kan fuskantar fushin gumakansu, amma sai Annabi Ibrahim {a.s} yake mayar musu da martani ta hanyar fayyace girma da buwayar Allah Madaukaki.

“Kuma mutãnensa suka yi jayayya da shi; Ya ce: Shin kunã jayayya da ni a game da Allah, alhãli kuwa hakika Yã shiryar da ni. Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, {saboda babu abin da zai same ni} sai abin da Ubangijina Yã so. Ilimin Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõmai. Shin ba zã ku yi tunãni ba?”

“Kuma yãyã zan ji tsõron abin da kuka yi shirki da shi, alhali ku kuma ba ku tsõron cẽwa lalle kũ kun yi shirki da Allah, abin da kuwa bai saukar muku da wata hujja ba game da shi. To, wani ɓangare daga ɓangarorin biyu ya fi cancanta da samun aminci, idan har kun kasance masu sani?”.

“Waɗanda suka bada gaskiya, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu”.

“Kuma wancan hujjarMu ce Muka bayãr da ita ga Ibrãhĩma a game da mutãnensa. Munã ɗaukaka darajõji waɗanda Muka so. Hakika lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Masani”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} da mutanensa da suka dauki matakin yin jayayya da shi ne domin kare gurbatacciyar akidarsu ta shirka, kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya fara kira ne zuwa ga kadaita Allah Madaukaki yana umurtan mutanensa kan yin watsi da gumaka, amma sai mutanen suka bijirewa kiransa kuma suka doge a kan gurbataccen tunaninsu na shirka, inda suka yi jayayya da shi kan cewa gumaka su ne iyayen gijinsu kuma dole ne sai sun bauta musu, don haka Annabi Ibrahim {a.s} ke ce musu; “Shin kunã jayayya da ni ne game da {samuwar} Allah” kumakuna kira na kan barin tafarkin Allah Ubangijin talikai, “Alhãli kuwa hakika Yã shiryar da ni, kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi” lalle ku sani ba ni tsoron iyayen gijinku, kuma babu wani cutuwa da zata same ni daga gumaka ko taurari ko wata ko kuma rana? Lalle hakika wadannan abubuwa ba su kasance abin bauta da zasu cutar ko kuma amfanarwa ba saboda bijire musu. Tabbas babu wani abin da zai same ni na cutuwa, “sai abin da Ubangijina Yã so” saboda Ubangijina shi ne wannan da ke da dukkanin tasiri a kan bayinsa kuma yake amfanar da su tare da cikakken ikon cutarwa, domin shi ne Ubangijin da iliminsa ya yalwaci dukkan komai, shin hakan bai ishe ku abin tunani ba? Sannan Annabi Ibrahim {a.s} a nashi bangaren ya dauki matakin tsorantar da mutanensa da azabar Allah yana mai fayyace musu cewa: “Kuma yãyã zan ji tsõron abin da kuka yi shirki da shi, alhali ku kuma ba ku tsõron cẽwa lalle kũ kun yi shirki da Allah” ta hanyar samar masa da abokin tarayya a kan tubali da dalili na karya, amma duk wannan fadakarwa ba ta yi amfani ga mutanen ba, sai ma kara dulmiya da suka yi cikin bata da rudun rayuwa.

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya sake bullo da wani sabon salon fuskantar mutanensa gami da baffansa Azara ta hanyar gudanar da muhawara da su a kan dalili na hankali da nufin zaburar da su domin komawa ga hakikanin fidirarsu ta dan-Adamtaka da cewa: “A lokacin da ya ce wa babansa da mutãnensa, mene ne kuke bauta wa?”. “Suka ce; Munã bauta wa gumãka ne saboda haka zamu ci gaba da bautansu”. “Ya ce; Shin suna jin ku  a lõkacin da kuke kiransu?. Hakika amsar wannan tambaya a fili yake ga duk mai hankali cewa; Tabbas gumaka ba su ji koda an kira su domin sandararrun abubuwa ne da ba su jin kira. Sai Annabi Abrahim {a.s} ya ci gaba da gabatar musu da salon kira ta hanyar dalili na hankali da cewa: “Ko kuwa {gumakan} sunã amfãnar da ku, kõ sunã cũtar da ku? Tabbas ala-tilas su amsa da cewa lalle kam gumaka ba su amfanarwa ko cutarwa saboda a dabi’a ta hankali babu yadda sandararren abu da babu ruhi tare da shi zai amfanar ko ya cutar, sai Annabi Ibrahim {a.s} ya ce; To don mene ne dalilinku na gudanar da bauta ga wadannan gumaka da ba su ji, ba su gani sannan  ba su amfanarwa ballantana cutarwa? Sai suka yi furuci da gaskiyar al’amari da cewa: “Ã’a {dalilin dai kawai} shi ne mun  sãmĩ iyayenmu ne suna aikatã kamar haka” mu kuma sai muka kama tafarkinsu a matsayin gado ido rufe.

Tabbas bayan da duk wata hujja ko dalili ya zo karshe ga mutanen Annabi Ibrahima {a.s} da baffansa Azara kuma har ta kai ga matakin yin furuci da gazawarsu a gaban dalilai na hankali, sai Annabi Ibrahim {a.s} ya sake bude fagen shiryar da su zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki da cewa: “To shin kun ga abin da kuka kasance kuna bauta wa”. “Kũ da iyayen naku da suka gabata”. “To haƙiƙa sũ maƙiya a gare ni, sai Ubangijin talikai ne kadai zan riƙa {abin bauta}” Ya mutanena ku sani cewa; Tabbas rikon gumaka a matsayin iyayengiji, wani babban sharri ne da ke wurga mutum cikin rayuwar rudu da zaluntar kai a duniya, sannan ya dauwamar da shi cikin mummunar azabar lahira, sakamakon haka akwai wani abin da ya kai gunmaka zama abin kyamata da daukansu a matsayin abokan gaba? Amma yin riko da Allah Madaukaki “Wannan da shi ne Ya halicce ni, sannan Yake shiryar da ni”. “Kuma wannan da shi ne Yake ciyar da ni, kuma Yake shayar da ni”.  “Kuma idan na yi rashin lafiya, to shi ne zai warkar da ni”. “Kuma shi ne wannan da zai kashe ni, sannan ya {sake} rayar da ni”. “Kuma wannan da nake kwaɗayin ya gãfarta mini kurãkuraina a rãnar ƙiyama”. To shi ne Ubangiji da yake gudanar da al’amuran mutum, kuma shi ne ya cancanci bauta ta gaskiya, amma sai mutanen Annabi Ibrahima {a.s} suka sake bijirewa maganganunsa saboda sun fifita son rai a kan hankalinsu don haka kiran bai yi musu tasiri ba.  

   

          

Add comment


Security code
Refresh