An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:59

Hikayar Annabi Ibrahim {3}

A ci gaba da hikayar da muka fara gabatar muku ta Annnabi Ibrahim {a.s} musamman dangane da matakan da ya dauka na kalubalantar al’ummarsa da suka shahara a fagen bautar gumaka ta hanyar gabatar musu da dalilai na hankali gami da kokarin da ya yi na ganin ya shiryar da baffansa Azara da ya kasance shahararren a fannin sassaka gumaka, a shirinmu na wannan mako zamu ambaci wani abu ne daga cikin irin darussan da zamu iya dauka a hikayar, sai a biyo mu don jin abin da shirin namu ya kunsa:-

Dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: “Kuma kamar haka ne Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni”. Hakika wannan ayar tana fayyace mana cewa: Lalle Annabawan Allah suna samun wata shiriya ta musamman daga wajen Allah Madaukaki, kuma mafi girman wannan shiriya ita ce kai wa ga matakin samun tabbaci da yakini kan al’amuransu. Tabbas wannan wani matsayi ne da babu mai kai wa gare shi, sai zababbun bayi daga cikin talikai.

Hakika yana daga cikin hanyar kafa hujja a kan masu taurin kai da dagawa a bayan kasa; Gwada cewa ana tare da su da nufin jiyar da su shiriyar da ta je musu gami da tabbatar musu da irin gurbataccen tunani da akidar batar da suke kai, saboda a mafi yawan lokuta idan aka raba gari da masu aikata laifi tare da nuna kyamatarsu, to ba kasafai suke tsayawa su saurari nasihar da za a gabatar musu ba. Kamar haka ne Annabi Ibrahim {a.s} ya yi hakurin shiga cikin jama’ar da suke shirka ga Allah ta hanyar bautar taurari, wata da rana, kuma ya yi da’awar fatar baki ta cewa; Wadannan abubuwa sune iyayen gijinsa, sannan bayan bayyanar rauni da rashin cancantarsu ga matsayin bauta, sai Annabi Ibrahim {a.s} ya tabbatar wa al’ummarsa cewa; Lalle Ubangijin talikai da ya cancanci bauta baya dauke da duk wata siffa ta rauni, sannan ya fito fili ya tabbatar musu da bijirewarsa ga abin da suka rika a matsayin iyayen giji. Kamar yadda alkur’ani mai girma ke fayyace mana cewa; “… A lõkacin da dare ya yi duhu a kansa ya ga wani taurãro, ya ce: Wannan ne Ubangijina. Sannan a lõkacin da ya ɓace, sai ya ce: Ba na son mãsu ɓacewa”.

Dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Lalle idan har Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa zan kasancẽ daga cikin mutãne ɓatattu”. Hakika wannan ayar tana fayyace cewa; Tabbas dukkanin Annabawa suna bukatar shiriya daga wajen Allah Madaukaki, kuma lalle shiriya ta hakika tana wajen Allah Madaukaki ne shi kadai, domin Allah ne kadai ke shiryar da wanda yake bukatar shiriya, kuma yake tabar da wanda yake bukatar dulmiyar da kansa cikin bata.

Dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Ya mutãnena! Lalle ni na bijire wa abin da kuka kasance kuna yin shirki da shi”. A cikin wannan ayar zamu ga cewa; duk da dalilai na hankali da hujjoji bayyanannu da Annabi Ibrahim {a.s} ya gabatar ga al’ummarsa amma suka ki hankalta, hakan bai sanya Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin bijire musu ba, a’a cewa ya yi hakika na bijire wa abin da suka kasance kuna yin shirka da shi, domin Annabi Ibrahim {a.s} yana ganin akwai yiyuwar su dawo cikin hankulansu nan gaba tare da rungumar tafarkin Allah Madaukaki.

Dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Yã bãbana! Lalle haƙĩƙa wani abu na ilimi ya zo mini da kai bai je maka ba, sabõda haka sai ka bĩ ni in shiryar da kai hanya madaidaiciya”. A cikin wannan ayar zamu fahimci cewa; Hakika Annabi Ibrahim {a.s} yana son sanar da babansa hakikanin gaskiyar shiriya ce da ta ginu a kan tubali na hankali da kwararan hujjoji na shari’a, inda bayan kokarin dora shi a kan tafarkin yin amfani da hankali da cewa: Yã bãbana! mene ne ya sa kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya amfanar da kai da komai?”. Saikumaya bijiro masa da batun boyayyen ilimi na ghaibu. Hakika a fili yake cewa komai karancin tunani da rashin zurfin basirar mutum yana sane da cewar gunki dai baya ji kuma baya gani ballantana ya yi magana, sannan kuma uwa uba baya da wani tasiri a fagen rayuwar kansa ballantana na wani daban. Sakamakon haka idan har Azara da yake da’awar sani a fannin ilimin taurari da kaifin basirar sassaka gumaka a siffofi daban daban ya yi furuci da wannan hakika, to babu shakka zai fahimci cewa; Lalle tabbas akwai wani ilimi da zai iya zuwa ga mutum daga duniyar ghaibu domin kubutar da mutane daga duhun bata zuwa ga hasken shiriya.

Har ila yau ayar tana fahimtar da mu cewa; Ba zai yiyu mutum a rayuwarsa ta duniya ya kasance ya rasa tafarkin gudanar da tsarin rayuwarsa ba, dole ne kodai ya kasance yana bin tafarkin Allah Madaukaki a matsayin hanyar tsira, ko kuma hanyar Shaidan a matsayin hanyar bata. Sakamakon haka ya zame dole a kan mutum ya zurfafa tunani da hangen nesa kan zabar ingantaciyar makoma da zata kai shi ga rayuwar aminci duniya da lahira ko kuma ya zabarwa kansa hanyar gudanar da rayuwa cikin rudu da koyi da al’adun magabatansa ido rufe.

Haka nan Annabi Ibrahim {a.s} ya yi amfani da salon magana ta hikima da furuci mai dadi wajen fuskantar baffansa Azara, inda yake kiransa da suna na girmamawa da nuna ladabi gare shi, inda ke ce masa; Ya babana. Hakika wannan al’amari ne da ke fayyace mana cewa; Dole ne duk wani mai kira zuwa ga tafarkin gaskiya ya kasance yana amfani da hankali da zurfin tunani gami da matakan girmamawa da nuna kauna ga mutanen da yake son shiryar da su, saboda an halicci zukatan mutane a kan son wanda ya kyautata mata tare da kin wanda ya munanta mata. Sannan yana kan masu shiryarwa daukan matakin gargadi da tsoratarwa ga masu girman kai da dagawa musamman a lokacin da suka doge a kan ayyukan laifukansu.  

Dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa: “Yã bãbana! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Haƙĩƙa Shaiɗan ya kasance mai saɓo ne ga Allah Mai rahama”. Wannan aya tana nuni da  cewa ne lalle Annabi Ibrahim {a.s} ya gargadi baffansa da cewa; Hakika tsawon lokacin da ka dauka kana gudanar da shirka ga Allah ta hanyar bautar gumaka, hakan zai sanya Allah Mai rahama da rahamarsa ta game dukkan komai ya yi fushi da kai tare da azabtar da kai. Don haka Ya babana ka yi dubi kan girman hatsarin da ka wurga kanka ciki sakamakon yin shirka ga Allah Madaukaki. Har ila yau Annabi Ibrahim {a.s} ya sanar da baffansa Azara cewa; Lalle sakamakon aikinsa shi ne kasancewa majibinci ga Shaidan, saboda Azara shahararre ne a fagen sassa gumaka domin sayarwa ga mutane don su bauta musu, lamarin da yake matsayin babbar hanyar yada akidar bautar gunki a tsakanin mutane tare da yin shirka ga Allah Madaukaki a bayan kasa.

A gefe guda kuma dangane da fadin Annabi Ibrahim {a.s} cewa; “Yã bãbana! Lalle inã ji maka tsõron wata azãba ta shãfe ka daga Allah”. Haka nan yana nuni da cewa ne lalle Annabi Ibrahim {a.s} ya kasance cikin damuwa da bakin cikin ganin baffansa Azara ya afka cikin halaka da zata dauwamar da shi a cikin azaban Allah Madaukaki.

 

Add comment


Security code
Refresh