An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:57

Hikayar Annabi Ibrahim {2}

A shirinmu da ya gabata mun fara gabatar muku da hikayar Annabi Ibrahim {a.s} ce da ya taso cikin al’ummar da suka riki wani abin bauta ba Allah ba, inda suke gudanar da bautan gumaka, taurari, wata, rana da sauransu, don haka Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin fuskantarsu ta hanyar gabatar musu da dalilai na hankali da nufin tabbatar musu da samuwar Allah Madaukaki. To a cikin shirinmu na wannan mako zamu tabo matakin da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka ne na kiran baffansa zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:- 

 

Haƙĩƙa kiran Annabi Ibrahim Khalil {a.s} kamar sauran kiran Annabawan Allah Madaukaki ne da tubulinsa shi ne kadaita Allah Madaukakin Sarki ta hanyar gabatar da dalilai na hankali da na shari’a. Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakin fara tsarkake gidan da ya taso  daga daudar kafirci da shirka ta hanyar kokarin shiryar da baffansa Azara da ya kasance daga cikin makusantar Sarki Namrudu da ya shahara a fagen wanzar da kafirci da aiwatar da zalunci a bayan kasa, inda Annabi Ibrahim {a.s} ya fuskanci baffansa cikin dabi’a ta ladabi da girmamawa, kamar yadda ya dauki matakin gargadin baffan nasa kan ya nisanci bautan Shaiɗan domin kada ya tashi a makoma daya da shi.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratu-Maryam daga aya ta 41 zuwa 45 yana fayyace mana haƙĩƙanin hikayar da cewa:-

“Kuma ka ambaci Ibrãhĩm a cikin Littafi. Haƙĩƙa shi ya kasance mai yawan gaskiyã ne kuma Annabi”.

“A lõkacin da ya ce wa babansa, Yã bãbana! mene ne ya sa kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya amfanar da kai da komai?”.

“Yã bãbana! Lalle haƙĩƙa wani abu na ilimi ya zo mini da kai bai je maka ba, sabõda haka sai ka bĩ ni in shiryar da kai hanya madaidaiciya”.

“Yã bãbana! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Haƙĩƙa Shaiɗan ya kasance mai saɓo ne ga Allah Mai rahama”.

“Yã bãbana! Lalle inã ji maka tsõron wata azãba ta shãfe ka daga Allah, sai ka kasance mataimaki ga Shaiɗan”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce dangane da matakin da ya dauka na kokarin shiryar da baffansa Azara da ya kasance makusanci ga Sarki Namrudu kuma shahararre a fagen sassasaka gumakan da ake sayarwa ga mutane, kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-  

Haƙĩƙa Azara ya kasance mutum ne masanin ilimin taurari da yake gudanar da duba ga azzalumin Sarki Namrudu, bayan haka Azara ya shahara a fagen sassaka gumaka, kuma ya kasance yana sassaka gumaka ya bai wa ‘ya’yayensa domin su sayarwa mutane, kuma Azara ya kasance baffah ne ga Annabi Ibrahim {a.s}, don haka Ibrahim yake girmama shi har yana kiransa da baba. Kamar yadda shi ma Azara ya kasance yana tsananin kaunar dan dan uwansa Ibrahim, kuma a lokacin da Annabi Ibrahim {a.s} ya girma ya kai matakin cikan hankali, Azara ya gabatar masa da gumaka kan ya je ya sayar da su ga mutane, kamar yadda yake bai wa ‘ya’yayensa gumaka suna zuwa sayarwa a gari.

Hakika Annabi Ibrahim {a.s} ya kasance yana da masaniyar cewa; Wadannan gumaka ba iyayen giji ba ne da suka cancanci bauta, iyaka dai abubuwa ne da aka sassaka kuma ake daura musu kyalle a wuyarsu ana jansu a kasa, kuma babu wani tasiri da suke da shi a fagen rayuwa, don haka a lokacin da Annabi Ibrahim {a.s} ya fice da gumakan daga gida domin sayrwa, sai ya fara tallata su da cewa; Wane ne zai sayi abin da ba zai amfanar da shi ko cutar da shi ba? Kuma Annabi Ibrahim {a.s} ya kasance yana gudanar da izgili ga gumakan da yake janye da su ta hanyar nutsar da su a cikin ruwa ko tabo yana cewa; Ku sha ruwa, shin ba kwa magana ne? Wata rana sai labarin abin da Ibrahim yake gudanarwa ga gumakan ya isa kunnen baffansa Azara, don haka Azara ya kira shi ya ja kunnensa, amma Annabi Ibrahim {a.s} bai fasa abin da ke gudanarwa ga gumakan ba. Sakamakon haka Azara ya dauki matakin kuntatawa kan Annabi Ibrahim {a.s}.

Matakin da Azara ya dauka domin ladabtar da Annabi Ibrahim {a.s} kan wofantar da gumaka shi ne; hana shi fita daga cikin gida, sai kuma Azara ya kai ga fahimtar cewa; Lalle Annabi Ibrahim {a.s} baya dauke da akidar bautar gumaka, iyaka dai yana bauta ne ga Allah Madaukaki shi kadai, kuma yana bautan ne a kan basira bisa dogaro da dalilai na hankali, inda hakan ya wurga Azara cikin dimuwa saboda babu yadda zai yi ya raba Ibrahim {a.s} da wannan akidar tashi.

Wata rana Annabi Ibrahim {a.s} ya tsaida shawarar tunkarar baffansa Azara domin kira shi zuwa ga kadaita Allah tare da gudanar da bauta a gare shi, inda Annabi Ibrahim {a.s} ya je wajen baffansa Azara cikin ladabi da furta maganganu cikin girmamawa yana ce masa: Ya babana! mene ne ya sa kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya amfanar da kai da komai?”. “Yã bãbana! Lalle haƙĩƙa wani abu na ilimi ya zo mini da kai bai je maka ba”. Ya babana kana da masaniyar cewa; wadannan gumaka tabbas ba sune suka cancanci bauta ba, iyaka dai abin bauta shi ne Allah wannan da ya halicci sammai da kassai da abin da suke cikinsu, “Sabõda haka sai ka bĩ ni in shiryar da kai hanya madaidaiciya”. “Yã bãbana! Kada ka bauta wa Shaiɗan”, domin idan har ka bauta wa gumaka, to lalle kana bautar Shaiɗan ne, saboda shi ne ke riya maka bautar gumaka domin ya nisanta ka da Allah Madaukaki, “Haƙĩƙa Shaiɗan ya kasance mai saɓo ne ga Allah Mai rahama”. “Yã bãbana! Lalle inã ji maka tsõron wata azãba ta shãfe ka daga Allah”. Hakika da irin wannan salo na hikima da ladabi gami da nuna jin kai Ibrahim {a.s} ya fuskanci baffansa Azara.

A nashi bangaren Azara ya dauki matakin fusata saboda maganar Annabi Ibrahim {a.s} yana mai cewa: “Ashe kai mai kyamatar iyayen gijina ne Ya kai Ibrahim?”. Don haka ka koma kana bautar wani abu na daban? “To babu shakka idan har baka bar abin da kake yi ba, lalle zan jefe ka” da duwatsu har mutuwarka. Sannan kuma Azara ya dauki matakin korar Ibrahim {a.s} daga wajensa, yana mai cewa; “Ka tafi can ka ba ni wuri tsawon lokaci” wato ka bace daga idona domin ba na son ganinka.

Ganin irin wannan tsaurara matakai da Azara ya dauka, sai Annabi Ibrahim {a.s} ya amince da batun kaurace masa zuwa wani lokaci, kuma ya yi masa bankwana cikin ladabi da girmamawa yana cewa: “Aminci a gare ka”, wato na barka lafiya “kuma da sannu zan nema maka gafarar Ubangijina domin kuwa ya kasance shi mai yawan bai wa ne gare ni”. “Kuma zan kaurace muku da abin da kuke bautawa koma bayan Allah, kuma in roki Ubangijina tsammanin ba zan tabe ba game da rokon Ubangijina”. Sannan Annabi Ibrahim {a.s} ya kama hanya ya fice daga wajen baffansa.        

  

Add comment


Security code
Refresh