An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:55

Hikayar Annabi Ibrahim {1}

A shirinmu na wannan mako zamu fara gabatar muku da hikayar Annabi Ibrahim Khalilullahi {a.s} ne da ya kasance daga cikin manyan Annabawan Allah mafiya girman matsayi da daukaka a bayan kasa da ake kira da Ulul-Azmi. Hakika Annabi Ibrahim Khalil {a.s} shi ne mutum na biyu daga cikin jerin manyan Annabawa guda biyar masu littattafai da aka aiko su domin shiryar da a’umma zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki, sai a biyo mu don jin abin da shirin namu ya kunsa:-

 

Hakika Annabi Ibrahim Khalil {a.s} ya fuskanci al’ummar zamaninsa da suka yi nisa a fagen gudanar da shirka ga Allah Madaukaki ta hanyar bautawa wasu halittu na daban ciki har da gumaka da suka sassaka da hannayensu, kamar yadda rayuwar rudu da zalunci ta yi ƙamari a tsakanin al’umma, inda Annabi Ibrahim {a.s} ya dauki matakan gabatar musu da ƙwararan dalilai na hankali da hujjoji na shari’a domin dawo da su kan fidirarsu ta dan Adamtaka da bin tafarkin shiriya na kadaita Allah da gudanar da bauta a gare shi shi kadai.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratul-An’am daga aya ta 75 zuwa 79 ya fayyace mana irin salon kiran da Annabi Ibrahim {a.s} ya dauka na tunkarar al’ummarsa da suka shahara a fagen gudanar da shirka ta hanyar gabatar musu dalili na hankali kamar haka:-         

“Kuma kamar haka ne Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni”.

“Sannan a lõkacin da dare ya yi duhu a kansa ya ga wani taurãro, ya ce: Wannan ne Ubangijina. Sannan a lõkacin da ya ɓace, sai ya ce: Ba na son mãsu ɓacewa”.

“Sannan a lõkacin da ya ga watã yã fito, sai ya ce: Wannan ne Ubangijina, Sannan a lõkacin da ya ɓace, sai ya ce: Lalle idan har Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa zan kasancẽ daga cikin mutãne ɓatattu”.

“Sannan a lõkacin da ya ga rãnã ta fito, sai ya ce: Wannan ne Ubangijina, wannan ne mafi girma, Sannan a lõkacin da ta fãɗi, sai ya ce: Ya mutãnena! Lalle ni na bijire wa abin da kuka kasance kuna yin shirki da shi”.

“Haƙĩƙa nĩ na fuskantar da fuskata ga wanda Ya ƙãgi halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma ni bã na cikin mushrikai”.

Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi Ibrahim {a.s} ce dangane da matakin da ya dauka na kokarin gyara gurbataccen tunanin al’ummarsa ta hanyar gabatar da dalili na hankali kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Ya zo cikin hikayar Annabi Ibrahim {a.s} cewa; Akwai wani mutum masani ilimin taurari mai suna Azara da ya kasance mai gudanar da duba ga wani azzalumin sarki mai tsananin kafirci da girman kai da ake kira Namrudu. Wata rana wannan masanin ilimin taurari Azara ya sanar da Namrudu cewa: Hakika a cikin hisabin da na gudanar na ga cewa tabbas za a haifi wani yaro da zai zo ya shafe addininka da na mutanenka ta hanyar maye gurbinsa da wani sabon addini Ya shugabana! Sai Namrud ya tambayi Azara; shin an haifi wannan yaro? Inda Azara ya amsa da cewa; Lalle har yanzu ba a kai ga haifarsa ba.

Sakamakon haka Namrudu ya ce; Lalle ya dace a dauki matakin raba tsakanin maza da mata musamman ma’aurata domin hana aukuwar wannan babbar barazana da take tunkararmu. Sannan Namrudu ya bada umurnin aiwatar da wannan shawara a duk fadin masarautarsa. Amma duk da tsaurara matakan tsaro da muzguna wa jama’a domin cika umurnin Sarki Namrudu, hakan bai hana mahaifiyar Ibrahim daukan ciki ba, kuma a lokacin da nakuda ta zo mata, sai ta samu wani kebantaccen waje nesa da idon mutane ta haife shi domin kare rayuwarsa, kuma ta dauki matakin nannade jaririn da ta haifa tare da adana shi a waje mai aminci sannan ta dawo gida, kuma tana yawaita zuwa duba jaririnta tare da shayar da shi har ya girma, kuma girman Ibrahim ya kasance cikin hanzari na ban mamaki har ya kai matakin matashi. A fege guda kuma jami’an tsaro suna ci gaba da tsaurara dokar Namrudu domin hana haihuwa a tsakanin jama’a, kuma koda an samu haihuwa a tsakanin mace da na miji matukar namiji aka haifa, to za a kashe yaron. Hakika Allah cikin iko da buwayarsa haka Ibrahima ya girma cikin aminci tare da kubuta daga zaluncin mai zubar da jinin kananan yara.

Wata rana Ibrahim {a.s} ya fito daga maboyarsa, kuma a wannan lokaci ya kai shekaru goma sha uku a duniya, sai ya yi dubi zuwa ga tarin halittu da ke kewaye da shi, inda ya ga girman ikon Ubangiji Allah Madaukaki, kamar yadda Ibrahim {a.s} ya zurfafa tunani a halittun Sammai da kassai tare da tabbatar da ayoyin Allah a cikinsu, kuma babu wani abin da zai gani har sai ya kara masa yakini da tabbaci kan samuwar Allah Madaukaki da buwayarsa. Don haka a lokacin da ya shiga cikin mutane sai ya ga suna bautar wasu abubuwa maimakon Allah Madaukaki, don haka Ibrahim {a.s} ya fada cikin mamaki da takaicin abin da ya gani daga mutane, sakamakon haka ya kuduri aniyar kalubalantar wannan mummunar dabi’a ta hanyar gabatar musu da dalili na hankali cikin hikima.

Bayan da rana ta fadi, dare ya rufa, taurari suka fito, sai Ibrahim {a.s} ya ga wasu jama’a suna bautar taurari tare da rusuna musu a matsayin kankantar da kai gare su, sai ya shiga cikinsu kuma ya dubi sama ya ga wani tauraro yana haske, sai ya yi da’awa da harshen baki cewa; Wannan shi ne Ubangijina, kuma ya kasance a cikinsu yana jiran lokacin mai da martani. Don haka a lokacin da wannan tauraro ya ɓace daga idon masu bautar taurari, sai Ibrahim {a.s} ya furta cewa; Lalle ba na bukatar Ubangiji mai ɓacewa, don haka hakika taurari ba su cancanci bauta ba.

Har ila yau Ibrahim {a.s} ya gamu da wasu taron mutane da su kuma suna rusunawa wata ne a matsayin abin bautarsu, don haka a lokacin da watan ya fito yana haske, sai ya shiga cikin taronsu ya sake da’awar baki cewa; Ai wannan shi ne Ubangina!, kuma ya zauna ya yi hakuri har lokacin da watan ya ɓace, sai Ibrahim {a.s} ya fuskanci masu bautar watan ya ce musu; Lalle idan har Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa zan kasancẽ daga cikin mutãne ɓatattu”. Sannan Ibrahim {a.s} ya zauna har zuwa asubahi kuma rana ta fito, idan ya shiga cikin taron jama’ar da suke bautar rana, sai ya ce; A’a wannan tafi girma zai yiyu ita ce Ubangijin! Kuma ya yi hakuri kamar yadda ya saba har zuwa yammaci lokacin da rana ke fãɗuwa, ranar tana ɓacewa daga idon mutane, sai Ibrahim {a.s} ya fuskanci wadannan jama’a ya ce; Lalleni kamna bijire wa abin da kuka kasance kuna yin shirki da shi. Hakika tauraro da wata da kuma rana ba sune abin bauta ba, don haka “Haƙĩƙa nĩ na fuskantar da fuskata ga wanda Ya ƙãgi halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma ni bã na cikin mushrikai”.

   

Add comment


Security code
Refresh