An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:51

Hikayar Annabi Lũɗu {4}

A makon da ya gabata mun fara ambaton wasu daga cikin ‘yan darussan da zamu iya dauka ne a cikin ‘yar takaitacciyar hikayar Annabi Lũɗu {a.s} da mutanensa da suka yi kaurin suna a fagen gudanar da muggan ayyuka da barna a bayan kasa, sai lokaci ya yi mana halinsa don haka a yau zamu karkare shirin namu, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

 

Dangane da fadin Allah Madukaki cewa: “Yanzu kwa rika zuwa ga maza, kuma kuna tsare hanya” a cikin wannan aya ta cikin Suratu-Ankabuti zamu iya fahimtar cewa; Mutanen Annabi  Lũɗu {a.s} mutane ne da suke tsare hanya domin gudanar da fashi da makami. Sannan ana fassara ayar da cewa; Mutanen Lũɗu suna tsare hanyar matafiya ce domin cutar da su ta hanyar daukan matakin wuce gona da iri kansu wato yi musu fyade ta hanyar Lũwaɗi da karfin tsiya.

Haka nan an ruwaito cewa; Mutanen Lũɗu sun kasance suna yin lalata da matafiya da suke sauka a gidajensu a matsayin baki. A wani kaulin kuma mutanen Lũɗu mutane ne da suak kasance suna jifan matafiya da duwatsu na daga bushesshen yumbu, kuma duk wanda jifarsa ta samu matafiyi, to shi ne zai dauki matakin wuce gona da iri kan wannan matafiyin, sannan kuma ya karbe kudaden matafiyin ta hanyar alkali da ke yanke hukunci kan duk matafin da aka kawo shi gabansa kan ya biya tarar dirhami ukuga mutumin da ya kwana a gidansa. Kamar haka ne alkur’ani mai girma ke cewa: “Kuma kuna zuwa da abin kyama a cikin gidajenku”.

Har ila yau wata ruwayar tana bayyana cewa: Mutanen Lũɗu sun kasance suna gudanar da Lũwaɗi a tsakaninsu a wajajen taruwansu a fili suna kallon junansu ba tare da jin kunya ba.

Hakika yana daga cikin dabi’a ta mutane mabarnata masu son gudanar da rayuwar sharholiya; yin gaggawa zuwa ga afkawa cikin halakar zunubi da sabonUbangijin talikai. Sakamakon haka mutanen Annabi Lũɗu suka kasance suna gaggawar zuwa ga bakinsa kamar yadda alkur’ani mai girma ke bayyana cewa: “Kuma mutãnensa suka zo masa sunã gaggãwa zuwa gare shi”.

Hakika aikata muggan laifuka a tsakaninal’umma lamari ne da ke zama shimfidar bullar wasu ayyukan laifi na daban a cikin wannan al’ummar. Kamar haka ne alkur’ani mai girma ke bayyana cewa:“kuma da ma can sun kasance sunã aikatã mũnãnan ayyuka”.

Hakika tsawatarwa kan laifi da hana mutane aikata shi lamari ne da baya ciki har sai an samar da wani abin da zai maye gurbinsa ta halartacciyar hanya. Kamar haka ne zamu ga cewa a lokacin da Annabi Lũɗu {a.s} ya hana mutanensa gudanar da mummunar dabi’ar Lũwaɗi  yake ce musu: “Yã ku mutãnẽna waɗannan 'yã'yãna mata sũne mafiya tsarki a gare ku {a kan maza}”.

Dangane da fadin Allah da ke cewa: “Kuma a lõkacin da umurnin Mu ya zo, sai Muka sanya samanta ya koma ƙasanta {wato alkaryar}, kuma Muka yi mata ruwan duwãtsu daga soyayyen yunɓu wasu bayan wasu”. Hakika mutanenAnnabi Lũɗu {a.s} sun bijirewa tafarkin gaskiya tare da zaluntar kansu, kuma suka yi wasa da makomar al’ummarsu gami wofantar da hankulansu da kuma dabi’unsu na dan- Adamtaka, sannan suka yi izgili ga Annabinsu kuma a duk lokacin da ya fadakar da su tare da yin gargadi a gare su, sai su kaurace masa tare da yin suka a gare shi. Sannan girman kai da rashin kunyarsu ya kai ga matakin da suka nemi wuce gona da iri kan bakinsa tare da kokarin keta musu hurumi. Tabbas wadannan mutane sun juyar da akalar duk wata kyakkyawar dabi’a zuwa ga akasinta, sakamakon haka ya zame wajibi su fuskanci azabar kifar da garinsu ta hanyar juyar da samansa zuwa kasansa, kamar yadda suka cancanci ruwan duwatsu daga sama da zai halakar da su baki daya. Tabbas an shafe mutanen garin Sadum daga kan bayan kasa tare da mai da garinsu a matsayin sahara kuma makabarta ga lalatattun mutane mabarnata domin hakan ya zame darasi kuma aya mai girma ga duk mai hankali.

Dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: “Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai”. Shin irin wannan azaba da ta sauka a kan mutanen Annabi Lũɗu, azaba ce da ta kebanta da su kawai? A’a azaba ce da ta cancanci duk wata al’umma da ta zalunci kanta ta hanyar kaucewa tafarki madaidaici, iyaka dai Allah cikin hikima da adalcinsa yana azabar da kowace al’umma ce daidai da laifin mutanenta.

A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu ne daga cikin taskar iyalan gidan manzon Allah tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta Annabi Lũɗu {a.s} kamar haka:-

Yazo cikin tafsirin Qummi daga Abu-Abdullahi {a.s} dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: “kuma Muka yi mata ruwan duwãtsu daga soyayyen yunɓu wasu bayan wasu”. Ya ce: “Babu wani mutum da zai bar duniya matukar yana halarta aiki irin na mutanen Lũɗu wato yana gudanar da Lũwaɗi sai Allah ya je fe shi da dutse daga dutsen da aka je fe su domin dutsen ya halakar da shi, amma mutane ba su ganin abin da ke faruwa”.

Har ila yau ya zo cikin littafin Kafi daga Abu-Abdullahi Sadiq {a.s} cewa: “Duk wanda ya kasance a kan hanyar lũwaɗi, to ba zai mutu ba har sai Allah ya je fe shi da dutse da zai halakar da shi, kuma babu wani da zai gani”. A cikin wadannan ruwayoyi biyu za a iya fahimtar ma’anar fadin Allah cewa: “Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai”. Wato ba gargadi ba ne da ya takaita ga kuraishãwa kawai wato gargadi ne ga dukkanin al’ummun da zasu a baya, kamar yadda za a iya fahimtar cewa; azabar da take sauka kan ‘yan Lũwaɗi ba azaba ce ta zahiri da kowa ke iya gani ba.

Add comment


Security code
Refresh