An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:50

Hikayar Annabi Lũɗu {3}

A karshen dan takaitacciyar hikayar da muka gabatar muku ta Annabi Lũɗu {a.s} da mutanensa da suka yi kaurin suna a fagen gudanar da muggan ayyuka da barna a bayan kasa, zamu ambaci wani abu daga cikin irindarussan da zamu iya dauka a hikayar, sai a biyo mu don jin abin da shirinyakunsa:-

 

Hakika Annabi Lũɗu {a.s} kamar sauran Annabawan Allah Madaukaki ya dauki matakin fuskantar mutane masu tsananin taurin kai da bijire wa gaskiya, inda ya bude kafar gudanar da muhawara da su, tare da fayyace musu kwararan hujjoji da dalilai da nufin dawo da sukan fidirarsu da dabi’arsu ta dan–Adamtaka, amma kasancewar su mutane ne da suka yi kaurin suna a fagen aikata muggan laifuka, hakan ya kara nisantar da zukatansu ga kan tafarkin gaskiya, tare da   mummunar tasiri wajen kara gurbata musu tunani da mai da su masu kyakyashasshen zukata, don haka suka dauki matakin bijire wa duk wani kiran gaskiya da je musu tare da shirya makarkashiyar Koran Annabi Lũɗu {a.s} daga garinsu.

Haka nan kasancewar mutanen Annabi Lũɗu {a.s} mutane ne da suke rayuwa cikin wadata, hakan ya kara yaudarar da su wajen gudanar da rayuwar sharholiya da walwala sama da kaidin rayuwar dan Adamtaka, sakamakon haka suka fadacikin rayuwar rudu da bata ta hanyar biyewa son zuciya har suka zame tamkar dabbobi, kai fiye da dabbobi. Kamar haka ne alkur’ani mai girma kefayyace halin dan Adama da ya jinginar da hankalinsa gefe guda kuma ya biyewa son rai domin gamsar da sha’awarsa ta rayuwa da cewa;“Sunã da zukãta wadanda ba sa fahimta da su, kuma sunã da idãnu wadanda bã sa gani da su, kuma sunã da kunnuwa wadanda basa ji da su; waɗancan kamar dabbobi suke, kai sun fi su ma ɓacẽwa; Waɗancansũ ne gafalallu”.

Dangane da mummunar dabi’ar mutanen Annabi Lũɗu {a.s} ta gudanar da Lũwaɗi kuwa. Hakika Annabi Lũɗu {a.s} ya dauki matakin kalubalantarsu da cewa; Shin zaku kasance kuna aikata mummunar aiki da babu wasu mutane da suka rigayeku aikatawa a tsawon tarihi? Kamar yadda alkur’ani mai girma ke bayyana cewa: “Kuma {ku tuna} Lũɗu lõkacin da ya cewa mutãnensa: "Shin zaku rika mummunan aiki, wanda bãbu wani mahaluki da ya gabãceku da shi daga halittu?”. Hakika baya ga matakin da Annabi Lũɗu {a.s} ya dauka na fadakar da mutanensa irin girman laifi da munin abin da suke aikatawa, ya kuma fayyace musu wani babban hatsarin da suka wurga kansu ciki na kirkirar mummunar dabi’a da zata zame dalilin halakar mutane da zasu zo bayansu a kusa ko a nesa.

Har ila yau Annabi Lũɗu {a.s} ya ci gaba da fayyace wa mutanensa tsananin munin laifin da suke aikata wa na Lũwaɗi da cewa; Shimfida barna ce a bayan kasa. Kamar yadda alkur’ani mai girma ke bayyana cewa: “Lalle ne haƙĩƙa kunã jẽ wa maza don sha'awa maimakon mata; Kũ dai mutãne ne maɓarnata”.

Hakika Annabi Lũɗu {a.s} ya dauki matakin fayyace wa mutanensa cewa; Wace gurbatar tunani ce har zata kai mutum ga matakin barin hanyar samar da zuriya da haihuwar ‘ya’ya a tsakanin jinsin halittu! Hakika Ubangijin talikai ya shimfida tsarin biyar sha’awar jinsi a tsakanin halittunsa, tsarin da har dabbobi a kansa suke gudanar da rayuwarsu! Tabbas mummunar dabi’ar Lũwaɗi wato biyar sha’awar jinsi tsakanin jinsin halitta guda, aiki ne da ya sabawa fidira da dabi’ar rayuwar bil-Adama, kuma rusa tsarin dabi’ar halittan jiki da na ruhi ne gadan Adam, sannan mummunar dabi’a ce da duk wani mai cikan hankali ke kyamata.

Hakika dalilai na hankali da hujjoji na shari’a da Annabi Lũɗu {a.s} ya yi amfani da su wajen fuskantar mutanensa sun yi gagarumin tasiri a kwakwalansu tare da farfado musu da ruhin dan Adamtaka lamarin da ya sanya shugabanni bata masu bakin fada aji daukan matakin kalubalantarsa ta hanyar gudanar da izgili tare da ingiza mutanensu a kan Annabi Lũɗu {a.s} domin yi masa bore tare da kulla makarkashiyar korarsa daga garinsu. Kamar yadda alkur’ani mai girma ke fayyace mana cewa: “Kuma bãbu abin da ya kasance a matsayin amsa ga mutãnensa, sai kawai cewa; “Ku fitar da su daga garinku, haƙĩƙa sũ mutãne ne da suke nuna sumã su tsarki ne”. Har ila yau a cikin wannan ayar zamu fahimci cewa; Babban laifin Annabi Lũɗu {a.s} da har zai sanya a kore shi daga kasa shi ne; Shi da iyalansa da wadanda suka   bada gaskiya mutane ne masu da’awar tsarki, lamarin da ke fayyace cewa su kansu kafirai suna da masaniyar cewa; luwadi dabi’a ce ta rashin tsarki, don haka suke kokarin zargin Annabi Ludu {a.s} da mabiyansa da cewa suma a zahiri ne suke gwada kyamatarsu ga mummunar dabi’ar ta luwadi.

Haka nan yana daga cikin dabi’ar mabarnata masu son gudanar da rayuwar sharholiya a bayan kasa tun a tsawon tarihi; daukar matakin korar mutanen da suke kira zuwa ga wanzar da adalci da gudanar da tsarkakekkiyar rayuwa a tsakanin al’umma, saboda da suna ganin mutanen kirki a matsayin masu takuri da suke neman takaita hakkin rayuwar sharholiya da walwala, kuma suna kallo duk wani kira zuwa ga tsarin tsarkakekkiyar rayuwa ta gudanar da aure a tsakanin jinsin mace da namiji a matsayin wani rashin wayewa da fahimtar rayuwar duniya. Kamar haka ne a wannan zamani da muke ciki, muke ganin kasashen da suke da’awar wayewa da ci gaba a fuskar rayuwar duniya; suke fada da duk wata kasa ko mutane da suke adawa da mummunar dabi’ar Lũwaɗi.

Sannan yana daga cikin mummunar dabi’ar mabarnata musamman masu mulki daga cikinsu kokarin rusa duk wani kira zuwa ga tafarkin Allah ta hanyar zargin masu addini da cewa; Suna gudanar da ayyukansu ne domin riya. Kamar haka ne mutanen Annabi Lũɗu {a.s} suka zarge shi da mutanen da suka bada gaskiya da cewa; Su mutane ne masu da’awar tsarki da gudanar da riya.

Add comment


Security code
Refresh