An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 18 November 2014 14:48

Hikayar Annabi Lũɗu {2}

A shirinmu da ya gabata mun fara gabatar muku da hikayar Annabi Lũɗu {a.s} ce tare da ambaton irin halin kuncin da ya shiga sakamakon bakin da suka zo masa saboda tsoron mummunar matsala cin zarafi da zasu fuskanta daga lalatattun mutanensa da suke fice daga karkashin tsarin rayuwa ta dan Adamtaka suka rungumi muggan dabi’u da gudanar da ayyukan alfasha a bayan kasa. To a wannan mako zamu ambaci irin mummunar azabar da ta sauka a kan mutanen Annabi Lũɗu ce sakamakon bijirewa shiriyar da ta je musu. Sai a biyo mu don jin abin da shirin namu ya kunsa:-

 

Hakika Annabi Lũɗu {a.s} yana cikin halin tsaka mai wuya da tsananin zullumin kan abin zai faru a cikin dare a lokacin da lalatattun mutanensa zasu dauki matakin farma gidansa domin neman aikata lalata da bakinsa, don haka a cikin zuciyarsa ke cewa; Lalle wannan rana ce mawuyaciya. Tabbas duk wannan mummunan kangi da Annabi Lũɗu {a.s} ya samu kansa a ciki, amma hakan bai hana shi shirya gudanar da liyafa ga bakin nasa ba sakamakon tsananin karamcinsa. Sai dai wata babbar matsala ta daban ita ce; a daidai lokacin da Annabi Lũɗu {a.s} yake shirin tunkarar makiya da zasu zo masa daga waje, sai kuma ga wata makiyar a cikin gidansa, domin matarsa kafira ce kuma ta kasance tana taimakon mutane azzalumai, don haka a lokacin da Annabi Lũɗu {a.s} ke shirya liyafa ga bakinsa, sai matarsa ta haura kan saman soro tana tafa hannunta alamar cewa akwai bakin maza a cikin gidanta, sannan ta hura wuta hayaki yana tashi domin sanar da mutanen garin Sadum cewa a halin yanzu zasu iya kawo farmaki gidan domin cimma burinsu, inda mutane Annabi Lũɗu suka tunkari gidansa har suna turarreniya a tsakaninsu.

Hakika Annabi Lũɗu {a.s} ya dauki matakin tsare mutanensa ta hanyar hana su shiga cikin gidansa yana mai kara jaddada yin kira gare su kan tsoron Allah Madaukaki, tare da kara fadakar da su hanyar biyan bukata ta jinsi ta tsarkakekkiyar hanyar aure tsakanin namiji da mace, yana mai fayyace musu cewa: “Yã ku mutãnẽna waɗannan 'yã'yãna mata sũne mafiya tsarki a gare ku, sai ku ji tsoron Allah, kuma kada ku kunyatã ni a gaban bãƙĩna”. Amma ina mutanen Annabi Lũɗu sun riga sun yi nisa cikin kafirci tare da bijirewa umurnin Allah Madaukaki, don haka suka doge a kan bakar aniyarsu ta neman kutsawa cikin gidansa ko ta halin kaka domin gudanar da mummunar dabi’arsu ta Lũwaɗi, sakamakon haka bakin Annabi Lũɗu {a.s} suka dauki matakin fayyace masa hakikaninsu da cewa sun Mala’iku ne daga Ubangijinsa kuma sun zo ne su halakar da lalatun mutanen Sadum halakakku.

Alkur’ani mai girma a cikin Suratu Hudu daga aya ta 81 zuwa 83 yana fayyace mana hakikanin hikayar da cewa:-

“{Bakin} Suka ce: Yã Lũɗu, hakika mũ manzannin Ubangijinka ne; Bã zã su iso gare ka ba. Sai ka fice ka yi tafiyarka da iyãlinka a cikin wani yanki na dare, kuma kada wani daga cikinku ya waiwaya, sai mãtarka kawai. Lalle ita kam abin da ya same su zai same ta. Hakika lõkacin da aka dibar musu asubahi ne kawai, shin lõkacin asubahi bã kusa yake ba?”.

“Kuma a lõkacin da umurninMu ya zo, sai Muka sanya samanta ya koma ƙasanta {wato alkaryar}, kuma Muka yi mata ruwan duwãtsu daga soyayyen yunɓu wasu bayan wasu”.

“{Duwãtsu ne} da suke dauke da alama daga Ubangijinka. Kuma ita ba ta zama mai nisa ba daga azzãlumai”. 

Yanzu kuma zamu ambaci ci gaban hikayar ta Annabi Lũɗu {a.s} ce kamar yadda ta zo cikin littattafan tarihi kamar haka:-

Bayan da tura ta kai bango kuma Annabi Lũɗu {a.s} ya furta duk irin dalilai da hujjoji da zai gamsar da mutanensa kan su janye daga kan mummunar aniyarsu amma suka ki saurarensa, hakika ya kai ga matakin fitar da ran kan shiriyar wadannan lalatattun al’umma, inda ya koma yana kiran daidaikunsu da cewa; Shin a cikinku babu sauran mai hankali ne da zai fifita hankalinsa a kan son ransa? Amma sai mutanen Sadum suka dauki matakin mayar masa da martani da cewa: Hakika Ya Lũɗu kai ka san abin da muke so na biyan bukatunmu na jinsi da bakinka maza. Bayan da ya zame babu wata mafita ga Annabi Lũɗu {a.s}, sai taimako ya zo gare shi, inda bakinsa suka mike suka bayyana masa cewa; Ya Lũɗu mu fa Mala’iku ne, don haka kada ka yi bakin ciki, kuma babu abin da zai same ka na cutarwa daga gare su. Sannan Mala’ika Jibrilu ya yi nuni da hannunsa ga mutanenen Lũɗu, sai kuwa suka makance, sannan ya juyo zuwa ga Annabi Lũɗu {a.s} ya umurce shi da ya tattara iyalansa su fice a daga wannan garin a cikin dare, kuma kada su kuskura su juyo a lokacin da suke fita saboda zasu ji wata kara mai razanarwa da take girgiza duwatse domin kada abin da zai faru a kan mutanen garin Sadum ya shafe su.

A gefe guda kuma Mala’ikun nan sun sanar da Annabi Lũɗu {a.s} cewa matarsa tana daga cikin wadanda za a halakar saboda kasancewarta kafira da ba ta yi imani da Allah ba, kuma ta kasance daga cikin masu ha’intar Lũɗu wajen gayyato masa lalatattun mutane zuwa gidansa a lokacin da ya yi baki. Don haka a lokacin da ya kama hanyar ficewa daga garin zata waiwaya domin ganin irin azabar da take sauka a kan  mutanen Sadum sai azabar ya shafe ta.

Bayan nan sai Annabi Lũɗu {a.s} ke tambayar Mala’ikun nan shin yaushe ne azabar zata sauko? Shin a halin yanzu ne? Don haka Mala’ikun suka amsa masa da cewa; Azabar zata sauka ce a lokacin asubahi, shin a halin yanzu lokacin asubahi bai karato ba? Sakamakon haka Annabi Lũɗu {a.s} ya tattara iyalansa ya kama hanyar ficewa da su a cikin wannan daren kusa lokacin asubahi. Hakika bayan da tawagar Annabi Lũɗu {a.s} suka yi nisa da garin Sadum, sai azaba ta fara sauka a garin, inda Mala’ikun nan suka kifar da garin wato samansa ya koma kasa, kasa ta koma sama, kuma a lokacin da ake juyar da garin sai Allah ya saukar musu da ruwan duwatsu daga wutar Jahima, wanda bushesshen yunbu ne mai karfi daya na bin daya, kuma kowane dutse yana dauke da sunan mutumin da zai halakar, haka azabar ta ci gaba da sauka har ta kammala halakar da dukkanin mutanen Lũɗu baki daya.

Hakika a lokacin da azabar Allah ke sauka kan mutanen garin na Sadum Annabi Lũɗu da tawagar iyalansa sun ji kara mai tsoratarwa, don haka Annabi Lũɗu {a.s} ke ci gaba da fadakar da su cewa; kada su kuskura su waiwaya, amma sai matarsa ta juya ta kalli wajen da karar ke fitowa, don haka ta halaka, inda jikinta ya fatattake ta hanyar gutsuttsurewa tamkar ginshiki da ke tarwatsewa a kasa. Wannan ita ce irin azabar da aka saukar kan mutanen Lũɗu, inda aka kifar da kasarsu ta hanyar nutsar da su a cikin kasa tare da shafe garin Sadum daga kan bayan kasa.

Shakka babu an shafe mutanen Lũɗu da garinsu daga kan doron kasa, kuma aka shafe su daga cikin shafin rayuwa tare da kawo karshen muggan laifukansu da barnarsu a bayan kasa. Bayan nan Annabi Lũɗu {a.s} ya ziyarci Annabi Ibrahim Khalilul Allah {a.s} kuma ya bayyana masa kissar mutanensa da irin tsananin laifukan da suka aikata har Allah ya halakar da su… Hakika Annabi Annabi Ibrahim {a.s} ya kasance yana da masaniya kan azabar da zata sauka kan mutanen Lũɗu saboda kafin Mala’ikun da Allah ya aiko su zuwa ga Annabi Lũɗu sun ziyarce shi tare da sanar da shi aikin da ke gabansu. Bayan nan Annabi Lũɗu {a.s} ya sake bude wani sabon shafin rayuwa tare da ci gaba da kiran mutane zuwa ga tafarkin Allah Madaukaki. 

 

 

  

Add comment


Security code
Refresh