An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 December 2015 03:14

Sojojin Najeriya Sun Kashe Daruruwan Mabiya Mazhabar Shi'a

Sojojin Najeriya Sun Kashe Daruruwan Mabiya Mazhabar Shi'a
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka, shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin lamurra da suka wakana a cikin kasashen Afirka, a yau shirin zai yi dubi ne kan abin da ya faru a tarayyar Najeriya a cikin wannan mako, dangane da kai harin da sojoji suka yi kan gidan Sheikh Ibrahim Zakzaki jagoran Harakar muslunci a Najeriya a garin Zaria, da fatan za a kasanc tare da mu a cikin shirin.

 

…………………………..

A ranar Asabar 12 ga Disamba 2015,  jami’an sojojin Najeriya suka kaddamar da farmaki kan cibiyar Husainiyyat Bakiyyatullah ta ‘yan uwa musulmi karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaki a garin Zaria, tare da kashe wau daga cikin mabiya Sheikh Zakzaki a wurin, bisa hujjar da sojojin suka bayar na cewa ‘yan uwa musulmi hana bababn hafsan hafsososhin sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Burutai wucewa ta titin da ke kusa da Husainiyya, har ma da zargin cewa ‘yan uwa musulmin sun yi shirin kashe shi  janar Burutai. Bayan faruwar lamarin a yammacin ranar Asabar ba da jimawa ba mun ji ta bakin mukaddashin kakakin rundunar sojin Najeriya kan me za su ce dangane da lamarin, ga abin da ya sheda wa sashen Hausa cewa sun dauki matakin da suka dauka ne domin kare rayuwar shugaban sojojin, kuma za su ci gaba da daukarv wasu matakan na daban.

………………………….

To bayan jin ta bakin kakakin sojin Najeriya a lokacin da lamain yake faruwa a yammacin ranar Asabar, a daya bangaren kuma mun ji ta bakin jagoran ‘yan uwa musulmin Sheikh Ibrahim Zakzaki kan lamarin, inda shi kuma ya karyata abin da sojojin suka fada, kan cewa an yi yunkurin kashe Burutai, tare da bayyana cewa wannan wani lamari wanda dama an shirya shi domin afkawa kan mabiya harkar Musulunci, domin kuwa hujjojin da sojojin suke bayarwa kan cewa an tare musu hanya, ba zai taba zama dalili ga abin da suka yi ba.

……………………………..

To a bangare guda kuma a daidai lokacin da sojoji suka kashe wasu daga cikin mabiya Sheikh Zakzaki a gaban Husainiyya a ranar ta Asabar, sun kuma killace Husainiyar baki daya, tare da hana shiga cikinta, da kuma hana wadanda suke ciki fitowa, kafin daga bisani su afka kansu tare da kashe da kuma rusa wurin. Mabiya Sheikh Zakzaki a birane daban-daban na arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a a cikin daren na Asabar domin nuna rashin amincewa da abin da yake faruwa a Zaria a lokacin.

……………………………………..

A cikin daren ranar ta Asabar sojojin sun kaddamar da hari kan a kan gidan sheikh Ibrahim Zakzaky, inda suka kashe dukkanin mutanen da suka samu a wajen gidan, tare da kona da kuma rushe gidan, inda suka kashe adadi mai yawa na mabiyansa.

…………………………

To yanzu haka dai rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa tun bayan faruwar wannan lamari babu wani bayani kan makomar Sheikh Ibrahim Zakzaki, tun bayan da aka nuna hotunansa a cikin jinni bayan harbinsa da jami’an soji suka yi da harsasan bindiga a cikin gidansa a ranar Litinin, inda sojojin suka fitar da shi tare da mai dakinsa wadda ita suka harbe ta, tare da kashe yaransa maza guda uku ta hanyar harbe su da bindiga a gabansa, kamar yadda kuma suka harbe ‘yar uwarsa Hajiya Binta Yakub, wadda ita ta rasu a gabansa. Har yanzu dai babu wanda ya san abin da She8ikh Zakzaky yake ciki in banfda wadanda suke tsare da shi, domin kuwa sun hana kowa ganinsa.

………………………………….

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani jigon, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Add comment


Security code
Refresh