An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 26 November 2015 12:39

Ziyarar Shugaba Buhari Na Najeriya A Tehran

Ziyarar Shugaba Buhari Na Najeriya A Tehran
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri an Afirka a mako, shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka, ko kuma wasu batutuwa da suke da alaka da kasashen na Afirka, inda a yau da yardar Allah shirin zai mayar da hankali ne kan taron da aka gudanar a kasar Iran na shugabannin kasashen kungiyar GECF masu arzikin iskar gas da suke fitar da shi, wanda kuma Najeriya tana daga cikin kasshen da suka halarta. Da fatan za a kasance tare da mu. ………………….. Taron na kasashe masu arzikin iskar gas dai ya gudana ne a birnin Tehran na kasar Iran a ranar Litinin da ta gabata, inda shugaba Buhari na tarayyar Najeriya ya kasance daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabaia  wurin, inda ya bayyana cewa Najeriya a shirye take a kowane lokaci domin aiki tare domin samun ci gaba a bangaren fitar da iskar gas a duniya, kamar yadda kuma ya ce a shirye suke su yi aiki tare da sauran kasashen duniya a wannan fuska, da kuma batun saka hannayen jari na kamfanonin kasashen ketare a bangaren fitar da iskar gas a Najeriya. Bayan haka kuma shugaba Buhari ya gana da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei, inda Ayatollah Khamenei ya sheda masa cewa, zaben Muhammad Buhari lamari ne mai matukar muhimmanci a matsayin shugaban kasa mai muhimmanci irin Najeriya, ya ce ko shakka babu alaka za ta ci gaba da kara kyautata a tsakanin Iran da Najeriya. A nasa bangaren shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana gamsuwarsa matuka dangane da yadda ganawarsu ta kasance, tare da yin fatan ci gaba da kara bunkasa alaka a tsakanin kasashen Iran da Najeriya a dukkanin bangarori. ……………………..

 

A jiya Talata ce shugaba Muhammad Buhari ya gana da ‘yan Najeriya mazauna kasar Iran, da suka hada da daliban jami’a, ma’aikatan ofishin jakancin Najeriya a Iran da kuma ma’aikatan sashen hausa na muryar jamhuriyar muslunci ta Iran da sauran ‘yan Najeriya da suke gudanar da harkokinsu a Iran, mun samu zantawa da shi a wurin inda mu ka ji ta bakinsa dangane da taron da ya halarta a nan Iran, inda ya yi mana bayani dalla-dalla kan manufar taron, da kuma ta hanyoyin da hakan zai amfanar da Najeriya da ma sauran kasashe mambobi na kungiyar kasashe masu fitar da isakar gas, kamar yadda kuma ya yi karin haske kan muhimmancin alaka a tsakanin kasashen Najeriya da Iran, ta fuskar tatatlin arziki da cikayya da sauran batutuwa da suka shafi ilimin kimiyya.

…………………………….

 

To a daya angaren kuma mun ji ta bakin wasu ‘yan Naeriya mazauna kasar Iran kan yadda suke kallon wannan ziyara ta shugaba Buhari, da kuma irin abubuwan da suke sheda masa a yayin ganawar tasu.

………………………………………………

 

Add comment


Security code
Refresh