An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 08 November 2015 03:12

Taron India Da Kasashen Afirka A New Delhi

Taron India Da Kasashen Afirka A New Delhi
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi dubi a cikin wasu muhimman lamurra da suka wakana a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a yau ma kamar kullum shirin zai duba wasu daga cikin irin wadannan batutuwa, wasu daga cikin abubuwan da shirin zai dubu kuwa sun hada da taron koli tsakanin India da kuma kasashen nahiyar Afirka, sai kuma batun amincewa da sunayen ministoci a majalisar dattijan Najeriya tare da sake mikawa shugaba Buhari su, da kuma gangami da ‘yan adawa suka gudanar a birnin yamai na jamhuriyar Nijar, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za  akasance tare da mu a cikin shirin. …………………………..

 

To bari mu fara da batun taron hadin gwiwa da aka gudanar tsakanin kasashen India, da kuma kasashen nahiyar Afirka, inda shugabannin kasashe 40 na Afirka suka halarci zaman taron a birnin New Delhi na kasar India, gami da kuma wakilai na sauran kasashen.

Wanann shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan taro na koli tsakanin bangarorin na India da kuma kasashen nahiyar Afirka, tun bayan da aka kafa wannan hadaka tsakanin bangarorin biyu a ckin shekara ta 2008.

Babbar manufar taron dai ita ce samar da wani yanayi na alaka mai karfi tsakanin India daya daga cikin kasashen duniya mai samun ci gaba ta fuskar ilimi da bunkasar tatatlin arziki da masana’antu da kuma yawan jama’a, da kuma kasashen nahiyar Afirka, wadanda kasar ta India take amfana da su a bangarori daban-daban, da hakan ya hada ma’adanai da kuma makamashi.

 

Kasar India tana son yin amfani da wannan damar ce wajen shiga da karfita a nahiyar domin samun wuri kamar yadda kasar China ta yi a lokutan baya a cikin kasashen nahiyar.

Dukkanin bangarorin da suka halarci zaman taron dai kama daga bangaren mahukuntan kasar ta India da kuma shugabannin kasashen nahiyar Afirka, dukkansu sun nuna gamsuwa da yadda taron ya gudana da kuma abubuwan da aka cimmawa.

…………………………

To daga batun taron India kuma bari mu nufi tarayyar Najerya, inda majalisar dattijan kasar ta amince da dukkanin sunayen da ta tantance tare da sake mayar da su ga shugaba Buhari domin nada su a matsayin ministoci.

An ta kai ruwa rana tsakanin ‘yan majalisar na jam’iyyar APC da kuma PDP dangane da wasu ‘yan majalisar a lokacin amincewa da su da su, duk kuwa da cewa an tantance su, musaman ma tsohon gwamnan jahar Rrivers Rotimi Amaechi, inda bangaren jam’iyyar adawa ta PDP suka fice, yayin da sauran ‘yan jam’iyyar APC mai rinjaye suka ci gaba da aikin, kuma suka amince da sauran ministocin.

…………………………………………….

To daga tarayyar Najerya kuma bari mu nufi Jamhuriyar Nijar, inda a ranar Lahadi da ta gabata ce ‘yan adawa suka gudanar da wani babban gangami a birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijar, domin nuna rashin amincewarsu a kan abin da suka kira yunkurin yin magudi da suka ce jam’iyya mai mulki da kawayenta na shirin yi a zabukan shekara ta 2016 da za a gudana a kasar.

………………………………………………………………………

Shi Dauda Tankama jigo a cikin kawancen jam’iyyun adawa na FPR ya bayyana ra’ayinsa dangane da wannan gangami, tare da jadda cewa ‘yan adawa suna hakkin su gudanar da dukkanin abin da doka ta ba su dama, da hakan ya hada da tsayawa takara ta dukkanin mukamai a karkashin inuwar jam’iyyun da suka tsayar da su.

…………………………………

A cikin wannan mako ne wasu wasu ‘yan ta’adda da ake sa ran ‘yan Boko Haram ne suka kai wani hari a garin Ala da ke cikin jahar Diffa, inda suka kashe mutane fiye da 10, lamarin da ya saka al’ummar wannan yanki cikin zaman zullumi, duk kuwa da cewa mahukunta sun ce sun tura jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya faru, domin tabbatar tsaro da kuma farautar ‘yan ta’addan da suke aikata wannan aika-aika.

…………………………

To a can tarayyar Najeriya ma wani batun da ke da alaka da kungiyar Boko Haram wato batun ‘yan gudun hijira, na daga cikin abin da mutane ke ta magana a kansa, musamman ma a bangarorin da ‘yan gudun hijirar suke fuskantar matsaloli, duk kuwa da cewa mahukunta a yankunan da abin ya fi shafa wato a jahohin Borno da kuma Yobe gami da Adamawa, sun ce mutanen da suke zaunea wuraren da aka tsugunnar da ‘yan gudun hijira suna samun kulawa, duk kuwa da cewa adadinsu yana da yawa, domin kuwa a wani sansani guda da ke Maiduguria dadin wadanda ke cikinsa ya kai mutane miliyan daya da rabi, amma duk da hakan ana kokari wajen kula da su, kamar yadda ita ma hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta tababtar da hakan, sai wadanda suka warwatsu zuwa wasu yankunan ne da ba su da wata madafa, su ne suka fi shan wahala.

…………………………………………

To a can J . Demokradiyyar Congo kuwa a cikin wannan mako an sace wasu mutane da suke gudanar da wasu ayyuka na musamman domin taimaka al’ummar kasar.

Shugaban hukumar bunkasa kauyuka ta kasar Demokradiyyar Congo, Paul Muhasa, ya ce; An sace mutane 12 masu nazari da bincike tare da matukinsu a garin Katwiguru da ke gundumar Rutshuru.

Muhasa ya ci gaba da cewa: Mutanen da ake sace din suna gudanar da bincike ne akan  yanayi da kuma abinic a yankin, kuma kawo ya zuwa yanzu ba a tantance ko wace kungiya ce ta ke da alhakin sace mutanen ba.

Hukumar bunkasa kauyukan dai ta hada kai ne da hukumar abinci ta duniya domin bai wa ma’aikatan gona horo.

……………………………….

 

To jama’a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki, dole a nan zamu ja linzamin shirin, sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin na ke yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh