An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 29 October 2015 19:54

Zaben Shugaban Kasa A kasar Ivory Coast

Zaben Shugaban Kasa A kasar Ivory Coast
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku  acikin wannan shiri na Afirka a Mako, shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman batutuwa daga wasu cikin kasashen nahiyar, daga cikin abubuwan da shirin zai duba a yau, akwai zabukan da aka gudanar a kasashen Ivory Coast da kuma Tanzania, sai kuma batun tantance sunayen ministoci a majalisar dattijan Najeriya, da kuma ziyarar da shugaban Najeriya ya kai a cikin jahar Diffa, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya bamu hali. Sai a kasance tare da mu a cikin shirin.

 

…………………………….

Bari mu fara duba batun zaben shugaban kasa a kasar Ivory, inda a ranar Lahadi da ta gabata ce aka gudanar da zaben, inda ‘yan takara 7 da suka hada da shugaba Alassane Ouattara suka kara da juna. Hukumar zabe mai zaman kanta  akasar dai ta ce kimanin kashi 60% na wadanda suka cancanci yin zabe ne suka kada kuri’ari’unsu.

………………………….

To daga batun zaben Ivory Coast kuma bari mu je ga batun zaben kasar Tanzania, wanda shi ma ya gudana a ranar ta Lahadi da ta gabata, wanda kuma shi ne zabe da jam’iyya mai mulki ta CCM ta fuskanci babban kalu bale daga bangaren jam’iyyun adawa da suka yi kawance.

Jam’iyyar ta CCm dai tana rike mulkin kasar Tanzania tun shekaru 50 da suka gabata.

………………………………..

To a can tarayyar Najeriya a bangaren batutuwa na siyasa, batun ci gaba da tantance sunayen ministocin da shugaba Buhari ya mika wa majalisa da kuma kai ruwa rana da aka yi ta yi kan wasu sunayen, na daga cikin abin da ya dauki hankula a wannan mako a kasar.

Tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi, na daga cikin wadanda aka yi da kwangaba-kwanbaya kan batun tantance su, amma daga karshe dai majalisar ta tantance shi kuma ya wuce.

………………………………

To jama’a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki dole a nan zamu dasa aya sai Allah ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani shirin, kafin lokacin na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Add comment


Security code
Refresh