An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 09 October 2015 19:27

'Yan Boko Haram Sun Sake Kaddamar Da Hare-Hare A Najeriya

'Yan Boko Haram Sun Sake Kaddamar Da Hare-Hare A Najeriya
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimamn lamurra da suka wakana a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a yau da yardarm Allah shirin zai duba wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, daga cikin kasashen da shirin ai leka a yau a kwai tarayyar Najeriya, J. Nijar, Kamaru, Ghana da kuma Burkina Faso, da ma wasu kasashen na daban gwargwadon yadda lokaci ya bamu hali, domin duba batutuwa da suke da alaka da siyasa tsaro da sauransu, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin. ………………………………….

 

To bari mu fara shirin daga Najeriya, inda kuma za mu duba batutuwa ne da suka danganci tsaro a kasar a cikin wannan mako, inda a wannan mako ‘yan ta’adda suka kaddamar da hare-hare a birnin Abuja fadar mulkin tarayar Najeriya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 kamar dai yadda majiyoyin hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta tabbatar, biyo bayan hare-haren da aka kai a Kuje da kuma unguwar Nyanya.

Tun bayan kai hare-haren, jami’an tsaro sun dauki tsauraran matakan tsaroa  aciki da wajne birnin na Abuja, domin sa ido a kan dukkanin kai komon da jam’a suke yi a ko’ina, kamar yadda kuma jami’an tsaro suka bayyana hakan da cewa hankoro ne da kungiyar Boko Haram ke yi domin nuna cewa har yanzu tana nan.

A nasa bangaren shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci asibitin kasa (National Hospital) domin duba wadanda harin na Kuje da kuma Nyanya ya rutsa da su da suke karbar magani a asibitin, inda ya duba su kuma ya yi musu alkawalin cewa gwamnatin tarayya ce za ta dauki nauyin jinyansu baki daya.

 

…………………………………

To daga Najeriya kuma bari mu nufi J. Nijar, inda a can ma za mu duba batun tsaron ne, wanda shi ne ya fi daukar hankali a kasar a cikin wannan mako, sakamakon hare-haren ta’addanci da ‘yan kungiyar Boko haram suka kai a wasu bangarori a kasar, na baya-bayan nan shi ne na garin Diffa, inda akalla mutane 10 ne suka rasa raukansu.

Bayanai da jami’an tsaro suka bayar daga jahar ta Diffa sun tabbatar da cewa 'yan kunar bakin wake ne su hudu suka kaddamar da hare-haren a ranar Lahadi da safe, daga cikin wadanda suka rasu kuwakwai jami’in tsaro guda da kuma fararen hula 5 gami da maharani su 4.

Harin farko dai bam din ya tashi ne kusa da wani kanti sai na biyu wanda ya tashi a kusa da barikin rundunar tsaro yayin da dan kunar bakin wake na karshe ya sulale.

Ana zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram ne suka kai wannan hari, wanda shi ne na uku da kungiyar ta kai a yankin na Difa a cikin mako guda, bayan wanda suka kai a Barwa, inda suka yi wa sojoji kwanton bauna kuma suka kashe biyu daga cikinsu.

……………………………….

To a can kasa Burkina Faso kuwa jami’in sojin kasar ne suka sanar da kame Janar Gilbert Diendere wanda ya jagoranci juyin mulki a kasar a kwanakin baya, bayan kwashe kwanaki yana boye a cikin ofishin jakadancin fadar Vatican a Wagadugu, kuma ana tuhumarsa da zargin cin amanar kasa.

 

Yayin da a bnagare guda jami’an tsaro na kasar Burkina Faso suka saki mataimakin jagoran kungiyar ‘yan tawayen Abzinawan arewacin kasar Mali bayan cafke shi a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Wagadugu fadar mulkin kasar.

Jami’an tsaron dai sun cafke Muhammadu Gari Maiga mataimakin shugaban ‘yan tawayen Abzinawar Mali a jiya ne a lokacin da yake shirin ficewa daga kasar Burnina Faso, inda aka tsare shin a tsawon sa’oi yana amsa tambayoyi.

Mahukuntan Burkina Faso suna zargin ‘yan tawayen Abzinawan da marawa sojojin da suka yi juyin mulki baya, kamar yadda aka zargin Janar Diendere da hada baki baki da wasu kungiyoyi da suka hada har da na ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi a cikin mali domin taimaka musu.

…………………………………………………………….

A can jamhuriyar Afirka ta tsakiya kuwa, gwamnatin rikon kwarya ta kasar ce ta sanar da makoki na tsawon kwanaki uku dangane da kisan mutane kimanin 40 da aka yi a cikin wannan mako a kasar.

Shugabar rikon kwarya ta kasar Katharine Samba Panza ce ta sanar da makonin wanda aka fara daga ranar Litinin da ta gabata, kuma za a kammala a yau Laraba, domin juyayi kan abin da ya faru na kisan mutane 40 a kasar sakamakon rikicin da ya sake gocewa a kasar a cikin ‘yan kwanakin nan.

Kungiyoyin farar hula da dama suna gudanar da zanga-zanga a kasar tare da yin kira ga Samba Panza da safka daga kan shugaban kasar sakamakon kasa shawo kan lamurra a kasar.

A ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata ne dai aka kashe wani matashi musulmi a birnin Bangui fadar mulkin kasar, tare da cire kansa da kuma yin rubutun izgili ga musulmi da jininsa  akan gawarsa, lamarin da ya sak ejawo wani tashin hankali a birni.

……………………………………

A can kasar Ivory Coast kuwa hukumar zabe mai zaman kanta a kasar  ta sanar da cewa fiye da mutane miliyan 6 ne suka yi rijistar sunayensu domin kada kuri’a a zabukan da za a gudanar a karshen wannan wata.

Kakakin hukumar zaben Yusuf Bakayoko ne ya sanar da hakan, inda ya ce dukaknin adadin mutanen da suka yi rijistar sunayensu ya kai miliyan 6 da 300 da 142, adadin da ya hauara  na zaben shekara ta 2010, inda a lokacin mutane miliyan 5 da dubu 700 ne suka yi rijista, amma kimanin miliyan 4 daga cikinsu ne suka kada kuri’a.

Jam’iyyun adawa a kasar ta Ivory Coast suna zargin cewa dukkanin abin abubuwan da hukumart zaben take aiwatarwa, tana bayar da muhimmanci ga bangaren shugaba Allasane Ouattara, domin murkushe ‘yan adawa da kuma baiwa jam’iyya mai mulki nasara, zargin da hukumar zaben take musuntawa.

…………………………………..

An gudanar da wasu sauye-sauye a majalisar ministocin kasar Kamaru, ta hanyar sauyin wasu, wasu kuma an safke daga mukamansu baki daya, tare da nada wasu a kan mukaman nasu.

Wannan canjin ya taba guraban ministoci 15, inda aka canja wa tsoffin minstoci 6 ma’aikatu, yayin da 9 kuma aka sallame su baki daya, tare da maye gurbinsu da wasu.

Ministocin 9 da aka kora dai ana zarginsu da rashin iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata, da ma wasu zarge-zargen na daban, da suka hada da almundahana

Add comment


Security code
Refresh