An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 10 August 2015 18:24

Cikar Shekaru 55 Da Nijar Ta samu 'Yancin Kai

Cikar Shekaru 55 Da Nijar Ta samu 'Yancin Kai
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi a dubi a kan muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, a yau kamar kowane mako da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin muhimamn lamaurra da suka a waka a wannan mako inda za mu mayar da hankali a kan cika shekaru 55 da samun’yancin kai a Najar, da kuma batun ziyarar shugaba Buhari na Najeriya a jamhuriyar Benin, sai kuma batun tsaro tarayyar ta Najeriya.

 

Da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin.

 ………………………………..

To bari mu fara da batun bukukuwan cikar shekaru 55 da samun ‘yan kai a Jamhuriyar Nijar, wanda ake gudanarwa a kowace rana ta 3 ga watan Agusta, a wannan Litinin da ta gabata an gudanar da wadannan bukuwa a fadin kasar kamar yadda aka saba, shugaba Muhammad Yusuf ya gabatar da bayani inda yake yin kira zuwa ga zaman lafiya, tare da jadda kudirinsa na ganin dimokradiyya ta ci gaba a kasar, yayin da kuma wasu daga cikin jam’iyyun adawa kasar ke ganin babu wani ci gaba da aka samu a kasar, kuma ana yi dimokradiyya hawan kawara kamar yadad suke cewa.

…………………………

A cikin wannan mako ne shugaba Buhari na tarayyar najeriya ya kai wata ziyarar aiki a Jamhuriyar Benin da ke makwaftaka da kasarsa, inda ya gana da takwaransa shugaban kasar Benin Boni yayi.

Bangarorin biyu dai sun tattauna a kan muhimamn batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, musamman wadanda suke da alaka da tsaro, kasantuwar Benin an daga cikin kasashne 5 da suka kafa kawancen yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram.

Ziyarar ta Buhari a Benin ta samu karbuwa a wajen jami’an gwamnati da kuma al’ummar kasar, inda aka yi masa babbar tarba a birnin Kotonu, kamar yadda kuma mahukuntan kasar suka ba shi lambar yabo mafi girma a kasar.

Music…………………………………….

Dangane da batun tsaro kuwa rundunar sojin Najeriya ta ce a cikin ‘yan lokutan nan ana samun gagarumin ci gaba wajen murkushe ‘yan ta’adda na Boko Haram a cikin jahar Borno, inda suka kafa babbar tungarsu a kasar, inda bayanin ya tabbatar da cewa an fatattaki ‘yan ta’addan daga garuruwa da dama da suka kwace iko da su a lokutan baya, wanda hakan ne ma ya sanya su cana salon kai harinsu, domin a halin yanzu ba za su iya tunkarar sojojin Najeriya ba, sai dai su fakaici idanun jama’a su kai hare-haren bam a cikin kasuwanni, da masallatai, da sauran wuraren hada-hadar jama’ar.

…………………………………..

To jama’a lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki dole a nan za mu dakata, sai Allah ya sake hada mu a mako nag aba  acikin wani sabon shirin, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai har ya kammala musamman Muhamamd Aminu Ibrahim, ni da na shirya kuma na gabata, ke muku fatan alkhairi, wassalamu alikaum wa rahmatullah.

 

Add comment


Security code
Refresh