An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 04 August 2015 05:27

Ziyarar Shugaban Amurka Barack Obama A Kenya

Ziyarar Shugaban Amurka Barack Obama A Kenya
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi a dubi a kan muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, a yau kamar kowane mako da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin muhimamn lamaurra da suka a waka a wannan mako a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, daga cikin abubuwan da shirin zai yi dubi a kansu a wannan mako, akwai batun ziyarar shugaban kasar Amurka a kasar Kenya, sai kuma batun sakamakon zaben shugaban kasa a kasar Burundi, da kuma batun takaddamar shugabanci a cikin jam’iyyar MNSD Nasara mai adawa J. Nijar tsakanin bangaren shugaban jam’iyyar Seni Umaru da kuma bangaren Albade Abuba, kamar yadda kuma za mu duba wasu batutuwa da suka shafi harkar tsaro a Najeria da J. Kamaru, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu. ……………………………….. To bari mu fara da batun ziyarar shugaban kasar Amurka Barack Obama  a kasar Kenya, wadda ya fara a ranar Juma’ar da ta gabata, kuma ya kammala a ranar Lahadi. A yayin ziyarar tasa Obama ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar ta Kenya dangane da batutuwa daban-daban, musamman batun tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar, haka nan kuma ya gana da danginsa a bangaren mahaifinsa Hussain Obama wanda dan asalin kasar ta Kenya ne. Haka nan kuma Obama ya tattauna batun nan na auren jinsi wanda mahukuntan kasar ta Kenya suka yi watsi da shi, tare da tabbatar masa da cewa hakan ya saba wa al’adun mutanen kasar. …………………………… Dangane da zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Burundi kuwa, hukumar zaben kasar ce ta bayyana cewar Nkurunziza ya samu kaso 75 cikin 100 na kuri'un da aka kada. A cikin mako guda ne dai bayan sanar sa sakamakon ake sa ran tabbatar da shi, duk kwa da cewa ‘yan adawa dai sun kaurace wa zaben, tare da bayyana shi da cewa ya yi kama da wasan kwaikwayo, domin kuwa  acewarsu tuni shugaban kasar tare da hukumar suka shirya duk abin da suke son aiwatarwa, shi kuwa daya dan takarar Agathon Rwasa ya samu kaso 19 cikin dari daga kuri'un da aka kada. Kungiyar tarayyar turai ta fara tattauna batun dakatar da irin taimakon da take baiwa kasar ta Burundi, sakamakon zaben da aka gudanar wanda a cewar kungiyar ya yi hannun riga da sahihin tafarki na dimukradiyya, kamar yadda kuma wasu kungiyoyin na kasa da kasa suke ci gaba da sukar yadda aka gudanar da zaben. ……………………….   To dangane da batutuwan da suka shafi tsaro kuwa a tarayyar Najeriya da kuma Jamhuriyar Kamaru, a cikin makon nan mayakan kungiyar Boko Haram sun tsananta kai hare-hare a cikin kasashen biyu, daga ciki kuwa har da harin da aka kai a ranar Lahadi a lokacin da jama’a ke cin kasuwa a birnin Damaturu na jahar Yobe, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16 tare da jikkatar wasu da dama. Jami’an soji na tarayyar Najeriya sun ce wannan shi kadai ne abin da Boko Haram za ta iya yi a halin yanzu, amma ba tunkrara sojoji ko kwace garuruwa da suke yi lokutan baya ba, kuma tare da kokarin jami’ar tsaro da sauran jama’ar gari da ke bayar da hadin kai wajen gudanar da ayyukan tsaro, za a kawo karshen wannan matsala. A can jamhuriyar Kamaru ma an kai wani harin makamancin wannan a garin Marwa da ke arewacin kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkatar wasu da dama. …………………………… To bari mu sake komawa a tarayyar ta Najeriya, a cikin wannan mako ne majalisun dokokin kasar na dattijai da wakilai suka suka suka saurari korafin da kungiyar ‘yan jaridar ta kasar NUJ ta gabatar, dangane da matsin lamba da cin zarafi da ‘yan jarida suke fuskanta a Najeriya, tare da neman majalisun su sake yin dubi kan batun kare hakkoki da mutuncin ‘yan jarida a kasar. …………………………….   Wata badakala ta shugabanci ta kunno kai a jam’iyyar MNSD Nasara mai adawa tsakanin bangaren shugaban Jam’iyyar Seni Umaru da kuma Abade Abuba, bayan da kotun daukaka kara ta bayar da hukuncin cewa bangaren Albade Abuba na da hurumin ci gaba da gudanar da harkokinsu da sunan jam’iyyar. …………………………… To wannan muka kawo karshen shirin an wannan mako sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi wassalamu alaikum warahmatullah. End          

Add comment


Security code
Refresh