An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 23 July 2015 19:07

Shugaba Muhammad Buhari Na Najeriya Ya Ziyarci Kasar Amurka

Shugaba Muhammad Buhari Na Najeriya Ya Ziyarci Kasar Amurka
Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi a dubi a kan muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, a yau kamar kowane mako da yardarm Allah za mu duba wasu daga cikin muhimamn lamaurra da suka a waka a wannan mako a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, daga ciki kuwa har da sakonnin da wasu daga cikin sarakuna na masarautun Hausa a Najeriya da J. Nijar suka isa ga al’umma a lokacin bukukuwan salla karama da aka gudanar a wannan mako, sai kuma batun tsaro, akwai kuma batun gurfanar da tsohon shugaban Chadi a gaban kuliya a Senegal, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu. ………………………..

 

To bari mu fara shirin namu kan batun salla da ta gudana a cikin wannan mako, inda sarakuna da malaman addinin muslunci suka mika sakonni ga jama’arsu a manyan biranan Hausa a Najeriya da kuma J. Nijar, sakonnin dai sun mayar da hankali kan yin kira da a yi addu’a domin Allah ya kawo zaman lafiya a kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar da sauran kasashe makwabta da ma duniyar usulmi baki daya.

……………………

A ranar Lahadin da ta gabata ce shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya nufi kasar Amurka, domin gudanar da wata ziyarar aiki bayan samun goron gayyata daga shugaban kasar ta Amurka Barack Obama, inda a ranar Litin Obama ya tarbi shugaba Buhari a fadar White House tare da tawagarsa.

A yayin ganawar tasu Barack Obama ya bayyana cewa Buhari yana tsari mai kyau da yake da shi domin tunkarar ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram, haka nan kuma yana kyakkyawan tsari ta fuskar bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ya ce Amurka za ta taimaka ma Najeriya inda har gwamnatin ta Najeriya ba ta kauce wa wannan tsari ba.

A yayin ganawar tasu, sun tabo batutuwa da suka da alaka da tsaro a Najeriya, da kuma batun kara bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar, inda shugaban na Amurka ya ce kasarsa za ta aiki tare da gwamnatin shugaba Buhari musamman a wadannan fagage.

Obama ya ce Amurka tana bayar da muhimamnci matuka dangan eda duk wani abu da ya shafi Najeriya, saboda a cewarsa duk abin ya shafi Najeriya to yana tasirin ga nahiyar Afirka ne ba kasar kawai ba.

…………………….

To har yanzu dai a tarayyar ta Najeriya daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a wannan mako shi ne batun tsarin talala da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a kasar SSS suka yi wa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaroa  gwamnatin da ta shude Kanar sambo Dasuki, inda a ranar Lahadin da ta gabata hukumar ta fitar da bayani kan dalilan da suka sanya jami’an nata suka kai wannan samame a gidan nasa da ke unguwar Asokoro a cikin birnin Abuja.

Inda ta ce sun yi hakan ne da nufin gudanar da bincike a hukumance, amma yaki amincewa da hakan sai bayan da aka kai ruwa rana, daga bisani dai jami’an na hukumar SSS sun gudanar da aikinsu a gidan nasa.

Bayanin ya ce an samu manyan motoci 12 a gidan, da suka hada da 5 masu sulke, kamar yadda kuma aka samu manyan bindigogi masu sarrafa kansu guda 7 a cikin gidan nasa, kuma ya kasa amsa tambayoyin da aka yi masa kan lasisin mallakar motocin masu sulke.

…………………………….

A can kasar Somalia kuwa, rundunar tarayyar Afirka da ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar ce ta sanar da cewa an fara kaddamar da wani gagarumin farki kan sansanonin ‘yan kungiyar Al-shabab reshen Alkaida a kasar Somalia.

Bayanin wanda rundunar kungiyar tarrayar Afirka ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya tabbatar da cewa, an fara fatattakar mayakan Alshabab daga wasu sansanoninsu da ke kudancin kasar, duk kuwa da cewa ana tafka matsanancin gumurzu tsakaninsu da mayakan na Alshabab, amma kuma babu gudu babu ja da baya har sai an murkushe dukaknin mayakan ‘yan ta’addan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ranar da aka gudanar da idin karamar salla a kasar, jagoran kungiyar ta Alshabab Ahmad Umar Abu Ubaidah ya sanar da cewa, a cikin kwanaki masu zuwa za su tsananta kai hare-harensu a cikin kasashen Somalia da kuma Kenya, lamarin da ya kara zaburar da rundunar ta tarayyar Afirka domin kara daura damarar yaki da mayakan kungiyar, da ke da alaka da Alkaida.

……………………………….

To bari mu sake komawa J. Nijar, inda gungun ma’aikatan ma’aikatar kudi a kasar suka sanar da sake shiga wani yajin aiki na kwanaki 5 a karo na biyu, domin kokawa dangane da abin da suka kira rashin yin aiki da dokar biyansu wasu alawus-alawus da ya kamata a ba su, to amma kuma a nasu bangaren wasu kungiyoyin farar hula suna ganin cewa  wannan doka ta saba wa kaida, daga cikin har da kungiyar MPCR karkashin jagorancin Malam Nuhu Arzuka, ga kuma abin da yake cewa kan wannan batu:

………………………………..

A ranar Litinin da ta gabata ce aka gurfanar da tsohon shugaban kasar Chadi Hussain Hibre a gaban kotu a birnin Dakar na kasar Senegal, inda ake tuhumarsa da tafka laifukan yaki kan al’ummar kasar Chadi a lokacin da yake shugabancin kasar.

A lokacin da ya gurfana a gaban kotun, tsohon shuagaban kasar ta Chadi ya yi ta Magana yana daga murya, ta yadda ya hana sauraren alkalan kotun, inda yake fadin cewa shari’ar aikin shirme ce kawai, tare da musunta dukkanin tuhumomin da ake yi masa, daga bisani dai kotun ta bayar da umarnin da a fice da Hussain Hibre daga wurin, yayin da kuma wasu magoya bayansa da ke wajen kotun suka yi ta rera taken yabonsa.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar tarayyar Afirka ta gurfanar da wani tsohon shugaba na wata kasar Afirka a gaban kuliya tana tuhumarsa da aikata laifukan yaki kan al’ummar kasarsa.

……………………….

To yanzu kua bari mu nufi kasar Kamaru, inda rahotanni daga garin kamouna suka ce daukacin mutanen garin sun tsere zuwa wasu garuruwa da ke kusa da garin nasu, sakamakon munanan hare-haren da ‘yan Boko Haram suka kai musu.

Shedun gani da ido sun tababtar da cewa a lokacin da maharan na Boko haram suka kai harin, sun yi ta saka wuta a ko’ina, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ta hanyar konewa da wuta, da suka hada har da kananan yara, yayin da kuma sauran al’ummar garin suka yi ta gudu domin tsira da rayukansu.

Wannan dai na daga cikin munanan hare-hare da ‘yan ta’addan an Boko Haram suka kai a cikin Kamaru a kwanakin baya-bayan nan, a daidai lokacin da mahukuntan kasar ke kara damarar shiga yaki gadan-gadan da mayakan kungiyar.

………………………………

A jamhuriyar Afirka ta tsakiya kuwa, Firayi ministan kasar kasar ne  Mahamat Kamoun ya sake gudanar da wani garanbawul a majalisar ministocin kasar a daidai lokacin da ake fuskanta zabuka masu zuwa a kasar.

Mahamat Kamoun ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa, sabuwar majalisar ministocin kasar ce za ta jagoranci lamurra daga nan har zuwa lokacin gudanar da zabukan kasar a cikin watan Oktoba mai zuwa, haka nan kuma ya bar wasu daga cikin muhimamn ma’aikatun kasar da tare da ministocinsu ba tare da wani canji ba, da hakan ya hada da ministocin tsaro, harkokin cikin gida da kuma shari’a.

Daga cikin ma’aikatu masu matukar muhimmanci Mahammat ya gudanar da garambawul a kansu har da ma’aikatar harkokin cikin gida, sadarwa da kuma ma’aikatar sulhu tsakanin al’ummar kasa.

………………………………….

To jama’a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki, dole a nan za mu dakata, sai idan Allah ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani sabon shirin, kafin lokacin, a madadin wadanda suka hada sautin shirin a faifai har ya kammala, ni Abdullahi Salihu da na shirya na gabatar, nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

 

 

 

 

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh