An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 12 June 2015 10:44

Buhari Ya Fara Da Ziyartar Jamhuriyar Nijar Bayan Rantsar Da Shi

Buhari Ya Fara Da Ziyartar Jamhuriyar Nijar Bayan Rantsar Da Shi
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, shirin da kan yi dubi a cikin wasu muhimman lamurra da suka waka a cikin nahiyar Afirka, inda a yau ma da yardarm Allah shirin zai duba wasu batutuwan, da suka hada da ziyarar farko da sabon shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya kai kasashen Nijar da kuma Chadi, da kuma cimma yarjejeniyar sulhu a tsakanin bangarorin Abzinawa ‘yan tawaye na arewacin Mali da kuma gwamnatin kasar, da kuma matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a kasar Ghana, wadda ta haddasa gobara da kuma asarar rayukan jama’a, da ma wasu batutuwan gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da  fatan za a kasance tare da mu.

 

………………………………………

To shirin namu zai fara ne da batun ziyarar sabon shugaban tarayyar Najeriya Muhmmad Buhari ya kai a Jamhuriyar Nijar, wadda ita ce ta farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa. Babbar manufar ziyarar dai ita ce kara bunkasa alaka tsakanin kasahen biyu a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da batun tsaro, musamamn ma batun Boko Haram da yadda kasashen biyu za su tunkari wannan matsala. Bayan kammala ziyara a J. Nijar Shugaba Buhari ya nufi kasar Chadi inda a can ma ya gana da shugaban kasar Idris kan wannan batu.

……………………………..

Bayan kammala ziyarar tasa a kasashen Nijar da Chadi, ba tare da bata lokaci ba kuma ya nufi kasar Jamus, inda ya halarci babban taron shekara-shekara na kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya, inda ya gana da manyan shugabannin kasashen duniya, da suka hada da shugaban Amurka Barack Obama, da kuma na Faransa, gami da shugabar gwamnatin Jamus da kuma da Firayi ministan kasar Birtaniya.

………………………………..

A can kasar Mali kuwa babbar kungiyar ‘yan tawayen abzinawa a arewacin kasar ce ta  cimma matsaya dangane da yarjejeniyar sulhu tsakaninsu, kuma nan da makonni biyu masu zuwa za a rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.

Mai jagorantar tawagar gamayyar kungiyoyin abzinawa ‘yan tawaye a arewacin Mali Bilal Agh Sharif ya ce a tattaunawar da suka gudanar a birnin Aljiers na kasar Aljeriya, sun cimma daidaito tare da bangaren gwamnatin Mali kan wannan yarjejeniya, kuma bangarorin biyu za su rattaba hannu a kanta a ranar 20 ga wannan wata na Yuni.

An cimma wannan yarjejeniya dai tare da halartar wakilan majalisar dinkin duniya, kungiyar tarayyar turai, kungiyar tarayyar Afirka gami da na ECOWAS, wasu masu majiyoyin diplomasiyyah sun sheda cewa daftarin yarjejeniyar ya amince da mika wasu manyan mukamai na gwamnatin kasar Mali ga kungiyoyin, kamar yadda kuma za a saka wasu daga cikin mayakan ‘yan tawayen a cikin ayyukan tsaron kasar ta Mali a hukumance, musamamn ma wadanda za su mayar da hankali wajen ayyukan tabbatar da tsaro a arewacin kasar.

…….………………………………

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya kai wata ziyara a kasar Ghana domin taya al’ummar kasar alhinin abin da ya faru na ambaliyar ruwa wadda ta jawo matsananciyar gobara a birnin Akra, da ta lakume rayukan mutane kimanin 200, kamar yadda gwamnatin kasar Ivory Coast ta aike da wata tawaga a karashin jagorancin ministan man fetur na kasar, inda suka yi rangadi tare a asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka samu raunuka sakamakon wannan ambaliyar da gobara. Tawagar ta kasar Ivory Coast ta bayar da taimakon magunguna na musamman da suka shafi kunar wuta, wadanda suka kai nauyin ton biyu.

………………………….

To bari mu sake komawa jamhuriyar Nijar, inda a ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da wata zanga-zanga da kungiyoyin farar hula kimanin 40 suka kira, domin nuna rashin gamsuwarsu dangane da yadda lamurra suke wakana a kasar, inda suke cewa akwai tarin matsaloli da ya kamata a gwamnati ta dauki matakan warwarewa da han yanzu ba su gani a kasa ba.

………………………….

To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin namu na wannan mako, sai idan Allah mai kowa da komai ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani sabon shirin, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai musamman Muhammad Aminu Ibrahim Kiyawa, ni Abdullahi Salihu Katsina ke yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

 

 

 

  

Add comment


Security code
Refresh