An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 25 March 2015 19:10

Hukumar Zabe Ta Kammala Shirin Zabe A Najeriya

Hukumar Zabe Ta Kammala Shirin Zabe A Najeriya
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, shirin da kan yi dubi a kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suke wakana a nahiyar Afirka.  

 

A yau shirin zai mayar da hankali ne kan batun siyasar Najeriya, inda yanzu haka kwanaki uku ne rak suka rage a gudanar da zabe, bayan nan kuma za mu leka jamhuriya Nijar domin jin yadda aka kammala gasar kokowar gargajiya kasar ta bana, da fatan za a kasance tare da mu.

 

Music………………………………..

 

To bari mu fara shirin namu daga tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako ne shugaba Jonathan ya kai ziyara a birnin Daura da ke jahar Katsina, kuma mahaifar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammad Buhari, inda aka bayyana ziyarar da cewa ta nadin sarauta ce da sarkin Daura ya yi masa, amma sarki ya kore hakan sakamakon suka da yake sha daga mutane kan tarbar Jonathan da ya yi..

 

…………………………………..

 

To a nasa bangaren kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta APC janar Muhammad Buhari, ya gana da mayan 'yan kasuwa da kuma wasu kungiyoyin ma'aikata masu zaman kansu, a Abuja, inda ya yi musu alkawalin cewa matukar dai ya samu nasara a zabe mai zuwa, to kuwa zai mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro, da kuma yaki da cin hanci da rashawa, wanda hakan shi ne babban abin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci, da habbaka tattalin arzikin kasa.

 

………………………………………………….

to a daya hannu kuma jam'iyyar adawa ta APC ta bayyana cewa, tana da shirye-shirye da take aiwatarwa, domin tabbatar da cewa zabukan da za a gudanar a kasar sun gudana cikin nasara, ta hanyar wayar da kan jama'a musamamn mata da matasa da kuma mutanen karkara, dangane da zaben da kuma abubuwan da ya kamata a kiyaye a lokacinsa, tare da tabbatar da cewa an kauce ma duk wani abin da zai kawo rudani da kuma tashin hankali.

 

………………………….

 

To a can jamhuriyar Nijar kuwa, a ranar Lahadi da ta gabata ce aka kawo karshen gasar kokowar gargajiya kasar da aka saba gudanarwa a kowace shekara, wanda kuma wannan shi ne karo na 36 da aka gudanar da wannan gasa da birnin Agadez dake arewacin kasar ya karbi bakunci, inda kuma dan wasan kokowa Isaka Isaka daga jahar Dosso ya dauke takobin, wanda ya bashi danar zama sarkin kokowa na wannan shekara.

 

……………………………….

 

To jama'a masu saurare ganin lokacin da muke da shi ya kawo jiki, a nan za mu dasa aya, sai idan Allah mai kowa da komai ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai har ya kammala, Abdulahi Salihu Usman Katsina daya tsara shirin ni Hassan Barka dana gabatar nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakkatuhu.

 

Add comment


Security code
Refresh