An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 22 February 2015 14:19

Taron Shugabannin Kasashen Yankin Afirka Ta Tsakiya A Kamaru

Taron Shugabannin Kasashen Yankin Afirka Ta Tsakiya A Kamaru
Assalamu Alaikum jama’a masu saurare barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi dubi a cikin wasu muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar Afirka a cikin mako. A wannan makon da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin batutuwan tsaro da siyasa a tarayyar Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar, kamar yadda za mu duba batun kisan misrawa 21 da ‘yan ta’addan ISIS suka yi a kasar Libya, da kuma martanin kasar ta Masar kan lamarin, haka nan kuma za mu duba batun zaman shugabannin kasashen Afirka da ke fama da cutar Ebola, da kuma jin irin matsayar da suka dauka domin fuskantar wannan lamari, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, sai a kasance tare da mua  cikin shirin.

 

……………………………………..

To bari mu fara da batun tsaro a Najeriya, a cikin wannan makon daruruwan mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar da hari a birnin Gombe fadar mulkin jahar Gombe da ke arewa maso gabacin kasar, da nufi kwace iko da birnin baki daya, amma jami’an tsaro da suka hada da sojoji da kuma ‘yan sanda sun yi ba ta kashi tsanani tsakaninsu da mayakan na Boko Haram, inda mayakan sama na tarayyar Najeriya suka yi amfani da jiragen sama na yaki wajen kaddamar da hare-hare a kansu, wanda hakan ya tilasta su suka janye, bayan da wasu bayanai suka ce sun kwashi tarin makamai a wasu wurare na soji.

Mahukunta a jahar dai sun kafa dokar ta baci jim kadan bayan faruwar lamarin, da nufin shawo kan lamarin da kuma tabbatar da tsaro a birnin.

……………………………………..

A jahar Borno ma jami’an soji sun sanar da cewa sun yi artabu da mayakan na Boko Haram a ranakun Lahadi da Litinin da suka gabata, lamarin da ya ba su damar fatattakarsu daga wasu yankuna na jahar da suka kwace iko da su a watannin baya, kamar yadda shi kansa Kashim Shattima ya tabbatar wa wasu kafofin yada labarai da inganci wanann bayani na rundunar sojin Najeriya.

…………………………….

To a can jamhuriyar kuwa kura ta lafa a garin Diffa bayan artabuy da mayakan na Boko haram, wadanda suka kai hare-hare a cikin garin, amma jami’an tsaro sun dakile yunkurin nasu, kamar yadda jami’an tsaron na Nijar suke ci gaba da sintiri a birnin domin tabbatar da doka da oda, haka nan kuma wasu bayanai sun tabbatar da cewa tuni jami’an tsaron suka yi awon gaba da jagoran ‘yan kungiyar ta Boko haram a jahar Diffa tare da wasu daga cikin mukarrabasa, an kuma samu tarin makamai masu matukar hadari a cikin gidan nasa.

……………………………..

To wani batun wanda shi ma yake da alaka da Boko haram din shi ne zaman taron da shugabannin kasashe mamobi a kungiyar bunkasa harkokin tattalin yankin tsakiyar Afirka suka gudanar  a birnin Yawunde na kasar kamaru, domin tattauna yadda gwamnatocin wadannan kasashe za su fuskanci hadarin kungiyar Boko Haram a yankin tsakiyar Afirka.

Taron dai ya samu halartar shugabannin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Congo Brazzavile, Gabon, Equatorial Guinea, Chadi da kuma Kamaru mai masafkin baki.

Dukkanin shugabannin wadannan kasashe dai sun hadu a kan cewa hadarin kungiyar Boko haram bai takaitu da Najeriya ba kawai kawai, lamari ne da su ma ya shafe su kai tsaye, kuma dole ne a hada karfi da karfe domin fuskantar wannan barazana ta ‘yan ta’addan Boko Haram.

………………………

To dangane da batun siyasa wanda shi ma yake da alaka da tsaro kai tsaye a tarayyar Najeriya kuwa, tun bayan furucin shugaba Jonathan da ke cewa za a kwato dukkanin ‘yan matan Chibok da ‘yan Boko Haram suka kwace nan da ‘yan makonni masu kuwa, wasu daga cikin masu fafutuka domin ganin an kwato yaran tare da dawo da su zuwa ga iyalansu da kuma wasu daga ckin wakilan ‘yan yankin na Chibok da ke cikin wannan, sun nuna shakku matuka dangane da hakan, yayin da wasunsu ma suka yi watsi da wannan furuci. ……………………………………

A ranar Lahadi da ta gabta ce mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na IS suka nuna wani faifan bidiyo, da ke nuna yadda suka yi wa wasu Misrawa kibdawa kisan gilla ta hanyar yi musu yankan rago a gabacin garin Sirte na kasar Libya, lamarin da ya tayar da hankulan al’ummomin kasar ta Masar.

Kafin yi mutanen 21 yankan rago, wanda ya jagoranci kisan ya yi jawabi da a cikinsa yake cewa, kungiyar ta IS wadda ke da’awar kafa daular muslunci, za ta fadada ikonta da ya ce zai hada har da biranan makka da Madina, bayan yin kamalamai batunci ga mabiya a ddinin kirista da kuma kafirta musulmi da ba su cikinsu, daga nan kuma suka sharara ma mutanen wuka suka cire musu kawuna baki daya.

‘Yan sa’oi bayan fitar da faifan bidiyon, jiragen yakin kasar Masar suka yi lugudan wuta a kan sansanonin ‘yan ta’adda na IS a cikin kasar Libya, tare da lalata runbunan makamai na kungiyar da dama, bayanin rundunar sojin Masar y ace an kashe mayakan IS da dama da suka haura 60 a lokacin kai harin, kuma za a ci gaba da yin hakan har sai an ga bayansu a cikin kasar Libya.

Gwamnatin kasar ta Libya dai ta fito ta nuna goyon bayanta ga kasar Masar dangane da wannan mataki da ta dauka ba tare da wani bata lokaci ba.

………………………………………….

To a bangaren kuma da ya shafi batun lafiya a nahiyar ta Afirka, shugabannin kasashen Guinea, Saliyo da kuma Liberia sun sha alwashin kawo karshen cutar Ebola  a cikin kasashensu baki daya daga nan zuwa tsakiyar watan Afirilu mai kamawa.

Shugabannin kasashen da ke fama da matsalar cutar Ebola sun bayyana hakan ne a wani zama da suka gudanar a birnin Conakry na kasar Guinea a ranar Lahadi da ta gabata, inda suka cimma matsaya kan yin aiki tukuru domin kawo karshen cutar wadda ta lakume rayukan mutane da dama a cikin kasashensu, haka nan kuma sun bukaci karin taimako daga sauran kasashen duniya domin cimma wannan manufa.

Tun a cikin watan Disamban shekara ta 2013 ne dai cutar ta Ebola ta bulla a kasar Guinea Conakry, daga bisani kuma bulla zuwa kasashen Liberia da Saliyo, inda ta fi mummunar barna, ya zuwa yanzu kimanin mutane 9177 suka rasa rayukansu sakamakn kamuwa da cutar ta Ebola.

…………………………….

To jama’a masu saurare lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki, dole a nan za mu dakata, sai a idan Allah ya kai mua  mako nag aba za a ji mu dauke da wani sabon shirin, amma kafin lokacin, a madadain wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai har ya kamma, musamman Muhamamd Amiru Ibrahim, ni da na shirya na kuma na gabatar, nake yi muku fatan alkahiri, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

   

Add comment


Security code
Refresh