An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 05 February 2015 08:45

Yakin Neman Zabe A Najeriya

Yakin Neman Zabe A Najeriya
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka  a Mako, inda shirin kan duba wasu daga cikin abubuwan da suka faru a wasu daga cikin kasashen nahiyar, domin yin tsokaci kansu, shirin na yau zai yi tsokaci ne kan batutuwa da suka shafi lamurran siyasa da tsaro a Nigeria, da kuma batun martanin da jam’iyyun adawa a J. Nijar suka mayar wa gwamnati, kan zanginsu da hannu a zanga-zangar da matasan kasar suka gudanar wadda ta koma tashin hankali a makon da ya gabata, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali. ……………………………….. To bari mu fara shirin namu daga tarayyar Najreiya, za mu fara ne kuma da batun tsaro wanda shi ne ya fi ci wa al’ummar kasar tuwo a kwarya, inda a cikin wannan mako ne yan bindiga na kungiyar Boko Haram suka kaddamar da hari a garin Maiduguri na jahar Borno kwana daya bayan ziyarar da shugaba Jonathan ya kai garin, duk kuwa da cewa bayanai sun ce jami’an soji sun dakile yunkurin na Boko Haram a kan birnin Maiduguri, kafin lokacin dai ‘yan Boko Haram sun fitar da wani fafan bidiyo da suke yin barazanar kai munanan hare-hare a wasu yankuna na kasar, amma shugaban hukumar sadarwa ta musamman kan harkokin tsaro a Najeriya ya sheda wa dan rahotonmu a Abuja cewa suna yin dubi da idon basira kan wannan batu. …………………………………… To a bangaren batutuwa na siyasa kuwa, a cikin wanann makon ne kwalejin katsina ta fitar da sakamakon jarabawar karshe ta kamala karatu da janar Buhari ya rubuta a lokacin da ya kamala karatunsa na sakandare a wannan makaranta, wannan kuwa ya biyo bayan bayanan da ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki suka yi na cewa janar Buhari bai kamala karatun sakandare ba. …………………….. To sai dai bayan fitar da wannan sakamao da shugaban makarantar Isiyaku Bello ya yi, an yi ta yada cewa ana yi ma rayuwarsa barazana, daga bisani kuma aka rika bayyana cewa ma an kashe, amma rundunar ‘yan sanda ta jahar Katsina ta karyata, kamar yadda shi ma da kansa shugaban makarantar ya fito ya sheda wa manema labarai cewa: ……………………… To wani batun kuma wanda shi ma ya dauki hankali tare da jawo kace-na-ce shi ne furucin da babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki ya yi, da ke neman a daga lokacin gudanar da zabe, to amma dan rahotonmu a Abuja ya tuntubi shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Attahiru Jega kan batun ya ce a halin yanzu ba zai yi gaggawar cewa komai kan lamarin ba, duk kuwa da cewa a kwanakin baya ya sheda wad an rahoton namu cewa zabe na nan daram kamar yadda aka shirya shi. …………………………. To a can J. Nijar kuwa  jam’iyyun adawa ne suka mayar wa gwamnati martani, kan zarginsu da hannu a zanga-zangar da matasan kasar suka gudanar wadda ta koma tashin hankali a makon da ya gabata, sakamakon nuna bacin rai kan zanen batuncin da jaridar Charlie Hebdo ta yi ga manzon Allah, wanda shugaban Nijar ya halrci gangamin da wasu shugabanni suka yi a Paris domin nuna goyon bayansu ga jaridar dangane da harin da aka kai mata. ………………………   To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin nay au, sai Alah ya hada mua  mako nag aba, kafin lokacin a madadin muhd Awwal Kunya da ya hada shirin a faifai, ni Abdullahi salihu da na shirya kuma na gabatar, nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.     

Add comment


Security code
Refresh