An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 25 January 2015 11:59

Zuwan Muhammadu Isufu Faransa Ya Jawo Tashin Hankali A Nijar

Zuwan Muhammadu Isufu Faransa Ya Jawo Tashin Hankali A Nijar
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka  a Mako, inda shirin kan duba wasu daga cikin abubuwan da suka faru a wasu daga cikin kasashen nahiyar, domin yin tsokaci kansu, shirin na yau zai yi tsokaci ne kan tashe-tashen hankula da suka faru a jamhuriyar Nijar, da kuma martanin da dan takarar shugabancin kasa a Najeiya karkashin jamiyyar adawa ta APC janar Muhammad Buhari ya mayar, kan jita-jitar da ake yadawa cewa an fita da shi magashiyan zuwa kasashen ketare ba shi da lafiya, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin. Music………………………………..

 

To bari mu fara shirin namu daga jamhuriyar Nijar, a cikin wannan mako ne dai matasa suka gudanar da zanga-zanga a biranan Yamai, Damagaram da kuma Agadez, domin nuna bacin ransu dangane da zane-zanen batunci ga manzon Allah da jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta buga, kamar yadda kuma da dama daga cikin matasan da suka shiga zanga-zangar suka nuna bacin ransu kan halartar da shugaban kasar Muhammad Issufu ya yi a gamgamin da aka yi a birnin Paris domin nuna goyon bayansu ga wanann jarida sakamakon harin da aka kai kanta tare da kashe wasu daga cikin ma’aikatanta, inda wasu ke bayyana cewa furucin da shugaba Muhamamd Issufu ya yi na cewa Charlie ne kuma dukkanin al’ummar Nijar ma Charlie ne, hakan shi ne babban abin da ya bakanta musu rai. Wasu daga cikin matasan sun kai kaddmar da farmaki kan wasu kaddarori na gwamnati da kuma mabiya addinin kirista da kuma na jam’iyya mai mulki, inda har wasu suka rasa rayukansu a Yamai da kuma Damagaram.

………………………………

Wannan zanga-zanga dai ta zo ne kwana daya kafin wata zanga-zangar da manyan jam’iyyun adawar kasar suka shirya yi tun a lokutan baya, inda su ma suka gudanar da tasu zanga-zangar kashe gari, amma jam’ain tsaro sun yi amfani da karfi wajen murkushe su, tare da kame adadi mai yawa daga cikinsu, lamarin ya sanya mahukunta a jamhuriyar Nijar suka danganta zanga-zangar matasan da kuma ta ‘yan adawa.

…………………………..

To sai dai a nasu bangaren ‘yan adawar sun mayar da martani da cewa gwamnati ta amfani da karfin iko ne domin han gudanar da abin da dokar kasa ta basu damar yi.

…………………………….

To a can tarayyar Najeriya kuwa,  dan takarar shugabancin kasa a Najeiya karkashin jamiyyar adawa ta APC janar Muhammad Buhari ne a zantawarsa da dan rahotonmu daga Abuja Muhammad sani Abubakar  ya mayar, kan jita-jitar da ake yadawa cewa an fita da shi magashiyan zuwa kasashen ketare ba shi da lafiya, inda ya ce lafiyarsa lau, kuma wadanda suke yada hakan manufarsu ita ce karya zukatan ‘yan najeriya.

………………………..

To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin nay au, sai Alah ya hada mua  mako nag aba, kafin lokacin a madadin muhd Awwal Kunya da ya hada shirin a faifai, ni Abdullahi salihu da na shirya kuma na gabatar, nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    

Add comment


Security code
Refresh