An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 13 January 2015 12:43

Janar Buhari Ya Yi Allawadai Da Kone Motocin PDP A Plateu

Janar Buhari Ya Yi Allawadai Da Kone Motocin PDP A Plateu
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka  a Mako, inda shirin kan duba wasu daga cikin abubuwan da suka faru a wasu daga cikin kasashen nahiyar, domin yin tsokaci kansu, daga cikin abubuwan da shirin zai yi dubi a kansu a yau akwai batutuwan tsaro da siyasa a Najeriya, da kuma yadda aka gudanar da Maulidin manzon Allah (SAW) a jamhuriyar Nijar, da fatan za a kasance tare da mu.

 

…………………………………

To madalla, bari mu fara batutuwan siyasa daga tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako hukumar zabe ta kasar ta sake jadda matsayinta na tabbatar da cewa za ta tsaya kai da fata domin ta ga an yi aiki da dokokin zabe kamar yadda suke a rubuce a cikin kudin dokokin zabe, ba tare da yin la’akari da matsayinsa na jam’iyya ko na mukamin gwamnati ba.

………………………

A cikin wannan makon ne wasu matasa a jahar Palateu suka kai farmaki kan motocin kamfe na dan takarar shuagabancin kasa na jam’iyyar PDP, kuma wanda ke rike da kujerar shugabancin Najeriya a halin yanzu Goodluck Ebele Jonathan, inda aka kone motocin biyu kurmus, tuni dan karar shugabanci kasa na babbar jam’iyyar adawa ta APC janar Muhammad Buhari yay i Allawadai da harin.

…………………………….

A bangaren batun tsaro kuwa, wanda si ne ya fi ci wa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya kuwa, a wannan makon an kai munanan hare-hare a sassa na arewa maso gabacin kasar, musamman a cikin jahohin Yobe da kuma Borno, mafi daukar hankali daga ciki kuwa shi ne harin Baga, wanda bayanai ke cewa ‘yan bindiga na Boko Haram sun kashe mutane kimanin 2000, duk kuwa da cewa jami’an sojin Najeriya sun kore wanann batu, inda suka ce akwai Karin gishiri matuka a cikin maganar, inda suka bayyana cewa mutanen da aka tabbatar da sun mutu sakamakon harin na Baga sun kai kimanin 150, dubbai kuma sun yi gudun hijira, bayanan kuma sai hare-haren birnin Maiduguri. A ranar Lahadin da ta gabata ma an kai wani harin na kunar bakin wake a wata kasuwa ta masu sayar da wayar salula a garin Potiskuma na jahar Yobe.

…………………………………

To wannan batu na matsalar tsaro a Najeriya bai tsaya nan ba kawai, domin kuwa a halin yanzu lamarin ya shafi wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar kai tsaye, inda yanzu haka akwai mutane kimanin 100,000 da suka yi gudun hijira daga yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula a jahohin Borno da Yobe da ke iyaka da jamhuriyar Najar da suka shiga cikin kasar ta Nijar, wadanda suka hada da ‘yan najeriya da kuma ‘yan Nijar mazauna Najeriya, inda mahkuntan na Nijar suka tabbatar da cewa kimanin mutane 60,000 da ‘yan kai ‘yan najeriya, yayin da 30,000 da ‘yan kai daga cikin ‘yan gudun hijira ‘yan Nijar ne mazauna Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida na J. Nijar Hassan mas’udu ya yi manema labarai Karin bayani dangane da halin da ake ciki, kan irin taimakon da suke bayarwa, da kuma wanda kasashen waje ke bayarwa domin taimaka masu gudun hijirar, haka nan kuma ministan na Nijar ya kore bayanan da ke cewa matasa da dama daga cikin jahar Difa sun shiga cikin Najeriya sun hade da ‘yan Boko haram, inda aka ce ana basu makudan kudade domin kai hare-hare.

…………………………….

To a cikin wannan mako ne dai aka gudanar da tarukan Maulidin manzon Allah a kasashe na duniya daban-daban, inda musulmi a kasashen nahiyar Afirka ba a barsu a bay aba wajen raya wadannan taruka a wadannan ranaku masu albarka, da ake tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta manzon (SAW) a wannan karo za mu yada zango ne a jahar Agadez ta Jamhuriyar Nijar, domin jin yadda wadannan taruka masu albarka suka gudana a jahar.

……………….

To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin nay au, sai Alah ya hada mua  mako nag aba, kafin lokacin a madadin muhd Awwal Kunya da ya hada shirin a faifai, ni Abdullahi salihu da na shirya kuma na gabatar, nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Add comment


Security code
Refresh