An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 15 December 2014 03:17

Zanu PF Ta Sake Zaben Mugabe A matsayin Shugabanta

Zanu PF Ta Sake Zaben Mugabe A matsayin Shugabanta
Jama' masu saurare Assalamu alaikum, barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, inda shirin ya kan kawo muku wasu daga cikin muhimman lamurra daga nahiyar Afirka, kamar kullum a yau ma zai mayar da hankali kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wasu daga cikin kasashen nahiyar a mako, amma sai mun fara da batun ziyarar da ministan harkokin watsa labarai na J. Nijar Alh. Yahuza Sadisu Madobi ya kawo nan jamhuriyar Njar domin halartar wani taro na ministocin harkokin watsa labarai na kasashen musulmi, bayan nan kuma za mu duba wasu batuuan daga nahiyar Afirka, da fatan za a kasance tare da mu.  

 

…………………………………………..

 

To bari mu fara da batun ziyarar ministan watsa labarai na jamhuriyar Nijar Alh. Yahuza Sadisu Madobi a nan Tehran, wanda kuma ya yi ganawa ta musamman da sashen Hausa na muryar jamhuriyar muslunci ta Iran.

……………………………..

 

To can Najeriya kuwa a cikin wannan mako ne aka kame wani jirgin daukar mallakin wani kamfanin jiragen kasar Rasha dauke da wasu makamai, bayan da jirgin ya yada zango a filin safka da tashin jiragen sama na malaman Aminu Kano da ke birnin kano, daga bisani mahukunta a kasar sun bada izinin tashin jirgin.

 

Majiyar watsa labarun kasar Rasha ta ambato Ofishin jakadancin kasar da ke birnin Abuja yana cewa; Tuni jirgin saman daukar kayan ya tashi zuwa kasar Chadi a ranar Litinin bayan da ya sami izini daga mahkuntan Najeriya.

 

Jirgin saman wanda mallakin kasar Rasha ne yana kan hanyarsa ne daga Bungui zuwa Chadi, sai dai ya  yada zango a birnin kano, bayan da aka rufe filin saukar jiragen sama na birnin  N'Djamena.

 

Bayan tsayawar jirgin samar a filin saukar Jirage na Malam Aminu Kano, an kame ma’aiktansa biyar bayan da aka sami jirage masu saukar Angulu guda biyu na  Faransa  da kuma motoci masu silke da akwatunan albarusai.

 

……………………………….

 

A cikin wannan makon ne jam'iyyar adawa mafi girma a Najeriya ta APC ta gudanar da zabukanta na fitar gwani a jahohin kasar, kamar yadda ita jam'iyyar PDP mai mulki ta gudanar da nata daga bisani.

 

………………………….

 

Jam'iyyar Zanu PF da ke mulki a kasar Zimbabwe ta sake zaben shuagaban kasar Robert Mugabe a matsayin shugabanta, yayin da kuma aka zabi matarsa a matsayin shugabar bangaren kula da harkokin mata na jam'iyyar. 

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a jiya a gaban dubban magoya bayan jam'iyyar ta Zanu PF a birnin Harare, shugaba Robert Mugabe ya yi mika godiyarsa ga dukkanin 'ya'yan jam'iyyar, dangane da abin da ya kira karamcin da suka nuna masa na sake zabarsa a matsayin shugaban jam'iyyar, tare da shan alawashin ci gaba da bin ka'idojin jam'iyyar da kuma kiyaye akidun da ta ginu a kansu.

Shugaba Mugabe dan shekaru 90 da haihuwa, ya karbi ragamar shugabancin kasar Zimbabwe tun a shekara ta 1980, bayan da ya jagorancin gwagwarmayar da kai ga kawo karshen mulkin mallakar turawan Birtaniya a kasar.

……………………………………………

 

To jama'a masu saurare lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki a nan za mu dasa aya  saia  shirinmu na gaba, kafin lokacin nake yi muku fatan aljhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

Add comment


Security code
Refresh