An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 21 November 2014 06:36

An Nada Shugaban Rikon Kwarya A Burkina Faso

An Nada Shugaban Rikon Kwarya A Burkina Faso
Jama' masu saurare Assalamu alaikum, barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, inda shirin nay au kamar kullum zai mayar da hankali kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wasu daga cikin kasashen nahiyar a mako, daga cikin abubuwan da shirin zai yi dubi a kansu kuwa har da batun kafa wata majalisar da za ta jagoranci lamurran shugabanci na rikon kwarya a kasar Burkina Faso, da kuma batutuwa da suka shafi siyasa da tsaro a Najeriya, sai kuma batun gangamin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a jamhuriyar Nijar, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, sai a kasance tare da mu.   …………………………………………..

 

 

To madalla, bari mu fara da batun kasar Burkina Faso, inda aka share wannan mako ana tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar da kuma kungiyoyin farar hula gami da shugabannin kabilun kasar, da kuma sojoji a da ke rike da madafun iko a kasar a daya bangaren, dangane da batun girka majalisar shawara wadda za ta jibinci sha'anin gudanar da mulkin rikon kwarya a kasar, kafin lokacin gudanar da zabuka a shekara mai zuwa.

 

………………………………….

 

To tarayyar Najeriya kuwa har yanzu dai batutuwa na tsaro su ne suka fi daukar hankula a cikin lokutan nan, inda  a cikin wannan makon batun sake kwace garin Mubi gari na biyu mafi girma a jahar Adamawa daga hannun 'yan bindiga na Boko Haram yana daga cikin muhimman batutuwa da suka dauki hankula, bayan da 'yan tauri tare da taimakon jami'an tsaro suka kaddamar da hari a garin kuma suka fatattaki 'yan bindigan na Boko Haram.

……………………………….

 

To bayan sake kwace garin na Mubi daga hanun 'yan bindiga na Boko Haram, 'yan bindigar sun kwace iko da garin Chibok na jahar Borno, bayan sace 'yan matan sakandare fiye da 270 na wannan gari da 'yan bindigar suka yi kimanin watanni 7 da suka gabata, wadanda babu labarinsu a halin yanzu, duk kuwa da cewa an yi artabu da jami'an tsaro da kuma mayakan na Boko Haram, a yunkurin da jami'an tsaron suke yi na sake kwace iko da garin.

 

A can garin Azare na jahar Bauchi ma an kai harin kunar bakin wake da bama-bamai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu, dukkanin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata dai fararen hula hula da ke gudanar da hidimominsu nay au da kullum. Babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin, amma dai hukumomi a jahar da kuma sauran al'ummar gari suna zargin kungiyar ta Boko haram ne da kai harin.

 

……………………………………

 

A bangaren siyasa kuwa batun gangamin da shugaban majalisar wakilai Alh. Aminu Tambuwal ya gudanar tare da kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin kasa a karakashin inuwar jam'iyyar adawa da APC na daga cikin batutuwan da suka dauki hankula.

 

………………………………..

 

A jamhuriyar Nijar kuma a cikin wannan mako ne jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki ta gudanar da wani gangami a birnin Damagaram, domin nuna karfinta da kuma samuwarta a jahar ta Damagaram wadda 'yan adawa suke da rinjaye.

………………………………….

 

To jama'a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki, a nan zamu ja linzamin shirin sai idan Allah ya kai mu mako na gaba, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

 

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh