Suratul Kahfi, Aya Ta 1-6 (Kashi Na 498)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu a cikin shirin domin aji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

****

Yanzu sai a saurari aya ta 1 zuwa ta 3 a cikin suratul Kahfi.

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجَا{1} قَيِّماً لِّيُنذِرَ بَأْساً شَدِيداً مِن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً حَسَناً{2} مَاكِثِينَ فِيهِ أَبَداً{3}

"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafin da babu karkata a cikinsa ga bawansa.

(Littafin ne) mikakke saboda ya yi gargadi mai tsauri daga azabarsa- ubangiji- kuma ya yi bushara ga muminai da su ke yin ayyukan kwarai da cewa suna da kykkyawan lada.

Za kuma su dawwama a cikinsa har abada."

Wannan surar ta fara ne da yi wa Allah godiya saboda saukar da wahayin da ya yi ga manzonsa. Tana kuma koya mana cewa ba saboda ni'imomin abin duniya ne kadai ake yi wa Allah godiya ba, ana yi masa godiya saboda shiriyar da ya yi mana wacce ita ce ni'ima mafi girma. Ni'ima ce wacce ta zo acikin littafin Allah da ya ke na shiriya wanda babu karkata acikinsa. Littafi ne wanda ya ke a mike da ya ke kunshe da bayani akan addini na gaskiya.

Sau da yawa a cikin kur'ani ubangiji yana bayyana addini da cewa: Shi ne addini mikakke, yana kuma kiran mutane ne da su bi mikakkiyar hanya ta gaskiya. Hanya ce wacce sako-sako ko wuce gona da iri a cikinta. Kuma ma'aiki yana yi wa mutane gargadi da kuma bushara saboda su kasance cikin fadaka a koda yaushe.

Darussan da su ke a cikin wadannan ayoyi.

1-Ni'imar kur'ani tana da girman gaske da muhimmanci ta yadda ubangiji ya ke yi wa kansa godiya.
2-Bushara da gargadi da annabi ya ke yi akan koyarwar da ta zo a cikin kur'ani ne, ba daga gare shi ba ne domin kur'ani shi ne addini mikakke.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 4 da ta 5 acikin wannan sura ta Kahfi.

وَيُنذِرَ الَّذِينَ قَالُوا اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَداً{4} مَّا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ وَلَا لِآبَائِهِمْ كَبُرَتْ كَلِمَةً تَخْرُجُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِباً{5}

" Kuma ya yi gargadi ga wadanda su ke cewa Allah ya riki Da. Ba su da masaniya da shi, kuma ba su da masaniya da iyayensu. Kalmar da ta ke fitowa daga bakunansu tana da girma. Abinda su ke fada ba wani abu ba ne face karya."

Ayoyin da su ka gabata suna magana ne akan gargadi da wa'azi. Amma wadannan ayoyin kuwa suna yin magana ne akan zance mara tushe da ke cewa ubangiji yana da Da. Kirictoci da yahudawa da kuma mushrikai duk sun yi tarayya akan wannan. Mushrikai suna cewa mala'iku 'ya'yan Allah ne, su kuma kiristoci suna cewa Isa ne dan Allah, yayin da yahduawa su ke cewa Uzairu ne dan Allah.

Hakikanin gaskiya shi ne cewa wannan irin tunani yana cin karo da akidar tauhidi wanda ya zo a cikin saukakkun littatafai.

Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin.

1-Fada da gurbatattun akidu wadanda su ke karkatattu shine aiki mai muhimmanci da annabawa su ke yi.

2-Wajibi ne akida ta ginu bisa ginshikin ilimi idan kuwa ba haka ba to za ta kai mutum ga karkacewa.

3-Jahilci da rashin sani ne su ke ingiza mutum ya rika jinginawa ubangiji abubuwan da ba su dace ba.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 6 acikin suratu kahfi.

فَلَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ عَلَى آثَارِهِمْ إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهَذَا الْحَدِيثِ أَسَفاً{6}

"Tamkar kana son ka halaka kanka saboda bakin ciki idan ba su yi imani da wannan zancen ba."

Wannan ayar tana kwantarwa da ma'aiki hankali ne dangane da halin mutane. Ya kasance yana yin bakin ciki saboda ganin yadda mushrikai ba su yi imani da zancen gaskiya ba.

Yadda ma'aiki ya ke bakin cikin ganin cewa kafirai sun ki yin imani da gaskiyar da ya zo musu da ita, yana yin tsananin da zai iya sanadiyyar mutuwarsa. Yana yin haka ne saboda jin tausayinsa ga mutane da son ganin sun shirya. To wannan ayar ta sauka ne saboda na bashi nutsuwa akan hakan.

Darussan da su ke cikin wannan aya.

1-Damuwa akan cewa mutane ba su karfi gaskiya ba wani abu ne mai kima wanda annabawa su ke da shi.

2-Jagororin addini da masu wa'azi wajibi ne a gare su su rika yin kwazon shiryar da mutane da gyara halayensu da akidunsu, koda kuwa ba su sami sakamako na zahiri ba.

Karshen wannan shirin kenan sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin anan gaba.