An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Awwal

Awwal

Ranar 12 ga watan Farvardin, daya ne daga cikin ranaku masu tarihi da kuma muhimmanci cikin kalanda da tarihin Iran musamman cikin shekarun baya-bayan nan. Saboda kuwa a wannan ranar ce a shekarar 1357 hijira shamsiyya (1979), aka tabbatar da sakamakon shekara da shekaru na gwagwarmaya da fada da mulkin kama-karya ta gidan sarautar Pahlawi da kuma neman ‘yancin kan al’ummar Iran da kuma tabbatar da Jamhuriyar Musulunci a kasar ta Iran. A wannan ranar ce dai al’ummar Iran, ta hanyar ba da kashi 98.2 cikin dari na kuri’ar da suka kada a yayin kuri’ar jin ra’ayin al’umma da aka yi ga Jamhuriyar Musulunci, wanda hakan ya sauya tsari da tushen siyasa, zamantakewa da kuma al’adu a kasar sannan kuma ya kafa tsari na addini da kuma na mutane a kasar. A saboda haka ne tun daga wancan lokacin har zuwa yau a ke kiran wannan rana da sunan “Ranar Jamhuriyar Musulunci” a kasar ta Iran.
Friday, 25 March 2016 06:29

Iran A Shekarar 1394 (1)

  Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shiri na Iran a Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Friday, 25 March 2016 05:48

Iran A Mako 27-12-94

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Iran cikin mako wanda ni MuhammadAwwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Saturday, 27 February 2016 16:57

Iran A Mako 25-02-2016

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako shirin da ke leko muku wasu daga cikin lamurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.
Sunday, 31 January 2016 05:21

Suratul Naml Aya Ta 89-93 (Kashi Na 694)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.
Sunday, 31 January 2016 05:17

Suratul Naml Aya Ta 86-88 (Kashi Na 693)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.
Sunday, 31 January 2016 05:10

Suratul Naml Aya Ta 82-85 (Kashi Na 692)

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka Mai Sanda, inda mukan kawo muku bayani dangane ayoyin kur’ani mai tsarki, da kuma abubuwan da suke koyar da mu, har yanzu muna a cikin surat Naml, inda  a yau za mu kawo muku bayani kan ayoyi na 82 zuwa 85 a  cikin surat Naml, da fatan za a kasance tare da mu.
Sunday, 31 January 2016 04:59

Suratul Naml Aya Ta 76-81 (Kashi Na 691)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.
Sunday, 31 January 2016 04:45

Suratul Naml Aya Ta 70-75 (Kashi Na 690)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah. **************MUSIC******** To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 70 zuwa 72 a cikin surar Namli:    وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُن فِي ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ    70-Kuma kada ranka ya baci game da su, kada kuma ka zama cikin kuncin zuciya game da makircin da suke kullawa.   وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ   71- Suna kuma cewa: Yaushe ne lokacin wannan wa’adin idan kun kasance masu gaskiya.   قُلْ عَسَى أَن يَكُونَ رَدِفَ لَكُم بَعْضُ الَّذِي تَسْتَعْجِلُونَ    72-Ka ce da su: lallai sashin abin da kuke dokin zuwansa ya kusanto. A cikin shirin da ya gaba a aya ta 69 kun ji yadda kur’ani kur’ni mai tsarki ya bukaci masu nuna bakar adawa da Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da su yi yawo da yin tafiye tafiye a bangarori daban daban a fadin duniyar nan  domin ganin yadda al’ummomi daban daban da suka ki amsa kiran manzonninu suka hallaka da zama turba abin mantawa da daukan darasi daga rayuwarsu.Amma wadannan ayoyi da muka saurara suna Magana ne kai tsaye da manzon Allah (SWA) cewa: kar ka damu da bakar adawa da jayayya da kin karbar gaskiya da kiran gaskiya da shiriya  saboda kai ka isar da sakon da aka turoka da shi kuma ka sabke nauyin da aka daura maka da isarwa a kunnuwansu haka Allah ya bawa kowane mutum yanzi da zabi ko yayi imani ko ya kafirce ya rage nashi kuma kowa ne aiki an yi masa tanadi da sakamakon da ya dace da shi.Wani hamzari ba gudu b aba wai kawai sun ki yin imani kuma suna kokari da kulla makircin hana wasu su karfi wannan kira na manzon Rahama (SWA) ,Allah ba zai bar su ba ko cin nasara a wannan makircin da suke kulla maka . Ci gaban ayoyin sun yi nuni da maganganun da mushrikai key i da cewa; su mushrikai na ci gaba da izgilin da suke yi wa Manzon Allah da mumunai na cewa:wannan alkawali da ka key i mana bayanin da tsoratar da mu da azaba da yawan bayani kansu kana cewa :azabar Allah a wannan duniya da lahira za ta riske mu,mi yasa wannan azaba har yanzu ba ta riske mu ba muna jiran ta ta zo. To Allah ya amsa masu da cewa;ku bar gaggauwa da azarbabi  ba da jimawa ba za ku fuskanci wannan azaba tabbas abin da kuke yi wa izgili zai riske ku. A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da cewa; damuwa da nuna takaici kan tababbu yana da iyaka dole mu yi iyakacin kokarinmu na shiryar da wadanda suka kaucewa hanya madaidaiciya amma idan sun fahimta da karbar gaskiya fa lillahi Hamdu idan kuwa suka ci gaba da riko da hanyar tabewa kar mu tsanantawa kanmu sai mu bar su da yin bara’a da sub a tare da mun cutar da kanmu ba kan halin da suke ciki. Rangwame da Karin lokacin da Allah ke bawa kafirai da azzalumai  ba don bay a manta da su ba ne kuma ko ba jima ko ba dade za su gamu da sakamakon mummunan aikin da suka aikata a wannan duniya ko a gobe kiyama. *******************MUSIC************   Yanzu za mu saurari karatun ayoyi na 73 zuwa 75 a cikin wannan sura ta Namli:   وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ   73-Kuma hakika Ubangijinka Mai falala ne ga mutane,sai dai kuma yawaicinsu ba sa godewa.   وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ    74-Hakika kuma Ubangijinka lallai Ya san abin da zukatansu suke boyewa,da kuma abin da suke bayyanawa.   وَمَا مِنْ غَائِبَةٍ فِي السَّمَاء وَالْأَرْضِ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ   75-Kuma babu wani abu da yake boye  cikin sammai da kassai face yana cikin littafi mabayyani watau Lauhul Mahafuzu.   Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da muka saurara ne a baya da ke cewa:idan Allah ya kyale masu banna da azzulumai da kafirai gami da mushrikai da jinkirta masu azaba  ba  yana nunin kasawa ko ya sha’afa da su da mantawa da su  ba ne .a’a don lutifi da falalarsa Allah ne ga wayunsa saboda haka yake jinkirta masu da kara masu lokaci da damar yin tuba.Amma kash ba su lura da amfana da wannan rahama ta Allah ,bas u yin godiya da canja halayensu daga mummuna zuwa kyaukkawa sai dai ci gaba da kuma nacewa kan aikata saboda banna. Tana yuyuwa mabannata suna zaton Allah yak i hukumtasu da gaggauta azabtar da su ne saboda bas hi da masaniya kan ayyukan da suke aitawa ko bas hi da masani kan abubuwan da suke kullawa da makircinsu  da mummunar niyarsu.To su sani ba wai sub a duk wani abu mai rain a linfashi da wand aba yayi Allah ya san da zamansa da abin da yake aiktawa daidai da kwayar zarta babu wani abu da yake boye ga iliminsa saboda komi yana rubuce a lauhin mahfuz kuma ilimin Allah bas hi da karshe da iyaka ,Allah yana sane da komi da tafiyar da lamarinsa. Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da daukan darussa kamar haka:Mu amfna da wannan damar da Allah ya ba mu da yin tuba da aikata ayyukan alheri da gyara ayyukanmu. Mu sani Allah masani ne kan komi babu wani abu a cikin sammai da kassai da yake boyuwa da Allah ko da kuwa su abubuwa sun boyu ga mutum kamar ranar tashin kiyama . Ba wai kawai nuna bukatar gyara ayyukanmu ba kadai hatta niyarmu muna bukatar gyara ta domin ya sani da masaniya kan duk wani abu da muka boye. Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..
Saturday, 30 January 2016 13:20

Suratul Naml Aya Ta 64-69 (Kashi Na 689)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.
Page 1 of 186