An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 24 August 2015 06:55

Aifuwar Imam Ridah (a.s)

Jama’a masu saurare Assalamu aleikum, barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shiri na musamman, dangane da zagayowar ranar aifuwar Imam Rida (AS) daya daga cikin limaman shiriya na Ahlul bait (AS) Muna taya dukkanin al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan rana mai albarka. Da fatan za a kasane tare da mu a cikin shirin. Music……………………………………………………….. Imam Ali bn Musa Rida (a.s) shine Limami na takwas daga cikin Limaman gidan iyalan Ma’aikin Allah tsarkaka, sunan ma’aifinsa Imam Musa Alkazim (a.s) sunan Ma’aifi’arsa Tajma kuma ana kiranta da sunaye kamar hamar haka Arwa da kuma Sakan, bayan ta aifi Imam Aliyu Rida Imam Musa Kazim ya sanya mata sunan Attahira. An aifi Imam Aliyu bn Musa Rida a garin Madina shekara ta 148 bayan hijrar Annabi daga Makka zuwa Madina, wasu riwayoyin kuma sun bayyana cewa an aifeshi a shekara ta 151 bayan hijra, wasu kuma sun ce a shekara ta 153, amma sahihin tahiri shine maganar farko wata an aife shi a shekara ta 148 bayan hijra.bayan an aifeshi ma’aifinsa Imam Musa (a.s) ya yi murna sosai sannan ya yiwa ma’afiyarsa barka da cewa(ina taya ki Murka Ya ke Najma, wannan karama ce daga Ubangijinki) sannan sai Najma ta sanyashi a cikin farin kyalle ta meka shi ga Ma’aifinsa Imam Musa Kazim (a.s) yayin da ya amshe shi yayi masa khuduba sannan ya sanya masa sunan kakansa Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) , bayan haka ya meka shi wajen Ma’aifiyarsa tare da cewa Hakika wannan falalar Allah ne mai wanzuwa a tsakanin bayinsa. Hakika Imam (a.s) yanada lakabi masu yawa mafi shuhura suna kamar haka:Arida, Asabir, Azakiyu ,Alwafi, kuratu Aynul mumunin, Makidatu Mulhidin, Assidik da kuma Alfadil . Kuniyarsa kuma shine Abulhasan domin a banbabce shi da ma’aifinsa Imam Kazim ana kiransa da Abulhasan Sani shi kuma Ma’aifinsa ana kiransa da Abulhasan Madi. Bayan shekaru 16 da aifuwarsa daular Umawiyawa ta fadi sai aka kafa Daular Abbasiyawa, wancan lokaci ya kasance lokacin da soyayyar iyalan gidan Ma’aikin Allah ta bunkasa a tsakanin Al’umma bayan da Al’umma ta fahimci matsayin su a wajen Allah madaukakin sarki da kuma kakansu Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka. Soyayarsu da Abassiyawa na tafiya keke da keke, saboda Al’umma ta fahimci irin  zaluncin da bani Umaiyya suka yi musu, su kuma Abassiyawa saboda sun kifar da Azzalumar daular Bani Umayya,kamar yadda mahawarar Imam Kazim (a.s) da Haruna Al’abbasi ta shaida hakan yayin da Haruna Abbasi ya ce Imam Kazim (a.s) kaine wanda Al’umma ke yi maka mubaya’a cikin Sirri, sai Imam Kazim (a.s) ya amsa masa da cewa:(ni shugaban  zukata ne kai kuma shugaban kankar jiki ne) ma’ana ni shugaba ne da Al’umma suka amince da ni a cikin zukatansu, kai kuma shugaba ne da Al’umma suka aminceda kai a zahiri saboda tsoron salwanta rayukansu. Hakika masu saurare Allah madaukakin sarki ya hore wa Imam Rida (a.s) kyawawen dabi’u da kuma falala masu yawa kamar yadda ya horewa Ma’aifaisa masu girma kuma ya yi masa Ado da duk wani karamci da daukaka sannan ya sanya shi Alama ga Al’ummar kakansa Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, yake shiyar da Al’umma hakikanin Addinin Kakansa Ma’aikin Allah (s.a.w), hakika halayen Imam Rida (a.s) wani bangare ne daga halayen Kakansa Ma’aikin Allah shugaban kyawawen dabi’u (s.a.w) wanda kuma ya yi wa sauren Annabawa (a.s) fintinkau wajen cikar kamala,yayin da yake bayyana halayen Imam Aliyu bn Musa Rida (a.s),Ibrahim bn Abas ya ce:ban taba gani kuma ban taba ji ba, mutuman da ya fi Abil Hasan Rida (a.s) falala ba, domin shi bai taba aibata ko kuma cin zarfin wani ba,bai taba yanke maganar wani yayin da yake magana ba, bait aba kin biyar bukatar wani ba yayin da ya gabatar da bukatarsa, bai taba meke kafafuwansa  a gurin zamansa ba, ko kuma zakin wanda yake kalkashin ikonsa ko mabiyinsa ba, ya kasance mai barci kadan a cikin Dare, yana raya Aksarin Daransa daga farkonsa har zuwa karshensa, mai yawan kyautatawa da Sadaka, kuma mafi yawan sadakarsa ta kan kasancewa cikin duhun Dare ne). Daga cikin kyawawen Dabi’unsa a yayin da yake shugabancin Al’umma bai cika sanya mabiyansa aiki ba, idan ya nada wata bukata, shi da kansa ya kan tashi ya aiwatar da bukatarsa, kuma a yayin da ya bukaci zama da farko ya kan zamnar da wadanda suke yi masa hidma da farko kamar su mai gadi da saurensu domin ya basu darasi na cewa babu wani babbanci tsakanin Mutane, Ibrahim bn Abas yana cewa na ji Aliyu bn Musa Rida (a.s): na yi rantsuwa zan ‘yantar, kuma ban taba yin ranzuwa ‘yantarwa ba face na ‘yantar, kuma in ‘yantar da dukkanin bayin da na mallaka, idan yana ganin hakan shi ya fi Alheri,sannan ya nuna wani bawa bakar fata daga cikin bayinsa ya ce ko wani mutune aikinsa ne ya ke fifita shi a tsakanin Mutane idan ya kasance wannan daga cikin makusantan Ma’aikin Allah (s.a.w), sai ya aikata aiki mai kyau, idan kuma ba hakan ba, to wanda ya aikata aikin na kwarai zai kasance ya fi shi a wajen Allah)sai wani daga cikin mutanen dake tare da shi suka ce wallahi babu wani mutune a doron kasa da ya fika girma a bangaren ma’aifa, sai imam (a.s) ya ce masa Takawa da tsoron Allah shine Sharafinku da kuma girmanku,da’a da kuma bin umarnin Allah shine garkuwarku, har ila yau sai wani daga cikin Mutane yace masa wallahi kaine mafi alheri daga cikin Mutane sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa: ya kai wane kadda kayi rantsuwa, wanda ya fini Alheri, wanda ya kasance ya fi tsoron Allah kuma ya fi kowa yin nafilfilu na ibada sannan sai ya karanto wannan Aya tare da cewa wallahi wannan Aya  ba ta shafe ba,(Ya Ku Mutane, Hakika Mu Muka Halice Ku daga Namiji da Mace, Muka Kuma Sanya Ku kungiya da Kabilu(daban-daban)don ku san juna, Hakika mafi girmanku a wurin Allah wanda ya fi ku tsoron Allah, hakika Allah Masani ne, masani ne da Badininku) suratu Hujurat Aya ta 13. **********************Musuc***************************** Matsayin Imam Ridha (a.s) Ya zo cewa Imam Musa alKazim (a.s) ya ce wa 'ya'yansa: "Wannan dan'uwanku Ali dan Musa shi ne masanin alayen Muhammad (s.a.w), ku tambaye shi addininku, ku kiyaye abin da yake gaya muku…" . Imam Ridha (a.s) ya kasance haske ne da ya sauko daga salsalar gidan hasken da ya haskaka wannan duniya, kuma daya daga cikin waliyyan Allah (s.w.t) masu sanar da mutane Ubnagijinsu, masu kama hannayensu zuwa ga shiriya. Masu saurare ga wata takaicecciyar fadakarwa. Imami (a.s) shi ne wanda yake shiryar da mutane zuwa ga tafarkin tsira bayan wucewar manzon rahama (s.a.w), domin su samu rabauta a duniya da lahira. Don haka kowanne daga cikinsu haske ne da yake haskaka duniya domin mutane su gane hanyar da zasu taka zuwa ga Ubangiji wanda shi ne kololuwar kamalarsu. Imam Ridha (a.s) yana da matsayin yardar Allah madaukaki, shi yardajje ne abin yarda, kuma ya kasance wannan yardar tasa ta bayyana a zamaninsa, yayin da ya kasance abin yarda ga kowane abin halitta, sai wanda ya fita daga fidirar halitta  ta dan'adamtaka. An tambayi Imam Jawad[AS]cewa mi  yasa ake cewa babanka  Arri-dha,ya  ba da  amsa da cewa;Saboda makiyan sa sun yarda da shi,kamar yadda masoyan sa suka yarda  dashi.yace haka bai kasance  ga Imamai da suka gaba ce shi ba. Imam Rida (a.s) ya rayu cikin wani yanayi na ibtali da wahalhalu kamar yadda Imamai da suka gabace shi, suka rayu kuma ya gudanar da rayuwarsa a lokacin da fiye da khalifofi uku na Banu Abas suka yi zamani, ya ga zamanin Khalifofi Banu  Abas kamar haka, Mansour, Mahdi, Hadi, Rashid sai kuma Ma’amun wanda shi ne ma ya kai shi zuwa ga Shahada. Ga kadan daga cikin yadda rayuwarsa ta kasance da khalifa Ma’amun, bayan irin zalincin da kuma zubar da jinni da Khalifofin banu Abas suka aikata, fishin Al’umma ya karu wanda hakan ya sanya Ma’amun ya canza siyasa domin ya samu yardarm Mutane, kamar  yadda masu saurare suka sani Imaman daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka sun zama tamkar hotuna a zuciyar halifa, sai nan da nan ya tashi daga inda yake a zaune yana cewa: dole ne mu sami mafita… kuma mu yi maganin wannan bore da ke dagula mana siyasarmu… Abin  mamakin irin shawara da halifa Maamun ya yanke… Kuma wace irin musiba ce ta dami makusantansa… Kuma ta sa su suke yawaita tambaya, suna cewa: shin ta yaya Maamun zai yi nufin bada sarauta ga wani… ya mika daular da Banu Abbas suka gina ta da jini da kuma yaki, kuma saboda ita suka bada dukkan abinda suka bayar cikin tsawon shekaru 70 da suka gabata… ta wannan hanya mai sauki zata koma ga zuriyar Abu Talib…? A cikin wannan hali sai daya daga cikin waziran Maamun mai suna Hasan bin Sahl, bayan Maamun ya tattauna da shi da dan uwansa Fadl bin Sahl… sai ya ce wa Maamun: Ya shugabana shin ka san irin hadarin da ke tattare da kawar da mulki daga mutanen  gidanka…? Sai Maamun ya amsu masa ya ce: Na yi alkawari ga Allah akan zan bada wannan mulki ga mafificin zuriyar Abu Talib… Kuma ban san wani mutum da ya fi wannan mutumin ba…wato ya na nufin Imam Ridah (a.s). Sai Hasan bin Sahl da dan`uwan sa Fadl suka ga babu  abinda ya kamata su yi face su yi shiru tun da ga irin shawarar da halifa Maamun ya yanke, don haka sai suka daina nuna masa rashin yardarsu, bil hasali ma, sai Maamun ya ce musu… Ku tafi yanzu zuwa wajen Ali bin Musa Ar-Rida… ku ba shi labari cewa na yanke wannan shawara… Hasan bin Sahl da dan`Uwansa Fadl sai suka fita daga fadar Maamun… suka nufi birnin Madinal Munauwarah bayan sun riga sun gindaya wasu sharuda a tsakaninsu da Maamun… Yayin da suka isa wajen Imam Rida(A.S.)… sai suka yi masa tayin cewa za a nada shi a matsayin mai jiran gado… amma da sharadin ba zai bada wani umarni ba… ba kuma zai nada wani ya zama gwomna a wani wuri ba… ba zai yi maganar shari`a a tsakanin wasu mutane ba koda su biyu ne… ba kuma zai canza wani abu ba cikin abinda ke tsaye kan tushensa… Imam Rida(A.S.) yana dai sauraransu alhali ya san cewa Maamun bin Rashid yana kokarin daukan fansa ne… gami da kokarin da yake yi na ganin ya nuna wa mutane cewa adalci yake yi, daga bisani kuma ya sami mataimaka har ma ya samu ya rage fushin mutane da yanzu haka suka kai makura,  don ganin irin zaluncin da Banu Abbas ke aikata wa iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka,  har wa yau Maamun yana tunanin yadda zai samu ya kawo karshen bore da alawiyyawa suka yi wanda kuma a kulli yaumin sai dada girmama da tsananta yake yi a sanadiyyar tursasawa da zubar da jinin da Banu Abbas suke yi da barnatar da dukiya da kuma mummunar mulki da suke yi, ga kuma rashin kwanciyar hankali… don haka ne Maamun ya yanke shawara ta siyasa domin ya daure Imam Rida(A.S.) ta hanyar nada shi mai jiran gado… saboda ganin cewa shi Imami ne daga Ahlu Baitin Annabi(S.A.W.A.), kuma shi shugaba ne fitacce, sannan a zamaninsa babu wanda ya tsere masa a ilimi… Imam Rida(A.S.) bai yi wani jinkiri ba wajen kin yarda da wannan shawara ta Maamun… sai daya daga cikin sahaban Maamun ya fito da takobi ya ce masa: Wallahi shugaba na Maamun ya umarce ni da in sare wuyanka idan ka saba uimarninsa! Yai mamakin irin wannan mataki na siyasa… wane irin jiran gado ne wanda ba umarni ko hani a cikinsa… ba nada gwamna ko tube shi… ba zai yi hukunci a tsakanin koda mutum biyu ba… to bayan wannan duka, hakika Imam(A.S.) ya zamanto tilas ya karbi wannan jiran gado… *****************Musuc*********************** Imam Ali bin Musa Al-Rida sai ya bar Madina ya nufi Marwu, wato babban birnin hukumar Banu Abbas, ya bi ta hanyar Basra da Ahwaz… yayin da ya isa wani wuri da ake kira Nubaju… sai ya sauka kusa da wani masallaci a gurin, nan take mutane suka fara taruwa a gefensa… a tsakaninsu akwai wani mutum da ake kira Abu Habib Annubaji… wannan mutum sai ya tsaya yana al`ajabi yayin da ya ga Imam Rida ya fito da kwano wanda a cikinsa akwai dabinon [saihan] sai ya ga Imam ya dauka yana ci, abinda ya kara ba shi mamaki shine sai ya ga Imam(A.S.) ya dauki dabino ya ba shi… koda ya kirga sai ya tarar guda goma sha takwas ne Imam ya mika masa… to anan fa sai wannan mutumin ya fara magana a cikin ransa, yana cewa: Kwana ishirin baya na ga Manzon Allah(S.A.W.A.) a cikin mafarki yana zaune a daidai wannan wurin… kuma yana cin irin wannan dabinon daga wani kwano…Kuma Manzon Allah(S.A.W.A.) ya danko daga

 

dabinon da yake ci ya ba ni, koda na kirga sai na samu guda goma sha takuwas ne … a lokalin sai na yitawilin mafarkina da ce wa kenan zan rayu na tsawon shekata  goma sha takwas bayan mafarkin…

Sai Habibu ya juya wajen Imam Rida(A.S.) ya ce: Ya dan gidan Ma`aikin Allah… ka kara ba ni dabinon… sai Imam(A.S.) ya ce masa: da kakana Manzon Allah(S.A.W.A.) ya kara ba ka, to da ni ma na kara ba ka…

Bayan haka sai Imam Rida(A.S.) ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai garin Naishabur… sai wasu mutum biyu suka zo wurinsa, dayansu ana kiransa Abu Zar`a Arrazi, daya kuma ana kiransa Ahmad bin Aslam Attusi… tare da wadannan mutum biyu akwai jama`a daga malamai da maruwaita… a yayin nan Imam Rida yana cikin suturceccen karaga darbuka akan alfadari mai rodi-rodin launi, ya kuma shigo kasuwa da Alfadarin… Sai suka roke shi don girman darajar iyayensa tsarkakku ua nuna musu fuskarsa sa mai haske kuma ya gaya musu ruwaya daga iyayensa… Sai kuwa Imam ya amsa musu ya daga labule, sai ga goshinsa mai albarka yana annuri irin annuri na Imamanci… Sai mutane suka zama daga mai kuka… Sai mai juyayi wasu kuma sai takbiri da hailala suke yi… wadansu kuma sai sumbantar karagar suke yi don neman tabarruki…

A daidai wannan lokaci sai daya daga cikinsu ya ce jama`a a yi shiru…

Yayin da aka kashe kunne… Sai Imam Rida(A.S.) ya fito da kansa daga cikin lema ya ce: mahaifina kazim ya ruwaito daga mahaifinsa Ja`afar Assadik… daga mahaifinsa Muhammad Al-Bakir… daga mahaifinsa Ali bin Husain Assajjad… yace mahaifinsa Husain ya ruwaito daga mahaifinsa Ali Amirul Muminin ya ce: dan `uwana, kuma dan baffana Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ruwaito cewa: Mala`ika Jibrilu ya ce: na ji ubangiji mai daukaka, mabuwayi, wanda ya tsarkaka yana cewa: “Kalmar la`ilaha illallahu hurumi Na ne… Kuma duk wanda ya shiga hurumi Na ya kubuta daga azaba ta…”

Imam Rida(A.S.) yayi shiru jim kadan sannan ya ce musu: amma fa da sharadinta da sharuddanta…

To bayan wannan Imam(A.S.) sai ya ci gaba da tafiyarsa har ya sauka a wani wuri da ake kira Farwini… a wannan guri akwai dakin wanka, sai Imam(A.S.) ya shiga yayi wanka… sannan ya fito yayi sallah… bayan haka Imam ya ci gaba dai da tafiyarsa ya wuce garin Sarakhsa har ya iso Marwu babban birnin daular Banu Abbas wanda ta kasance tana shirin tarbarsa…

tana kuma sauraron isowarsa… a cikin wadannan masu tarba akwai shi halifa Maamun da fadawansa da mahukuntansa…

To sai aka shiga zance… aka shiga tattaunawa tsakanin Imam Rida(A.S.) da Maamun da waziransa da ya dora musu wannan aiki… Sai Imam nan gaba ga Maamun ya yi kokarin ya ki karbar wanna mukami na mai jiran gado, amma bayan Maamun yayi masa kashedi da cewa: hakika Umar ya sanya shura a tsakanin mutum shida kuma kakanka yana daya daga cikinsu sannan Umar ya ce: (wanda ya saba ku sare wuyansa) to dole ne ka karbi abinda na gaya maka, to bayan wannan sai Imam Rida ya karba…

Sannan sai Maamun ya umarci wazirinsa Fadl bin Sahl da ya fita gurin mutane ya sanar musu abinda ya tsayar game da Imam Ali bin Musa Ar-Rida… na cewa yana so ya nada shi mai jiran gado a bayansa…

Sannan kuma Maamun yayi umarni da a canja bakaken tufafi wanda dama suke nuni ga alama ta Banu Abbas

a canja su zuwa Koren tufafi… a ranar da za a yi mubaya`a ga Imam sai komandojin rundunoni da alkalai da sauran manyan mutane suka taho… dukkansu na sanye da koren kaya… Sai Maamun ya umarci dansa Abbas da ya zama wanda zai fara yin mubaya`a… Sai kuwa ya tashi yaje wajen Imam(A.S.) domin yayi masa bai`a… Sai Imam ya daga hanunsa, ya sanya tafin hannunsa na fuskantar mutane, bayan hannunsa kuma na ta wajen fuskarsa… wannan abu ya bada mamkai ga Maamun sai ya ce wa Imam(A.S.)ka bada hannunka a yi maka mubaya`a…

Sai Imam(A.S.) ya ce: hakika haka Manzon Allah(S.A.W.A.) ya kasance yake yin bai`a ga mutane.

Aka kare taron yin mubaya`a alhali Maamun ya bada muhimmanci sosai ga wannan taro… domin kuwa mawaka da masu wa`azoji da masu yin murna da sauran mutane duk sun halarci taron… kuma an raba kudi da kyaututtuka, Maamun kuma ya ci gaba da bin wannan lamari ta yadda maganar jiran gado zai kankama- mutane kuma su ga cewa lamarin da gaske ne… Sannan ya bada umarni kan a buga kudi da sunan Imam Rida(A.S.), aka kuma yi haka…

bayan haka sai ya bada umarni a dukkan fadin daular a dukkan garuruwa da cewa a rika ambaton Imam Rida(A.S.) a hudubobin Sallar juma`a da sauran wurare… sannan ya kara daukan wasu matakai da za su karfafa tsakaninsa da Imam(A.S.), sai ya aurar masa da `yarsa Ummu Habib… saidai kuma dukkan wadannan aiyuka da Maamun ya aikata yayi su ne domin mutane su ga cewa yana da kyakkyawar manufa… kuma su ga cewa wannan mataki na siyasa da ya dauka abu ne da yayi nufin gaskiya ciki…

Bayan haka sai kuma Maamun ya bukaci Imam(A.S.) da ya aiwatar da wani aiki na jama`a wanda hakan zai sa mutane su ga cewa hakkan Imam(A.S.) ya fara gudanar da aiyuka da suka shafi lamarin hukuma… don haka ya nemi Imam(A.S.) yayi Limanci ga mutane a Sallar idin azumi wanda ya zo jim kadan bayan an yi mubaya`a ga Imam(A.S.)… Imam kuwa nan da nan ya ce wa Maamun a`a, saidai kuma bayan Maamun yayi takidi ya kuma nanata masa, sai Imam ya ga an matsa masa lamba, anan sai ya ce wa Maamun: Ya shugaban muminai, idan da zakai min afuwa kan wannan to haka na fi so… idan kuwa baka yarda ba, to saidai in fita zuwa sallar idi kamar yadda Manzon Allah(S.A.W.A.) yake fita… kuma kamar

yadda Amirul Muminin Ali bin Abi Talib ya kasance yake fita…

Maamun sai ya ce masa: Ka fita kamar yadda ka so…

Halifa Maamun ya umarci gwamnoni da sauran mutane da cewa tun da sanyin safe su tafi kofar gidan Imam Rida(A.S.) su jira shi… mutane suka zauna a kan hanyoyi da saman gine-gine suna jira… gwamnoni kuma suka hadu a kofar gidan Imam Rida(A.S.) har zuwa lokacin da rana ta fito… Sai Imam(A.S.) ya tashi yayi wanka… ya nada farar rawani na auduga, ya jefa wani bakin rawanin ta gabansa daya bakin kuma ya jefa akan kafadarsa, sannan yayi ishara ga makusatansa ya ce musu: Ku aikata kamar yadda na aikata…

Sai ya fita ba takalmi a kafarsa yana cikin makusatansa, a cikin sifa ta mai tsoron Allah, mai yankuwa zuwa ga Allah madaukaki, ba tare da ya nuna wani shiga ta girman kai ko shiga ta mulki da sarauta ba, ya kuma daga kansa sama… ya fara takbiri: Allah Akbar… Allahu Akbar… Allahu Akbar… wal hamdu lillah ala ma hadana… Allahu Akbar ala ma razakana min bahimatul An`am… Wal hamdu lillahi ala mabtalana…

Wato yana cewa Allah mai girma… Kuma godiya ta tabbata ga Allah bisa shiryarwarsa garemu… Allah mai girma… Kan abinda ya arzuta mu da shi na daga dabbobin niima – kuma godiya ta tabbata ga Allah bisa jarabamu da yayi…

Imam(A.S.) ya daga muryarsa yana fadin haka… mutane su ma suka daga muryarsu, garin Marwu kuma ta girgiza saboda kuka da ihu da mutane ke yi… Sai gwamnoni suka fado daga kan dabbobin su… sannan suka yi jifa da takalmansu, yayin da suka ga Imam(A.S.) idan yayi kowane taku goma sai ya tsaya yayi takbiri sau hudu sannan ya ci gaba… suka zaci cewa sama da kasa da gine-gine duk suna amsa wa Imam… wannan abu ya tsoratar da mahukuntan Maamun da fadawansa… suka kuma ga irin kafuwar da Imam Rida(A.S.) zai yi tun yanzu da kuma irin nasarar da zai samu a bangaren siyasa… wannan abu ya sa Fadl bin Sahl ya ji tsoro sosai don haka sai yayi gaggawa ya tafi wurin Maamun, ya isa yana haki: ya ce: Ya kai Amirul Muminin, idan Rida ya isa masallacin idi a bisa irin wannan hali da yake, to mutane zasu fitinu da shi… Saboda haka shawara ta dai ita ce ka ce masa ya komo…

Nan take wutar fushi ta soma hauhawa… ta ci gaba da tsananta, don haka Maamun ya fara numfashi, kai ka ce bakin gajimare ne ya taru, yayin nan sai ya ga ba abinda zai yi face yayi aiki da shawarar wazirinsa kuma abokin shawararsa wato Fadl bin Sahl… don haka ya aika

zuwa wurin Imam Rida(A.S.) aka koma da Imam zuwa gida… alhali Maamun kuma yana nan yana tunani kan wani lamari da yake son aiwatarwa…

Daga karshe wannan fushi na Maamun da wannan bakin gajimare da ya taru sai ya saukar da wutar sa… amma anya kuwa akwai wanda zai ce bai san inda wannan wutar fushi ta sauka ba?… hakika wanda yayi tunanin haka yana cikin demuwa… domin kuwa sai ga mutane suna taruwa suna daga muryarsu suna fadin cewa: hakika Maamun ya kashe Ali bin Musa Arrida(A.S.)…Haka kuwa ya faru ne a karshen watan Safar   shekara ta 203 yayin nan yana da shekara 55 a duniya.

Imam (a.s) ya yi shahada ya nada shekaru 55 a duniya ya bar da guda shine Imam Jawad (a.s) da fatan masu saurare sun anfana da wannan shiri wassala alekum warahamalullahi ta’ala wa barkatuhu.

 

Add comment


Security code
Refresh