An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 14 April 2015 09:51

Shiri Na Musamman Kan Ranar Haihuwar Fatima (a.s)

Shiri Na Musamman Kan Ranar Haihuwar Fatima (a.s)
Shiri Na Musamman Kan Ranar Haihuwar Fatima (a.s)

 

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shiri na musamman daga cikin shirye-shiryen da muka saba gabatar muku da su a duk lokacin ranaku na musamman irin wannan, wato lokutan haihuwa ko kuma shahadar Ahlulbaitin Ma’aiki (s.a.w.a).

 

Masu saurare yau take 20 ga watan Jimada Thani, ranar da Allah ya ba wa Manzonsa (s.a.w.a) da wata kyauta wacce babu irinta inda yake cewa Inna A’atainakal Kauthar sannan kuma ya kare Ma’aikin nasa daga izgilin da Makiya suke masa na cewa shi mai yankakken baya ne da cewa Inna sha’ani aka huwal abtar. Wannan babbar kyauta kuwa ita ce Sayyida Fatima al-Zahra (a.s) wacce aka haifa a daidai irin rana mai kamar ta yau shekaru biyar bayan aiko Ma’aikin Allah (s.a.w.a).

 

Har ila yau kuma a daidai wannan ranar ce aka haifi daya daga cikin manyan jikokin Fatima al-Zahran (a.s) wato marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya assassa juyin juya halin Musulunci na kasar Iran.

 

Don haka shirin na mu na yau zai yi dubi ne cikin bangarori daban-daban na rayuwar Sayyida Zahra (a.s) kana daga karshe mu yi dubi ko da a gurguje ne cikin wani bangare na rayuwar Marigayi Imam Khumainin.

 

Kafin mu je ga hakan, muna taya dukkanin al’ummar musulmi musamman mabiya Ahlulbaiti (a.s) da kuma dukkanin masu saurarenmu murnar wannan rana mai albarka. Allah ya maimaita mana ya kuma sanya mu karkashin inuwa da kulawar Sayyida Zahra duniya da lahira.

 

=-------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

An haifi Fatima al-Zahra (a.s) ne a ranar juma’a, ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi’u daga Khadijatul Kubra. Hakan ne ma ya sanya Fatima ta kasance tana dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi’unsa, har ma an ruwaito Uwar Muminai A’isha tana cewa: “Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (s.a.w.a) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima ‘yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (s.a.w.a) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta”.

 

Haihuwar Fatima ya faranta wa Manzon Allah (s.a.w.a) rai, farin cikin da ba za a iya kwatanta shi ba saboda irin matsayin da Fatima take da shi a wajensa da kuma Allah Madaukakin Sarki, don haka ne ma daga baya aka jiyo shi yana fadin cewa: “Fatima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni. Ko kuma fadinsa cewa: “Lallai Fatima wani yanki ne daga gare ni.

 

Ita ma a nata bangare, ita ma Fatima ta kasance mai tsananin kaunar mahaifinta. Wato Fatima na girma alhali kaunar babanta gare ta na girma tare da ita, tausayinsa a kanta na karuwa; kuma ita ma tana musanya masa wannan kauna, tana cika zuciyarsa da lura; don haka ya kira ta da Ummu Abiha (wato uwa a wajen babanta). Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga ‘ya’yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da ‘ya’yansu kanana. Lallai wannan abin koyi ne na tsarkakkar alakar uba (da ‘ya’yansa) wajen gina ‘ya’ya da fuskantar da dabi’u da rayuwarsu, da cika zukatansu da kauna da tausayi. Lalle wannan alaka ta zama babbar abar misali a fagen renon ‘ya mace a Musulunci da lura da ita, girmama ta da daukaka matsayinta.

 

Ba haka kawai cikin wargi Annabi (s.a.w.a) ya sanya mata wannan suna na ‘Ummu Abiha’ ba. Ya sanya mata sunan ne, saboda aiki da hidima da kokarin da take yi ne. Fatima, shin a lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke Makka ne, ko a lokacin zaman Shi’abi Abi Talib – da irin wahalhalun da aka fuskanta a wajen – ko kuma a lokacin da mahaifiyarta Khadijah ta bar duniya ne, Fatima ta kasance tare da wannan mahaifi nata cikin dukkanin damuwar da yake ciki. Duk wanda ya karanci tarihi zai ga cewa cikin dan karamin lokaci Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci wasu abubuwa guda biyu masu sosa rai, wato rasuwar Khadijah (matarsa) da kuma Abu Talib (wato baffansa) wadanda ya siffanta su a matsayin wadanda Musulunci ya tsaya da kafafunsa ta hannun su, su biyu din tare da dan Amminsa Aliyu bn Abi Talib (a.s). Cikin dan karamin lokaci Manzon Allah ya rasa wadannan mutane biyu, hakan ya sanya shi cikin kadaici. Amma haka Fatima al-Zahra da ‘yan kananan hannayenta ta kawar wa Annabi wannan damuwa da yake ciki. Ummu Abiha, ta kasance mai kwantar wa Annabi da hankali. Don haka a wancan lokacin a fili za’a iya ganin ma’anar wannan sunan. A takaice ana iya cewa a wancan lokacin na tsanani, Sayyida Fatima al-Zahra (a.s) ta kasance tamkar uwa, likita kana kuma mai ba da shawara ga Ma'aiki (s.a.w.a), a lokacin kuwa ba ta wuce shekaru shida zuwa bakwai na rayuwarta ba. Ashe matsayar da al-Zahra (a.s) ta dauka na rage wa mahaifinta wahalhalun da yake ciki bayan ya kai kimanin shekaru hamsin na rayuwarsa, wato a takaice dai ya tsufa, bai isa ya zamanto abin koyi ga kowace matashiya da matashi ba?.

 

Har ila yau irin girman matsayin da Fatima ta ke da shi ne ya sanya Annabi (s.a.w.a) ya kan sumbanci hannunta. Bai kamata a dauki sumbartar hannun Fatima al-Zahra da Annabi (s.a.w.a) ya ke yi a matsayin irin kaunar dake tsakanin uba da ‘ya kawai ba. A’a, wannan wani abu ne na daban da ke da wata ma’ana ta daban. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa wannan matashiyar, wannan baiwar Allah, lalle ta kai wani matsayi na kusaci da Ubangiji sannan kuma wata baiwar Allah ce mai kolin matsayi.

 

Na’am Fatima al-Zahra, wata ‘yar’adam ce, wata mace ce, ita din ma matashiya; amma a a wata ma’ana wata hakika ce mai girma, wata haske ce ta Ubangiji mai haskakawa sannan kuma wata baiwar Allah ce saliha zababbiya. Ita ce wacce dangane da ita Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke ce wa Amirul Muminin (a.s) cewa: “Ya Ali, kai ne shugaban al’ummata sannan halifana a kanta a bayana. Kai ne mai jagorantar muminai zuwa Aljanna. Kamar ina ganin ‘yata Fatima a ranar Kiyama tana zuwa a kan wani rakumi na haske. A damanta ga Mala’iku dubu saba’in, a hagunta ga Mala’iku dubu saba’in, a gabanta ga Mala’iku dubu saba’in haka nan a bayanta ga Mala’iku dubu saba’in, tana jagorantar muminai mata na al’ummata zuwa Aljanna (Ana iya samun wannan hadisin cikin littafin Bihar al-Anwar, juzu'i na 43, shafi na 24.”. Wato a ranar Kiyama, Amirul Muminin (a.s) shi ne zai jagoranci muminai maza, ita kuma Fatima al-Zahra (a.s) ita ce za ta jagoranci muminai mata zuwa Aljannar Ubangiji. Ita ta kasance kini kuma kwatankwacin Amirul Muminin (a.s). Ita ce wacce a lokacin da ta tsaya a wajen ibadarta, dubban Mala’iku na kurskusa da Ubangiji suna isar mata da gaisuwa da jinjina mata, suna gaya mata abubuwan da a baya Ma’aiku suka gaya wa Maryam tsarkakakkiya, suna fadin cewa: “Ya Fatima, lalle Allah Ya zabe ki, ya tsarkake ki da kuma daukaka ki a kan sauran matan duniya”. Wannan shi ne matsayi na kusaci da Allah da Fatima al-Zahra (a.s) take da shi.

 

-------------------------------------------------/

 

Har ila yau a daidai wannan matsayi na kusaci da Allah, shi din ma a shekarun samartaka, lalle Fatima ta kai irin wannan matsayi na kusaci da Allah ta yadda kamar yadda wasu riwayoyi suka nuna a kan sami Mala’ikun Allah suna magana da ita da kuma sanar da ita wasu bayanai da masaniya. Don haka ne ma ake kiranta da Muhaddatha, wato wadda Mala’iku suke magana da ita. Wannan matsayi na kusaci da Allah kolin matsayi ne da ya dara na dukkanin matan da Allah Ya halitta. Fatima al-Zahra (a.s) ta kai wannan matsayi na daukaka.

 

Tsawon tarihi – shin a lokacin tsohuwar jahiliyya ce ko kuma jahiliyar karni na ashirin – an sami wasu mutane da suka yi kokarin kaskantar da mace da damfara ta da abubuwan kyalkyale-kyalkyale na duniya da suka hada da tufafi da ado da gwala-gwalai sannan kuma abar jin dadi na rayuwar duniya sannan kuma suke ci gaba da yin hakan. Musulunci ya bayyana Fatima al-Zahra  a matsayin abin koyin mata. Irin wannan rayuwa ta zahiri da jihadi da gwagwarmaya da ilimi da iya magana da sadaukarwa da iya zama da miji da uwantaka da yin hijira da kasantuwa a dukkanin fagage na siyasa da soji da juyin juya hali da ficen da ta yi a dukkanin fagage da ya sanya dukkanin mazaje mika kai, haka nan kuma a fagen kusaci da Ubangiji da irin ruku’u da sujada da zama a wajajen ibada da addu’oi da kankan da kai a gaban Allah da sauran ababen da suke kusata mutum da Ubangiji, duk sun yi daidai da irin wanda Amirul Muminin (a.s) yake da su. Wannan ita ce mace. Wannan ita ce irin mace abin koyin da Musulunci ya ke son ginawa.

 

Akwai wani lamari cikin rayuwar Fatima al-Zahra ma’abociyar tsarki (a.s) wanda wajibi ne a lura da shi.  Duk da cewa fahimtar irin wannan matsayi da Fatima al-Zahran take da shi ba, wani lamari ne da ya dara fahimta da kuma tunaninmu. A hakikanin gaskiya Allah Madaukakin Sarki ne kawai ya san irin wadannan bayi nasa – sai kuma wadanda suka kai wannan matsayi na zama manyan bayin Allah - da suka kai wannan matsayi na koli na kusaci da Allah da kamala ta dan’adam sannan kuma yake ganin hakan. A saboda haka Manzon Allah (s.a.w.a) da Amirul Muminin da ‘ya’yanta Ma’asumai ne suka san Fatima al-Zahra (a.s). To amma a cikin rayuwarta ta zahiri, akwai wani lamari mai muhimmanci wanda shi ne hada tsakanin rayuwar wata mace musulma cikin irin mu’amalarta da mijinta da ‘ya’yanta da kuma nauyin da ke wuyanta na kula da gida, a bangare guda kuma da nauyin da ke wuyanta a matsayinta na ma’abociyar jihadi ba kama hannun yaro wajen tinkara lamurra na siyasa masu muhimmanci bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a) lokacin da take zuwa masallaci da gabatar da jawabi da bayyanar da matsayarta da kuma kare wannan matsayar. Wato wata mujahida ce ta hakika mai jurewa dukkanin wahalhalun da ta fuskanta. Haka nan kuma a bangare na uku, wata ma’abociyar ibada, mai sallar dare da tsayuwa saboda Allah da kuma kaskantar da kai a gare shi a yayin ibadar. Haka wannan matashiya ta kasance tana ibada da neman kusaci da Allah tamkar tsoffin bayin Allah waliyai.

 

Idan aka hada wadannan bangarori uku waje guda, su ne za su iya bayyanar da rayuwar Fatima al-Zahra (a.s). Wannan babbar baiwar Allah ba ta taba raba wadannan bangarori uku ba. Wasu dai suna zaton cewa a lokacin da mutum ya kasance mai ibada da kankan da kai da addu’oi da zikiri, to kuwa ba ruwansa da duniya da abubuwan da ke cikinta cikin kuwa har da lamurra na siyasa da gudanarwa. Ko kuma wasu suna zaton cewa duk wanda ya zamanto dan siyasa – shin namiji ne ko mace – sannan ya zamanto mai kokari a fagen jihadi saboda Allah, idan har mace ce, to kuwa ba za ta iya aiwatar da aikinta na gida a matsayin uwa ko matar aure ba. Idan kuwa namiji ne ba zai iya zama mai kula da iyali da zama dan kasuwa ba. Suna zaton wadannan abubuwan kishiyar juna ne. Alhali kuwa a mahangar Musulunci babu wani karo da juna tsakanin wadannan abubuwa ukun. Abubuwa ne masu taimakawa juna a cikin rayuwar dan’adam ma’abocin kamala.

 

Shaksiyyar Fatima al-Zahra ma’abociyar tsarki a fagen siyasa da zamantakewa da jihadi wata shaksiyya ce madaukakiya wacce kuma ta yi fice; ta yadda dukkanin mata ma’abota gwagwarmaya da yunkuri da wadanda suka yi fice a fagen siyasa na duniya za su yi daukan darasi daga gajeruwar rayuwarta da ke cike da abubuwan amfani. Macen da aka haifa a gidan juyin juya hali wacce ta gudanar da dukkanin lokacin yarintarta a gaban mahaifinta wanda ya kasance babban dan gwagwarmaya na duniya da ba za a taba mancewa da shi ba. Wannan macen da a lokacin yarintarta, ta sha wahalhalu na gwagwarmayar lokacin zaman Makka, an tafi da ita zuwa Shi’abi Abi Talib. Ta dandani yunwa da wahalhalu da tsoro da sauran nau’oi na wahalhalun lokacin zaman Makka. Daga nan kuma ta yi hijira zuwa Madina, ta zamanto matar mutumin da ya gudanar da dukkanin rayuwarsa wajen jihadi saboda Allah. Tsawon kimanin shekaru sha daya na zaman aure tsakanin Fatima al-Zahra da Amirul Muminin (a.s), ba a taba samun wata shekara, kai rabin shekara ma da wannan miji na ta bai tafi filin daga ba. Haka wannan babbar baiwar Allah mai sadaukarwa ta zamanto matar wannan mujahidi sannan kuma jarumin kwamandan soji a filin daga. A saboda haka, rayuwar Fatima al-Zahra, duk da cewa gajeruwa ce, ba ta wuce shekaru ashirin ba; amma wannan rayuwar, a fagen jihadi da gwagwarmaya da kokari da juriya da koyar da wannan da wancan da kuma gabatar da jawabai da ba da kariya ga tafarkin annabci da imamanci da tsarin Musulunci, rayuwa ce da take cike da kokari da gwagwarmaya da aiki ba kama hannun yaro sannan daga karshe kuma ta yi shahada. Wannan ita ce rayuwa ta jihadi ta Fatima al-Zahra (a.s) wacce a hakikanin gaskiya ba ta da tamka. Ko shakka babu hakan lamari ne mai kima da matsayi a kwakwalwar bil’adama, shin a yanzu ne ko kuma a nan gaba.

 

A fagen ilimi ma, ta kasance wata masaniya ta koli. Wannan hudubar da Fatima al-Zahra (a.s) ta yi a masallacin Ma’aikin Allah (s.a.w.a) bayan rasuwarsa, wata huduba ce, kamar yadda Allamah Majlisi ya ce, wacce wajibi ne masana fasahar magana da sauransu su zauna don binciko ma’anonin kalmomi da jumlolin da suke cikinta. A bangaren fasaha (wannan hudubar) tamkar irin kalmomi da jumloli masu tsawo da kuma kyau na littafin Nahjul Balaga ne. Fatima al-Zahra (a.s) ta kan tafi masallacin Madina, ta tsaya a gaban mutane tana magana ba tare da karkarwa ba; tana magana na tsawon lokaci da mafi kyawun jumloli da kalmomin da suka dace.

 

Haka nan idan muka dubi lokacin da ya biyo bayan rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a), yadda al-Zahra (a.s) ta zo masallaci da yadda ta gudanar da sananniyar hudubar nan tata alhali a lokacin ba ta wuce shekaru sha takwas, ko ashirin ko kuma ashirin da hudu ba (gwargwadon sabanin ruwayoyin da aka samu kan lokacin haihuwarta), za mu iya fahimtar girma da fasahar da take da ita da za ta taimaka mana a bangaren huduba da magana. Duk da irin bala'i da wahalhalun da take ciki amma ta tafi masallaci gaban darurrukan jama’a, cikin hijabi ta gabatar da wannan hudubar, wadanda kalmominta daya bayan daya suna nan cikin kundin tarihi, lalle lamari ne babba.

 

Wannan huduba ta al-Zahra (a.s) bayan sama da shekaru 1,400 tarihi ya ci gaba da kiyaye ta saboda irin girma da fasahar da ke cikinta, wanda hakan kan sa mutum al'ajabi da mamaki a duk lokacin da ya dubi irin fasahar dake cikinta.

 

Rayuwar Fatima al-Zahra (a.s) ta dukkanin bangarori, rayuwa ce da take cike da aiki da kokari da kamala da daukaka ta ruhi ta wani mutum. Matashin mijinta a koda yaushe ya kasance a fagen daga, to amma duk irin wadannan matsaloli na rayuwa da take fuskanta, Fatima al-Zahra (a.s) ta kasance wata cibiya da mutane da musulmi suke komawa gare ta. Ita din nan ‘ya take ga Annabin da ayyuka suka dabaibaye shi, amma duk da irin wannan yanayin haka ta gudanar da rayuwarta cikin dukkanin daukaka. Ta tarbiyyartar da ‘ya’ya irin su Hasan da Husain da Zainab; ta kula da miji irin Ali sannan kuma ta samu yardar mahaifi irin Manzon Allah (s.a.w.a). A lokacin da musulmi suka sami nasara da ganima da yawa (bayan yakukuwa), to amma wannan ‘ya ta Ma’aiki ba ta kai kanta kusa da irin wadannan abubuwa na jin dadi da kyale-kyale na duniya da suke jan hankula budurwaye da manyan mata ba.

 

Ibadar Fatima al-Zahra (a.s), wata ibada ce abar koyi. Hasan al-Basri wanda ya kasance daya daga cikin fitattun ma’abota ibada da kuma zuhudu a duniyar musulmi dangane da Fatima al-Zahra (a.s) yana fadin cewa: “Saboda irin yawan ibada da tsayuwa a wajen ibada da ‘yar Manzon Allah take yi har sai da kafafunta suka kukkubura. Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) yana fadin cewa: A wani dare – daren Juma’a – mahaifiyata ta tsaya tana ibada har zuwa asuba. Wato har lokacin da alfijir ya keto mahaifiyata ta kasance tana ta ibada da addu’oi da kankan da kai a gaban Allah. Imam Hasan (a.s) – kamar yadda ruwayar ta bayyana – ya bayyana cewar na ji ta tana ta addu’oi wa muminai maza da muminai mata; tana addu’a wa mutane da kuma batutuwan da suka shafi al’ummar musulmi. Lokacin da gari ya waye sai na ce mata: Ya mahaifiyata! Ba ki kasance kina addu’a wa kanki kamar yadda kike addu’a wa waninki ba. Wato tun daga dare har zuwa safiya kina addu’a wa mutane? Sai ta ce masa: Ya kai dana! Makwabci kafin dan gida’, wato sauran mutane kafin kanmu. Wannan shi ne irin wannan karfin gwiwa. Haka nan jihadinta a fagage daban-daban, wani jihadi ne abin misali. Wajen kare Musulunci; wajen kare imamanci da wilaya; wajen kare Ma’aikin Allah; wajen kare babban kwamandan Musulunci, wato Amirul Muminin (a.s) wanda ya kasance mijinta ne. Amirul Muminin (a.s) dangane da Fatima al-Zahra (a.s) yana fadin cewa: “Ba ta taba bata min rai ba, sannan kuma ba ta taba saba wa umurni na ba”, wato tsawon rayuwarmu ta aure, ba ta taba yin wani abin da zai fusata ni ko kuma kin aikata wani umurni da na ba ta ba. Fatima al-Zahra, duk da irin wannan girma da daukaka da take da ita, a fagen iyali ta kasance wata matar aure ce; kamar yadda Musulunci yake so.

 

Irin ibadarta, irin fasaha da balagarta, irin wannan ilimi da take da shi, irin wannan masaniya da hikima, irin wannan jihadi da gwgwarmaya, irin wannan mu’amala da halaye nata a matsayin ‘ya mace, irin wadannan halaye nata a matsayin matar aure, haka nan kuma halayenta a matsayinta na uwa, haka nan da kuma irin kyautatawarta ga mabukata ta kai yadda a lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya aike da wani mabukaci zuwa gidan Amirul Muminin (a.s) don a biya masa bukatar da yake da ita; nan take Fatima al-Zahra ta dauki gadon fatan da ‘ya’yanta Hasan da Husaini suke kwanciya a kai ta ba wa wannan mabukacin don ba ta da wani abin da za ta ba shi tana ce masa: dauki ka je ka sayar ka yi amfani da kudin. Wannan ita ce Fatima al-Zahra. Wannan abin koyin. Wannan ita ce abar koyin matan musulmi.

 

Wajibi ne mace musulma ta yi kokari a tafarki hikima da ilimi; haka nan kuma a fagen gina kai da samun kyawawan halaye. Ta zamanto a sahun gaba-gaba a fagen jihadi da gwagwarmaya, ko wane irin jihadi da gwagwarmaya ne kuwa; ta kasance mai rashin kula da ababen kyale-kyale na duniya marasa kima; haka nan kuma ta kasance mai kiyaye mutumcinta ta yadda ba za ta janyo idanuwan duk wani bako zuwa gare ta ba. A cikin gida ta zamanto mai kwantar wa miji da ‘ya’ya hankula; ta zamanto dalilin kwanciyar hankali da zaman lafiyan iyali. Ta zamanto mai tarbiyyar yara lafiyayyu masu sanin ya kamata. Ta tarbiyyantar da mutane wadanda ba sa da wani kulli a zuciyarsu, mutane masu farar zuciya, lafiyayyun mutane a bangare ruhi da zuciya don ta samar wa da al’umma wasu irin mutane masu amfani.

 

-----------------------------------------------/

 

Masu saurare wannan dan kadan kenan daga cikin abin da za mu iya gabatar muku dangane da Fatima al-Zahra a cikin wannan shiri na mu saboda karancin lokaci. Ko shakka babu rayuwar Fatima al-Zahra dai kogi ne da sai dai kawai mutum ya dan iya diban dan abin da ya sami damar diba.

 

To bari mu karkare shirin na mu da fadin wani abu dangane da rayuwar jikanta marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda shi ma aka haifa a irin rana mai kamar ta yau.

 

A wannan bangaren za mu yi amfani ne da kalamai da maganganun Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei kan marigayi Imam Khumainin.

 

A wani jawabin Jagora a lokacin mubaya'ar kwamandojin soja da dakarun kare juyin Musulunci 17/3/1368 hijira shamsiyya, Ayatullah Khamenei yana cewa:

 

A hakikanin gaskiya baya ga annabawan Allah da WaliyanSa Ma'asumai (a.s) babu wani mai matsayi da za'a iya kwatanta shi da jagoranmu mai girma marigayi Imam (Khumaini). Shi wata taska ce ta Ubangiji a hannunmu. Hujjar Uangiji a kanmu. Kuma aya wacce take nuni da girman Ubangiji. Idan mutum ya gan shi zai tuna da matsayin jagororin addini da kuma yarda da su. Ba za mu iya kwatanta girman matsayin Annabi (s.a.w.a) da Amirul-Muminin (a.s.) da Shugaban shahidai (a.s.) da Imam Sadiq (a.s.) da Imam Mahdi ba. Tunaninmu ya yi kankanta wajen iya fahimtar girman matsayinsu. Sai dai a lokacin da mutum ya ke ganin mutum mai girman matsayi irin Imam abin kaunarmu da siffofinsa mabanbanta na imani mai karfi da cikakken hankali da hikima da kaifin kwakwalwa da hakuri mai zurfi da tsayin daka da gaskiya da tsarki da zuhudu da kau da kai daga kawar duniya da takawa da tsantseni da tsoron Allah da bautar Allah cikin tsarkin zuciya, sannan kuma da yadda ya ke bayyana kaskantar da kansa ga Imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su, to mutum zai fahimci wane irin girma ne Waliyai Ma'asumai suke da shi.

 

A wani sakon Jagora ga a'lmumar Iran dangane da girmama Imam Khumaini a ranar 18/3/1368, Ayatullah Khamenei yana cewa:

 

Mutum ne mai girman siffofin da idan aka cire Annabawa da Waliyai Ma'asumai (a.s.) to samun makamancinsa a tsakanin jagororin duniya da kuma a cikin tarihi yana da wuya.

Shi mutum ne ma'abucin imani da aikin kwarai da aniya mai karfin gaske da azama da jarumta ta kyawawan halaye da suka hadu da hikima da azama. Yana kuma da yankakken zance da bayani da suka hadu da gaskiya da tsayin daka. Yana da tsarkin zuciya da kaifin tunani da hazaka da tsoron Allah da tsantseni da yanke hukuncin da babu shubuha a ciki. Yana da halayen jagoranci na tsayin daka da suka hadu da tausayi da sassauci. A takaice ya hada siffofin da samunsu a tattare da mutum daya ya karanta a cikin karnukan baya. A hakikanin gaskiya girman halayensa da siffofinsa suna da wuyar samu. Matsayinsa na koli a ‘yan'adamtaka ya nesanta da duk wata almara.

Matsayinsa ya yi daidai da na uba kuma malami abin kauna ga almuar Iran. Shi fata ne da dukkan masu rauni a duniya musamman musulmi. Shi bawan Allah ne na kwarai mai kaskantar da kai ga Ubangiji, mai raya dare da ibada wanda kuma ya ke a matsayin ruhin zamaninmu. Shi kyakkyawan abin koyi ne ga musulmi kuma jagora na Musulunci. Ya daukaka addinin Musulunci ya kuma daga tutar Alkur'ani a duniya. Ya yantar da al'ummar Iran daga kangin bauta ta kasashen waje ya kuma cusa musu ji da kansu da tsayuwa kan kafafunsu. Ya yi shelar ‘yanci a duniya baki daya da kuma cusa fata a cikin zukatan al'ummun da suke rayuwa karkashin zalunci. Ya kafa tsarin siyasa da ya dogara da addini a daidai lokacin da manyan ‘yan siyasa a duniya suke kira da a mai da addini da kuma kyawawan halaye saniyar ware. Ya jagoranci Jamhuriyar Musulunci a tsawon shekaru goma tare da fuskantar kalubale mai girma da matsaloli masu hatsarin gaske amma bisa kawarewarsa da shiriyarsa ya kaita tudun mun tsira. Jagorancinsa na shekaru goma abin tunawa ne ga al'umma da jami'anmu kuma wata taska ce mai kimar gaske.

 

Add comment


Security code
Refresh