An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 01 January 2013 19:08

Mutane 60 Ne Suka Rasa Rayukansu A Bukukuwan Sabon Shekara A Ivory Coast

Mutane 60 Ne Suka Rasa Rayukansu A Bukukuwan Sabon Shekara A Ivory Coast
Mutanen 60 aka tabbatar da mutuwarsu a jiya da dare a birnin Abidjan na kasar Ivory coast a bukukuwan shigar sabuwar shekara ta 2013. Kafafen yada labarai da dama sun bayyana cewa mutanen sun rasa rayuaknsu ne sanadiyyar tattakesu da aka yi a lokacin da ake wasan wuta a kusa  da filin wasannin na birnin, inda dubban  mutane suka taru don wasan wuta na sabuwar shekar. Shugaban tawagar sojojin da suka shigo don bada agaji bayan yamutsin Lieutenant Colonel Issa Sako ya fadawa yan jaridu cewa mutane 60 ne suka tabbatar da mutuwarsu, kuma da dama daga cikinsu yara kanana, wadanda aka tattake a lokacin da yamutsi ya tashi cikin cinkoson mutanen masu wasan wuta. Sannan  wasu 200 kuma suna karban magani a asbitoci a birnin. Lieutenant Colonel Issa Sako ya ce mai yuwa yawan wadanda suka ya karu don tsanakin raunin da wasu suke fama da su. Har yanzun dai ba'a san musabban yamutsin wanda ya kai ga tattake wasu mutanen ba.  

Add comment


Security code
Refresh