An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mai da martani kan wani sabon shaidanci da kasashen yammacin Turai suka bullo da shi kan batun shirin makamashin nukiliyar kasar Iran na zaman lafiya.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa; Kasar Amurka ce ke da alhakin duk wani aikin ta’addanci a duniya.
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar manufar jibge ‘yan ta’adda a masu kafirta musulmi a kasar Siriya ita ce kunna wutar rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar manufar jibge ‘yan ta’adda a masu kafirta musulmi a kasar Siriya ita ce kunna wutar rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba amincewa da wata yarjejeniya kan shirin nukiliyanta karkashin inuwar barazanar kawo mata hare-hare ba.   Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da dubun dubatan malaman makarantu na Iran a yau din nan Laraba inda yayi watsi da barazanar da wasu jami’an Amurka suke yi na kawo wa Iran hari inda ya ce ko shakka babu Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta zuba ido kan duk wani wuce gona da iri a kanta ba tare da ta mayar da martani ba; kamar yadda kuma ya ce a halin yanzu bukatar da Amurka take da ita a tattaunawar nukiliyan ya dara bukatar da Iran take da ita ga tattaunawar.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin tsaro da ci gaban kasar Afghanistan a matsayin tsaro da ci gaban kanta ne, yana mai cewa hakan ne ya sanya wasu kasashen ba sa fatan ganin alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta karfafa.
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana amfani da dukkanin karfinta ne wajen kare kanta da hakkokinta.
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar al’ummar Iran ba su tsoron duk wata barazanar takunkumi ko batun daukan matakin soji kan kasarsu.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar kasar Amurka ce kan gaba a fagen kokarin rusa harkar tattalin arzikin kasar Iran. A ci gaba da jawabinsa a haramin Imam Ali Arridha {a.s} a birnin Mashhad a yau Asabar: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar makiya sun fi mai da hankali ne kan kokarin rusa harkar tattalin arzikin kasar Iran, kuma kasar Amurka ce kan gaba a wannan fagen, sannan babbar manufansu kan haka ita ce kokarin raba al’ummar Iran da tsarin Musulunci tare da tarwatsa matakan tsaro da zaman lafiya a kasar. Har ila yau Jagoran juyin juya halin ya kara da cewar babu wani mutum a Iran da baya kaunar ganin an kawo karshen takaddamar shirin makamashin nukiliyar kasar, to amma al’ummar Iran da tawagar kasar a zaman tattaunawa kan shirin makamashin nukiliyar Iran ba zasu taba lamintar sharuddan zalunci da za a gindaya a kansu ba. Haka nan Ayatullahi Khameine’i ya fayyace cewa; batun shirin makamashin nukiliya kadai ake gudanar da zaman tattaunawa a kai tsakanin tawagar Iran da na kasashen yammacin Turai da Amurka, don haka Iran ba zata taba amincewa da batun tattaunawa kan harkokin da suka shafi cikin gidanta ko makaman da ta mallaka ba ko kuma batun siyasar yankin gabas ta tsakiya.    
Published in Iran
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya taya al'ummar Iran da sauran al'ummomi da ke amfani da shekarar shamsiyya, murnar idin Nourouz da kuma shiga sabuwar shekarar shasiyyah ta 1394.  
Published in Top News
Page 4 of 5